NewsHausa NewsHausa

Pages

LATEST POSTS

Thursday, 28 July 2016

WAND YA SHA RUWA DA MANTUWA A AZUMIN NAFILA ,AZUMINSA YAYI?

WANDA YA SHA RUWA DA MANTUWA A AZUMIN NAFILA, AZUMINSA YAYI?

Tanbaya :
Assalamu Alaikum! Malam barka da war- haka.. Tambayace dani, qanwata ce tana azumin sitta shawwal sai tai mantuwa taci abu... Wasu sun ce wai axuminta ya karye tunda nafila ne. Shin hakan da suka fada gaskiya ne?

Amsa :

Wa alaikum assalam, Wanda yake azumi ya manta ya ci abinci ko ya sha abin sha, Allah ne ya ciyar da shi kuma ya shayar da shi, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisi, don haka azuminsa ya yi, babu banbanci tsakanin azumin nafila da na farilla.
                                                                                                Allah ne mafi sani.                                                        

Dr Jamilu Zarewa.                                                        

9 Shawwal 1437.

15/07/2016.

IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44,IDDARTA TA CIKA?

IDAN MAI TAKABA TA YI BARI BAYAN KWANA 44, IDDARTA TA CIKA ?:

Tambaya:

السلام عليكم ورحمة الله
Malalm don Allah a taimakamin da amsar wannan tambayar:

Mace ce mijinta ya rasu ya barta da ciki wata daya, bayan sati 2 da rasuwarshi sai cikin yazube to anan ya iddarta take?

1. iddar ta kare?

2. ko zata kirga wata 4 da kwana 10?

in kuma kirgar zat ai daga yaushe zata fara, ranar rasuwarshi ko ranar da cikin ya zube?
na gode.

Amsa:

Wa alaikum assalam,

Mutukar cikin na ta bai wuce kwana : 44 ba, ba za ta kammala iddar takaba da yin barinsa ba, tun da halittar mutum ba ta fara bayyana ga dan-tayin ba.                                                 
Mafi karancin lokacin da halittar mutum take fara bayyana yana farawa ne daga kwana: 80 zuwa 90.                                                                             
Idan haka ta faru da ita za ta yi idda da wata hudu da kwana goma.                                                            
Allah ne mafi sani.d
Dr Jamilu Zarewa.                                                         20/7/2016

IDAN DREBA YA KASHE MUTANE BAKWAI,YAYA KAFFARARSA

IDAN DREBA YA KASHE MUTANE BAKWAI, YAYA KAFFARARSA ?

Tambaya:

Assalamu alaykum tambayata anan shine idan tsautsayi yasa Kai ajalin rai bakwai da motarka, idan zakai axumi na kaffara nawa zakai ?

Amsa:

To dan'uwa kisan kuskure yana wajabta abubuwa guda biyu:

1- Diyya wace dangin wanda ya yi kisan za su bayar ga dangin wanda aka kashe da kuskure, sai dai in sun yafe.

2- Kaffara, wacce zai 'yanta kuyanga, in bai samu ba sai ya yi azumin wata biyu, kamar yadda aya ta 92 a Suratunnisa'i take nuni zuwa hakan.

Idan sama da mutum daya suka mutu a mota, ya wajaba ga Driban motar ya yiwa kowa kaffara kuma danginsa su biya diyya, mutukar shi ne sababi a hadarin, kamar ya zamana ya wuce danja ko kuma ya yi gudun da ya zarta ka'ida, ko burkinsa ya lalace amma ya ki gyarawa, ko wani abu makamancin haka wanda yake nuna sakacin Driba, ko wuce ka'idarsa.

Idan hadari ya faru wasu suka ji ciwo saboda sakacin Driba ko wuce ka'idarsa, sai suka mutu daga baya, danginsa za su biya diyyarsu kuma zai yiwa kowa kaffara, ko da kuwa bayan shekaru biyar ne da faruwar hadarin, saboda duk dalilin da yake kaiwa zuwa abu, to yana dai dai da abun

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba : Al'inaya 1\116, Madalibu Uli-Annuhaa 6\147 da kuma Fataawa Allajnah Adda'imah 23\352.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
17\7\2016

FATAWAR RABON GADO (36)

FATAWAR RABON GADO (36)

Tambaya :

Assalamu alaykum'm Allah ya gafarta malam dan'uwanmune ya rasu ba shi da Mata ba shi da 'ya'ya, mahaifiyarsa tana nan yana da yar'uwa mace uwa daya uba daya, mukuma ubanmu daya, shin muna cikin masu gado? Allah ya sakawa malam da alkhairi.

Amsa:

Wa alikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida:6, sai a bawa mahaifiyarsa kashi:1,  'Yar'uwarsa shakikiya kashi:3, ragowar sai a baku 'yan'uba ku raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.                               Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU ZAREWA.
18/07/2016.

FATAWAR RABON GADO (37)

FATAWAR RABON GADO (37)

Tambaya :

Assalamu alaykum malam da fantan an tashi lahia, don Allah ya Rabon gadon mamacin da ya mutu ya bar mata, amma bayi da ya'ya sai dai mahaifinshi da mahaifiyarshi na da rai, sai kuma 'yan uwanshi uwa daya uba daya?

Amsa:

Wa alaikum assalam, To dan'uwa za'a raba dukiyar da ya bari gida:12, sai a baiwa matarsa kashi uku, babarsa kashi biyu, babanshi kuma sai a bashi ragowar kashi bakwan.                                                                               'Yan'uwa ba sa yin gado, mutukar akwai uba.

Allah ne mafi sani.
24/07/2016

DR. JAMILU ZAREWA.

MAI AZUMIN NAFILA ZAI IYA KARYA AZUMINSA DA GANGAN!!

MAI AZUMIN NAFILA ZAI IYA KARYA AZUMINSA DA GANGAN ! !

Tambaya:

Aslm Na wayi gari da azumi sai aka kawo abinci sai na fasa azumin naci abincin ,malam yin hakan akwai laifi na sharia?

Amsa:

Wa alaikum assalam, ya halatta abin da ka yi, saboda fadin Annabi (s.a.w) "Mai azumin nafila sarkin kansa ne, in ya so ya cigaba da azumi, in ya so kuma ya karya".
kamar yadda Tirmizi ya rawaito                               
Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa.                                             25/7/2016

FATAWAR RABON GADO (38)

FATAWAR RABON GADO (38)

Tanbaya.

Ina da tambaya kan KALALA.

Idan mutum ya rasu, bashi da mata, ba d'a ba uba.

Amma yana da 'yan uwa SHAQIQAI maza da mata DA LI'ABBAI maza da mata.

Yaya gadon sa zai kasance?.

Amsa:

Wa'alaykumussalam. In har maza da mata ne shakikan,  sune zasu gaje dukiyar duka, kowanne namiji a cikinsu a bashi rabon mata biyu.
' yan uba basayin gado mutukar akwai namiji a shakikai.
Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa
26/07/2016