ZA KA IYA AURAN MACE BAYAN KA SAKI BABARTA! ! ! Tambaya:
Malam mutun ne ya auri mace yana tsammanin budurwace mai kananan shekaru, bayan sun tare sai ya gane cewa ba karamar yarinya bace tana da shekaru masu yawa, Don haka ba tare da sun yi saduwa na aure ba ya saketa.
Bayan haka tafiya ta kai shi zuwa wani gari inda acan yasami yarinya mai irin shekarun dayakeso sai sukayi aure. Bayan auren sai ya zaman wacce ya auran ' yar wancan mata daya sakane.
To anan Auren ya halatta ko kuma bai halatta ba a bisa ayoyi ko kuma Hadisai na Annabi s.aw?
Amsa: Wa alaikum assalam, idan mutum ya auri mace sai ya sake ta kafin su sadu, ya halatta ya auri 'yarta kamar yadda aya ta: 23 a suratun Nisa'i da kuma hadisin da Tirmizi ya rawaito suka tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Zarewa. 5/6/2016

Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment