Tambaya:MAGANIN QARFIN MAZA? - NewsHausa NewsHausa: Tambaya:MAGANIN QARFIN MAZA?

Pages

LATEST POSTS

Thursday, 18 August 2016

Tambaya:MAGANIN QARFIN MAZA?

MAGANIN QARFIN MAZA?
Tambaya:
Assalamu alaikum, Malam mutum ne yana da chemist yana sayar da magunguna. Ya halatta ya sayar da maganin qarfin maza ga wanda yake so ya biya bukatar iyalinsa? Allah ya qarawa Dr. imani da lafiya da ilimi, gaskiya muna amfana
Amsa:
Wa alaikum assalam, In har an jarraba an samu yana amfani kuma likitoci sun tabbatar ba ya cutarwa ya halatta a siyar da shi don aure ya gyaru, a kara samun donkon soyayya, saboda saduwa tsakanin ma'aurata turke ne tsayayye, wanda in ya goce aure ba zai tafi saiti ba, yana daga cikin ka'idojin Sharia duk harkokin mutane na yau da kullum wadanda ba ibada ba ne sun halatta, in har ba'a samu nassin da ya hana ba. Addinin musuluci ya haramta duk abin da yake cutarwa, kamar yadda nassoshi masu dinbin yawa suka tabbatar, wannan yasa duk maganin da likitanci ya tabbatar cutarsa ta fi amfaninsa yawa ya wajaba a guje shi, Tunkude cuta ginshike ne a cikin addinin musulunci.
Wasu masana yanayin dan'adam suna ganin: mutum ya tsaya a halittar da Allah ya yi masa, ba tare da ya sha maganin karfin maza ba, shi ne ya fi, saidai in rauninsa ya yi yawa, cin 'ya'yan itace da nama da kayan marmari, na daga cikin abubuwa da suke wanzar da mazakutar namiji, ba tare da cutarwa ba.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
17/8/1437
24/05/2016


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment