WANDA YA YI SAHUR ZATONSA ALFIJIR BAI KETO BA? - NewsHausa NewsHausa: WANDA YA YI SAHUR ZATONSA ALFIJIR BAI KETO BA?

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 21 June 2016

WANDA YA YI SAHUR ZATONSA ALFIJIR BAI KETO BA?

WANDA YA YI SAHUR A ZATONSA ALFIJIR BAI KETO BA !

Tambaya:

Assalamu'alaykum alykum.Allah karawa malam ilimi tambayata anan shine mutum ne akabashi wrong timing Na sahur har yashiga lokacin sallah da wurin minti 7-10 sakamakon irin timetable da aketurowa Na watsapp.malam ya matsayin axuminshi.

Amsa

Wa alaikum assalam, wanda ya ci sahur saboda zaton alfijir bai keto ba, azuminsa yana nan, kuma cin abincisa ya yi dai dai, tun da ba da gangan ya ci ba, kamar yadda aka rawaito daga Abdullahi dan Abbas Allah ya yarda da shi.        

Allah ne mafi sani.

Amsawa: Dr jamilu Zarewa.



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment