MALAMIN ISLAMIYARMU BA SHI DA TAJWIDI, YA WAJABA MU CANZA SHI ?
Tambaya:
Malam tambaya ta itá ce mun bude islamiya ta matar aure, to malamin da yake karantar da qur'an yana da matsalan tajweed kuma ya ki bar ma wani ya karantar Dan Allah Dr munada laifi cikin kuràkuran da yake koyarwa ?
Amsa:
Allah ya yi umarni da karanta Alqur'ani kamar yadda ya saukar, kamar yadda aya ta hudu a suratul Muzzamil ta yi nuni zuwa hakan.
wasu malaman musuluncin suna kasa tajwiidy gida biyu, akwai na dole kamar fitar da harufa kamar yadda suke a larabci, akwai na mustahabbi kamar yawancin maddoji.
Fitar da harufa wajibi ne saboda yana iya canza fassarar Alqur'ani.
Akwai wasu bangarorin na tajwidi wadan da ba wajibi ba ne dabbaka su, saboda Annabi (s.a.w) ya tabbatar da lada biyu ga wanda yake dagarawa a karatun Alqur'ani, kamar yadda ya zo a hadisin Muslim.
Allah ne mafi Sani
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.
9/8/2016.
No comments:
Post a Comment