August 2018 - NewsHausa NewsHausa: August 2018

Pages

LATEST POSTS

Friday, 31 August 2018

Kalli Yadda Wasu Wasu Barayi Sukama Wata DPO Tsirara A Kasuwa

A wata hira da tayi da manema labarai, wata DPO din 'yan sanda a Abuja ta bayyana yanda wasu 'yan daba suka wahalar da ita, yayin da suka je kama kayan sata a wata kasuwa dake Abuja.

A wata hira da tayi da manema wata DPO din 'yan sanda a Abuja ta bayyana yanda wasu 'yan daba suka wahalar da ita, yayin da suka je kama kayan sata a wata kasuwa dake Abuja. CSP Nana Bature Garba tace sai da aka gargade ta akan cewar kar ta sake ta shiga kasuwar Panteka dake unguwar Mpape a birnin Abuja, saboda irin hadarin da ke cikin kasuwar.

Ga dai irin bayanin da ta yiwa manema labarai. "Sunana CSP Nana Bature Garba. Ina so na bayyana muku labarin abinda ya faru dani lokacin da na ke DPO Mpape. Lokacin dana je Mpape suna da wata ka'ida cewa baka isa ka shiga kasuwar Panteka ka kama wani ba, ko ka dauki kayan mutane da aka sace a wajen.

Ni kuma sai nace ya za'ayi a ce 'yan sanda na wuri ace ba za'a shiga wurin ba, ni kam sai na shiga. Na tara 'yan sanda nace mu je. Ko kafin muje wurin ma mutanen Mpape suka dinga zuwa suna gargadina akan kada mu shiga wurin.

Abinda nake tunani shine, kamar akwai masu kai musu rahoto, domin kuwa ina kyautata zaton, kamar sun samu labarin muna zuwa. Domin kuwa muna zuwa wurin suka zagaye mu, suka sakar mana karnuka, muna budewa karnukan wuta, kamar daman abinda suke jira kenan, suka dinga jifan mu da duwatsu da sanduna ta ko ina a jikin mu.

A cikin 'yan sanda mu 18 da muka je wurin babu wanda bai ji ciwo ba. Sai da suka yi mana dukan tsiya, domin ko ni kaina da nake DPO sai da suka yaga min kayana suka yi mini tsirara, sai wata mata ce ta zo ta bani zani na daura. Sannan muka yi waya aka kawo mana agaji, kafin 'yan agajin su zo mun riga mun galabaita, ko tashi bama iya yi.

Da Allah ya bani lafiya, na ce ni kuwa wannan wurin ko menene a ciki sai na sani, na ce sai na sake komawa, saboda haka sai na rubutawa kwamishinana, na ce ina so a taimake ni mu samu a zo mu sake shiga wannan wurin, muga abinda za'a iya yi.

Sai ya ce to, tun daga wannan lokacin muka buda hanya, muke samu muna shiga wannan wuri, duk wanda aka yiwa sata zamu je wurin ayi bincike a kama wanda yake da laifi." Wannan shine takaitaccen labari na da gwagwarmayar dana sha a kasuwar Panteka dake Mpape Abuja.

Kalli Hoton Mawaki Davido Ya Fara NYSC a Lagos

Shahararren mawakin nan, David Adeleke Adedeji wanda ake kira da Davido yana ci gaba da jan hankalin ma'abota shafukan sada zumunta a Najeriya bayan da ya fara aikin yi wa kasa hidima wato NYSC a ranar Laraba.

Mawakin ya shiga sansanin masu yi wa kasa hidimar na unguwar Iyana Ipaja a jihar Legas.

Wajibi ne dai kowane dan Najeriya wanda bai wuce shekara 30 da haihuwa ya yi aikin yi wa kasa hidimar bayan kammala digiri da babbar difloma.

Davido ya rika wallafa hotunansa sanye da kakin 'yan yi wa kasa hidimar.

Wasu hotunan da aka ringa watsawa a shafukan sada zumunta sun nana mawakin wanda shahararren attajiri ne, tare da masu yi wa kasa hidima sun yanyame shi.

Ace singer and celebrity, Adeleke David Adedeji (DAVIDO), LA/18B/6389 as he registered for 2018 Batch 'B' Stream 2 Orientation Course at the Lagos NYSC Camp,Iyana Ipaja,Agege.

Posted by NYSC LAGOS on Tuesday, 28 August 2018

Wednesday, 29 August 2018

Kalli Yanda Kunama Ta Maqale Jikin Wandon Wani Mutumi

A rika duba kaya kamin a saka

Wannan hoton na fadakarwa ne akan a yi hankali da saka kayan da suka jima a jiye ba tare da dubawaba, kamar yanda ake iya gani a hoton, ga kunama nan tayi lamo a jikin wandon inda ace da tsautsai ya saka, saidai aji wani labarin daban.

Shafin Sarauniyane ya wallafa hoton wannan wando da kiran mutane akan a rika lura.

Manyan sarakunan Najeriya guda 4 da ba su da aure

Manyan sarakunan Najeriya guda 4 da ba su da aure
Sanannen abu ne a kusan kowanni kabila ko addini cewa aure muhimmin abu ne, kuma ita cikar kamalar mutum mace ko namiji, hakan ta sanya aure ya fi zama cancanta ga shuwagabanni, don haka zaka ga da zarar wani ya samu mukami sai yayi aure, ba duka aka zama daya ba, inda a Najeriya aka samu wasu manyan sarakuna dake mulkin manyan masarautu amma basu da aure, ku biyo mu.

Wadannan sarakunan basu da aure har yanzu, duk da suna gudanar da mulkin dubunnan al’umma.

Sarkin Gombe

Sarkin Gombe, mai martaba Alhaji Abubakar Shehu na Uku ya dane mukamin Sarki kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Gombe ne yana shekaru 39 bayan mutuwar mahafinsa, Alhaji Sheu Abubakar kimanin shekaru uku da suka shude.

Sai dai duk da cewa a yanzu haka yana da shekaru 42, amma Sarki Abubakar bai taba aure ba, kuma bashi da mata a ko ina, a duk fadin jihar Gombe da ma Najeriya gaba daya, wanda hakan na damun al’ummar jihar Gombe.

Majiyoyi sahihai sun tabbatar da cewar a yayin da za’a nada shi sarautar Sarkin Gombe, an so a daura masa guda daga cikin yayan Sarkin Musulmi amma abin bai yiwu ba, haka zalika aurensa da diyar Sarkin Dukku, Gimbiya Aisha Musnan saura kiris, amma abin bai yiwu ba.

Amma duk da wannan nakasu, Sarki Abubakar yana da kyakkyawar alaka da jama’ansa, talakawansa na kaunarsa sakamakon taimakon dayake musu.

Sarkin Ife (Ooni Ife)

Sarkin Ife na daga cikin matasan sarakuna a Najeriya, kuma shine shugaban majalisar sarakunan jihar Osun gaba daya, yayi aure har sau biyu, amma auren bai dade ba, aurensa na karshe a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2016 aka yi, inda ya auri Sarauniya Wuraola Zaynab Otiti Obanor, amma suka rabu a shekarar 2018.

Tun bayan wannan mutuwar aure wanda hatta sadakin daya biya saida aka dawo masa dasu, Ooni mai shekaru 43 bai sake wani auren ba, sai dai ana samun jita jitan cewa ya kusa angwancewa, inda ake danganta shi da Sarauniyar Kyau Tobi Philips.

Sarkin Agbor (Dein Agbor)

Dein na Agbor, Sarkin masarautar Agbor dake jihar Delta, Benjamin Ikechukwu Kiagborekuzi I shine wanda ya zama Sarki tun yana karamin yaro dan shekara 2, 1979 bayan rasuwar mahafinsa, a yanzu yana da shekaru 42 amma shima har yanzu bashi da mata.

Dayake Benjamin ya dade a kasar waje yana karatu, don haka tun bayan dawowarsa Najeriya a shekarar 2001 ake zargin wai buduwarsa baturiya zai aura, amma mambobib majalisarsa sun ce atabau ba zai auri baturiya ba, yar kabilar Agbor zai aura.

Sai dai shima Basaraken yana da girma sosai a idon jama’ansa, suna matukar kaunarsa tare da mutunta shi.

Sarkin Ubulu-Uku (Obi Ubulu-Uku)

Sarkin al’ummar Ubulu Uku dake jihar Delta, Oba Chukwuka Akaeze I ya dare karagar mulki ne a shekarar 2016 yana dan shekara 15 bayan miyagu masu garkuwa da mutane sun kashe mahaifinsa Edward Ofulue III, ma’ana yanzu shekararsa 17, inda ya kwashe shekaru biyu yana mulkar jama’a amma bashi da aure.

Amma a iya cewa karancin shekaru ne suka hana Oba Akaeze aure, don kuwa a yanzu haka yana kasar waje yana karatu, kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.
Naij.com

Labari me matukar ban mamaki: Shekaru 4 bayan aure sunata jima'ai amma har yanzu matar na nan da budurcinta


Duniyarnan sai mutum yayi tunanin ya gama jin abin mamaki sai wani sabo ya fito, wani labarine daya fito daga kasar China ke bayyana wasu ma'aurata da sukayi aure sama da shekaru 4 amma matar tana nan a sabuwar budurwarta saboda sunata yin jima'ai ba ta daidaiba a rashin sani, damuwar rashin haihuwa da suka shiga ciki ce ta sa labarin ya bayyana.

Ma'auratan wanda ba'a bayyana sunayensu ba saidai shekaru, matar tana da shekaru 24 mijin kuwa yana da shekaru 26, kamar yanda kafar watsa labarai ta Mirror ta kasar Ingila ta ruwaito.

Sunje asibiti sukawa likita korafin cewa suna ta jima'ai akai-akai tun bayan aurensu, yanzu shekaru 4 kenan amma babu maganar daukar ciki. Likitar da suka samu me suna Liu Hongmei ta bayyana cewa ma'auratan matasane kuma suna da lafiya dan haka abin da ban mamaki.

Matar ta mata korafin cewa tana jin zafi sosai lokacin jima'in amma saboda son haihuwa take jurewa.

Likita Liu ta bayyana cewa, ta sa a bincika matar sai suka gano wani abu me matukar ban mamaki, abinda suka gano kuwa shine matar haryanzu budurcinta na nan kamar budurwar da bata san namiji ba.

Da bincike yayi tsanani sai aka gano ashe ta dubura suke jima'ai shiyasa bata dauki ciki ba.

Bayan gano hakane, likita Liu ta zaunar da ma'auratan ta musu hudubar yanda ake jima'ai sannan ta basu littafin dake koya ilimin jima'i.

Da take hira da manema labarai, likitar tace, abin mamakine kuma ba'a cika samun irin wannan lamari ba ace ma'aurata sunyi aure tsawon shekara 4 amma basu san yanda ake daukar ciki ba.

Bayan 'yan watanni kadan sai ga ma'auratan sun dawo da kyautar kwai 100 da kaza ga asibitin saboda matar ta dauki ciki.

Kalli Hoton Hadiza Gabon daya birge

Hoton Hadiza Gabon daya birge

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wannan hoton nata da ya kayatar, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

Kalli Zafafan Hotunan Jaruma FATI WASHA


Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Washa kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da tasha kyau, tubarkallah,muna mata fatan Alheri.



Tuesday, 28 August 2018

Kalli yanda wani mutum yaje sayen mota da kudin karafa

ALLAH DAYA GARI BAMBAN..

Wani dan kasuwar kasar China ne ya je sayen sabuwar mota da kudaden karafa har 100,000 wanda ya dauki ma'aikatan kamfanin su hudu awowi 12 kafin su kammala kidayar kudaden.



Maryam Gidado tasha ruwan Allah wadai akan wannan hoton


Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado kamar kowace jarumar fim din Hausa, takan saka hotuna lokaci zuwa lokaci a dandalinta na sada zumunta kuma masoyanta sukan yaba, saidai a wannan lokacin labari ya sha ban-ban, dan kuwa wannan hoton ya jawo mata surutai daga masoyan nata.

Da dama da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan hoto sun ce bai dace ba sam musulma ta dauki irin wannan hoto haka kuma har ta nunawa Duniya.
Gadai wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan hoton:

Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado kamar kowace jarumar fim din Hausa, takan saka hotuna lokaci zuwa lokaci a dandalinta na sada zumunta kuma masoyanta sukan yaba, saidai a wannan lokacin labari ya sha ban-ban, dan kuwa wannan hoton ya jawo mata surutai daga masoyan nata.

Da dama da suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan hoto sun ce bai dace ba sam musulma ta dauki irin wannan hoto haka kuma har ta nunawa Duniya.
Gadai wasu daga cikin ra'ayoyin mutane akan wannan hoton:




Monday, 27 August 2018

Kalli Zafafan Hotunan Fati Shu'uma Tare Da kawayen ta Da suka birge

Wannan wasu sababbin hotuna ne da jaruma fati shu'uma na fitar wanda tayi tare da kawayenta wajen wakar baba bubari da sunka hau wakar ga hotunan,:-







Friday, 24 August 2018

hukuncin wanda yake wasa da azzakarin sa maniyyi ya fito, Ko Kuma matar da take sanya yatsa a cikin farjinta

Malam menene hukuncin wanda
yake wasa da azzakarin sa
maniyyi ya fito ? Ko Kuma matar
da take sanya yatsa a cikin
farjinta ?
Amsa
..... Yin haka bai halatta ba kuma
yana daga cikin manyan laifu a
musulinci.

..... Yana janyowa mai yin hakan
fushi da kuma tsinuwa daga
ubangiji ( S.W.A )

..... Manzon Allah ( S.A.W ) yana
cewa "Mutum bakwai, Allah ya
tsine mu su. Kuma bazai dube su
da rahama ba ranar al-qiyamah.

..... Zai ce mu su Ku shiga wuta
tare da masu shigar ta.

1. Wanda yake yin Luwadi
2. Wanda ake yin Luwadin dashi
3. Mai yin zina da dabbobi
4. Mai yin zina da uwa/Mahaifiya
5. Sannan kuma yayi da 'yar ta
6. Mai yin zina da hannayen sa
(wato mai yin wasa da azzakarin
sa da kuma
7. mace mai yin hakan ga al'aurar
ta)

.....sannan shi kuma wannan aiki
yana daga cikin irin laifukan da
mutanen Annabi Lut ( A.S ) suka
aikata.

...... Sannan kuma an Ruwaito
cewar duk masu yin hakan idan
har basu tuba ba.

..... Zasu tashi a ranar al-qiyamah
Hannayen su dauke da ciki
( wato juna biyu )

..... Sannan kuma Likitoci masu
ilimin sanin lafiyar jikin Bil-adama
sun fadi wasu illoli da dama
wadan da yin hakan yake
haifarwa.

1. Mantuwa mai tsanani
( mantuwar karatu e.t.c )

2. Raunin idanu masu yin hakan
idan basu dai na ba, suka
makancewa kafin wani lokaci
mai nisa

3. Raunin Al-aura duk mai yin
haka, Idan suka yi Aure sukan yi
fama da rashin karfin Azzakari,
saboda duk maniyyin da aka fitar
dashi da gan-gan baya fita gaba
daya. Wannan wanda yayi saura
sai ya daskare maka a cikin
marar ka.

4. Rashin haihuwa: wan an
daskararren maniyyin yana kashe
kwayoyin halitta daga jikin
Namiji ko Mace.

5. Ciwon hauka da Kuma
kaskanci.

Wannan kadan na tsakuro daga
cikin irin illolin da yake haifarwa.
A jikin Namiji ko Mace.

Dan girman ALLAH kayi/kiyi
posting din wannan abin akallah
a cikin friends ka/ki koda guda
10 ne. Yadda kusan kowa zai
samu. Da groups din ka/ki
Wannan wadannan matsalolin a
halin yanzu muna facing din su a
rayuwa,

Allah yasa mu amfana
Via====> SADEEK M BAPPARU

Thursday, 23 August 2018

Kalli Hoton Kwalliyar Sallar Jarumi Adam A Zangi

Kalli Hoton Kwalliyar Sallar Jarumi Adam A Zangi

HoTon Jarumi Adam A zango Kenan Muna Yimai fatan Alheri.

Kalli Hotunan Kwalliyar Sallah ta Jaruma Rahama Sadau

Kalli Kwalliyar Sallah ta Rahama Sadau

Tauraruqar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wannan kayataccen hoton nata da ta saka tana yiwa masoyanta barka da Sallah, tasha kyau, tubarkallah, muna mata fatan Alheri.

Kalli Hotunan kwalliyar Sallah ta Jaruma Maryam Yahaya


Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya kenan a wadannan kayatattun hotunan nata data sha kyau, tubarkallah, ta yiwa masoyanta gaisuwar barka da Sallah, muna mata fatan Alheri.




Monday, 20 August 2018

Labari me taba zuciya na matashin da aka haifa babu kafa

Allah me yin yadda yaso, wani sai yayishi da cikakkiyar halitta da lafiya, wani kuma yayishi da kudi amma ya kwace lafiyar, wani kuma yana cikin rayuwar za'a canjamai fasali, wannan bawan Allahn me suna Zion Clark dan kasar Amurkane da aka haifeshi babu kafa saidai kuma wannan be hanashi yin hobbasa dan cimma burin rayuwarshi ba.

Bayan kasancewar Zion bashi da kafa, kuma ya tasone a gidan riko, yanzu dai yana makarantar sakan direne kuma yana yin wasan kokawa wanda dama shine burinshi.

Labarin Zion ya taba zukatan mutane da dama domin kuwa duk da kalubalen da ya fuskanta a rayuwarshi be yadda ya zama nauyi akan mutane ba, ya tashi tsaye dan ganin ya zama abin alfahari ga jama'arshi.




Saturday, 18 August 2018

kalli kyawawan Hotunan Jaruma Maryam Yahaya Tare Da Kawar Ta

kalli kyawawan Hotunan Jaruma Maryam Yahaya Tare Da Kawar Ta 
 Hoton Jaruma maryama yahaya kenan tare da kawar ta,  munai mata Fatan Alheri


Wednesday, 15 August 2018

Kalli wasu kayatattun kyawawan hoton Rahama Sadau yare da 'yan uwanta

Kalli wani kayataccen hoton Rahama Sadau da 'yan uwanta

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wannan kayataccen hoton nata inda take tare da 'yan uwanta, sun sha kyau, tubarkallah, muna musu fatan Alheri.

Saturday, 11 August 2018

Karanta Kiji Sirrin Yanda Zaki Mallake Mijin Ki

Yar uwa ki bude kunnenki
gawani sirri amma don Allah idan kina da kishiya
ban yafe ku hadu da miji ki musguna mata sabida
idan kinyi wannan me house bazai sake jin dadi
wata mace ba, ki samu busheshiyar kubewarki
cokali uku ki matse lemon tsami aciki da madara
kizauna ki shanye ki dibi kadan ki hada da
dakeken bagaruwa kiyi matsi dashi na awa daya
sai ki wanke to fa ranar oga sai yayi kukan
agagwa
Ana so ko da yaushe idan mijinki zai kusance ki
yaji ki a matse kike, ba''a son lokacin da miji zai
kusanci matarsa ya wuce siririf. Don haka ya ke
da kyau mace ta rika kula da gabanta kar ya
bude. Abubuwan da ke matse mace suna da yawa
misali
Bagaruwan hausa.....ana dafa ta da ganyen
magarya ko ita kadai a rika wanke gaba dashi ko
ki zuba a baho ki zauna a ciki da dumin kaman
30mins a kalla sau biyu a sati
Kanunfari ana dafa shi a sha da zuma da zafi
zafi ko ki jika ya kwana da safe ki tace kisha da
madara da zuma. Ana kuma dafa ta a zauna a ciki
da dumin ta ko a rika tsarki ds ruwan ko kuma a
zuba kanunfari a garwashi a tsugunna shi ma sau
2 a sati
Kwallon mangwaro idan kika fasa zaki ga dan
ciki fari haka, ana busar dashi a daka a kwaba da
zuma arika matsi da shi bayan isha'I idan zaki
kwanta bacci ki wanke ko kuma ki dafa dan cikin
da bagaruwa ki wuni tsarki dashi ko ki zauna a
ciki shima a kalla 3x a sati
Almiski fari ko ja ki daka kanunfari ki tankadr
yai laushi sai ki kwaba da miskin da man zaitun
yawaita amfani dashi na matse mace sosai kuma
kullum hq cikin kamshi....yana gyara macen da ta
haihu sosai musamman da jinin haihuwa ya dauke
ki fara amfani dashi har ki ar'bain...
duk wanda ya karanta bai yi comment ba to
kar ya dauka ya kai wani gun ka bar mun abuna
anan gidan plss.
MEKIKE NEMA BAYAN
SO WAJEN MAIGIDA??? Yar'uwata kigwada
wannan Wallahi wallahi zakisha mamaki indai
NI'IMA ne saidai kifadama wani.
.Ki nemi
Dabino wanda ba busasshe ba (lubiya) da
Kankana mai yashi. kici dabinon sosai sai ki sha
kankana daga baya.ki aikata haka kamar bayan
La'asar
. Kisami man Hulba da pure madara
kota shanu ko peak ta ruwa sai ki hada ki aje yayi
1hr kafin ki kwanta.Idan zaki kwanta sai kisha sai
ki tsaya kamar 3mins saiki kwanta. Kisami
lalle 1cup kisa a ruwa ki dafa sai kijuye kisa a
baho kizauna Wallahi kam zaki matse. ko kinsan
tsarki da Sabulu na iya causing cancer agabanki?
Musamman detol dominshi yana kashe kwayoyine
agaban macce damasu amfani da marar
amfani..kisami KALTUFA(brown venigar) kirinka
tsarki dashi. Kiyi sharing ma yan'uwa mata kema
kisami Lada. Sadakatujjariya
ABUBUWAN DAKESA
MACE
TAFITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA

1.RIKO

Riko shine idan an aikatamata wani laifi kabar
abin aranka batare da kayafe ba.
Uwargida kada kizamo mai riko domin hakan ba
karamin jamaki matsala ba zaiyi musamman idan
mijinki nada saurin fushi . Saboda haka idan abu
yafaru mudinga hakuri domin mata ansanmu da
hakuri da juriya idan akai abu to dazaran ya
wuce to amaida komi ba komi bane domin
aljannarmu tana karkashin su sai sun daga zamu
samu mata mudinga hakuri aduk lamuran mu
sai muga mundace

2. YAWON MITA

Yar'uwa kar zizamto cikin mata masu yawan
mita a gurin maji
Abu baya wucewa ayita dawo da magana baya
wanan zai haddasamaki matsala domin zaki fita
ranshi. Idan abu yawuce to ayi hakuri abarshi
adaina tuna baya

3. FUSHI

Uwargida kar kamto mai yawan fushi ko nunama
miji kincika fushi
Karkimanta Allah da kansa "yace yanatare da
masu hakuri"shin bakison Allah yazamto yana
tare dake kowane lokaci
Yar'uwa kisama ranki hakuri fushi banaki bane
domin karkashin wani kike kowayace zomu zauna
zomu sabane
Hakuri shine ribarmu

4.RASHIN IYA GIRKI

Da anxo maganar girki sai naji tsoro tare da jin
kunya
Haba yar'uwa yakamata ace iyayen mu
nakoyamana girki
Wlh wallahi wlh samun yar aiki ba gata bane
Ina gatan yake kina can kwance yar aiki na saye
zuciyar mijinki da dadan abinci
yar'uwa/uwargida mutashi tsaye mukoyi girki
kodan saye zuciyar miji
Domin namiji nason matar da ta iya girki
Zakiga namiji na gayyato abokanai zuwa gidan
shi don suci abinci saboda yasan bazata bashi
kunya
amma idan baki iyaba fa zai fara tunanin kara
aure wato yayi maki KISHIYA
Hmmm mata mu gyara

5.KAZANTA

Uwargida ayi tsafta kodon lfyr jikinkin
karki manta tsafta nadaga cikin addini
Yar'uwa idan ba tsaftar yazakiyi ibada
Sanan kisani tsafta nasa miji yasoki sanan yaji
bayada kamarki zakiga kowane lokaci yana
manne dake yana shakar kamshinki
Idan kuwa bakida rsafta da yabaki kudin cefane
bakikara ganin shi sai dare domin koyadawo ba
abinda zaigani sai bacin rai har kiginga cewa
yadainasonki aa badaina sonkiyayiba kazantarki
tajawo maki
Sanan kisani kazanta tama mabudin kara aure ce
wato yayimaki kishiya
Pls kozakiyi chatting yazamto kin gyara ko ina
sanan yazamto kema kingyara jikinki da na
yaranki kuma idan mai yadawo abashi kulawa
abar cht
Nidai sholy baruwana
Lokacinda zai karowata baninan ni sholy nafada
nafita

6.KULA DA SHINFIDAR MIJI

Mata muna sakaci wajen bawa miji hakkinsa
kinaso amma kitsaya gulma wai jan aji ina ajin
yake bayan yagama saninki lungu lungu ba inda
baisaniba ajikinki
To wallahi ki gyara ki dinga bashi hakkin shi
yadda yakamata wanan shi zaisa mijinki yasoki
kuma ki mallakeshi

Rushe masallacin China ya jawo takaddama tsakanin Musulmai da gwamnati

Rushe masallacin China ya jawo takaddama tsakanin Musulmai da gwamnati

Daruruwan musulmi a yammacin China na takaddama da hukumomi domin hana rusa masallacinsu.

Jami'ai sun ce masallacin da a ka gama gininsa kwanan nan ba shi da takardun izinin gini a Ningxia.

Sai dai musulman sun ki amincewa, inda daya daga cikin mazauna garin ya ce ba za su "yarda gwamnati ta taba masallacin ba."
China na da musulmi miliyan 23, kuma musulunci ya karbu a yankin Ningxia tsawon karni da dama da suka wuce.

Amma masu fafutikar kare hakki sun ce akwai karuwar nuna kiyayya ga Musulmi a China daga hukumomi.

An gina masallacin ne a wani salo na gabas ta tsakiya, inda ya ke da hasumiyoyi da kubbobi masu tsayi da dama.

Ya a ka fara boren?

Ranar 3 ga watan Agusta, jami'ai su ka buga wata sanarwa da ke cewa za a rushe masallacin da karfi da yaji saboda ba a bayar da izinin tsarawa da gina shi yadda ya kamata ba.

An rarraba sanarwar a shafukan intanet tsakanin 'yan kabilar Hui, kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta Reuters ta ruwaito.

Mutane da yawa sun bukaci sanin dalilin da ya sa hukumomi ba su hana gina masallacin ba, wanda a ka gama shekaru biyu da su ka wuce, in dai har ba a bayar da takardun izinin gina shi ba, kamar yadda wata jaridar kasar Hong-Kong ta ruwaito.

Rahotanni sun nuna cewa an yi zanga-zanga a wajen masallacin ranar Alhamis kuma a ka ci gaba a ranar Juma'a. Hotunan da su ka bazu a shafukan sada zumuntan China sun nuna taron mutane mai dimbin yawa a wajen masallacin.

Har yanzu dai ba a tabbatar ba idan za a fara rushe masallacin ranar Juma'a kamar yadda a ka tsara, ko kuma idan an cimma matsaya.

Kafar watsa labaran kasar China ba ta ce komai ba har yanzu.
BBChausa.

An kera kumbo na farko Wanda zai iya shiga cikin Duniyar Rana

An kera kumbo na farko Wanda zai iya shiga cikin Duniyar Rana

Cibiyar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, ta kaddamar da kumbonta da aka kera kan dala biliyan daya da rabi, da zai zama na farko da ya kai ga duniyar Rana.

Kumbon wanda NASA za ta harba shi zuwa zuwa sama daga jihar Florida a yau Asabar, zai gudanar da bincike ne kan wasu sirrika na tsakiyar rana, da ake kira da 'Corona', wanda masana sukai ittifakin, zafinsa ya ninka na wajen rana sau 300.

Kumbon wanda aka sanyawa suna The Parker Solar Probe zai kuma taimaka masana sararin samaniya da ke duniya, wajen hasashen lokacin da kakkarfar guguwar da ke tsananin gudu a zagayen rana ka iya ketowa doron duniyaduniya .

Kumbon dai gina shi da kaurin inchi hudu da rabi, da ke karfin bashi kariya daga karfin zafin rana mafi tsanani da ake ji a doron duniya da ya ninka sau 500, wato kwankwacin zafin digiri 1, 371 a ma’aunin Celcsius.

Ana sa ran da zarar kumbon ya kusanci Rana, gudunsa zai karu zuwa saurin tafiyar kilomita dubu 700, 000 cikin awa guda, abin da zai bashi damar zama abin da dan adam ya kera mafi sauri a tarihi.
RFIhausa.

Ku Kalli Hoton Hadiza Gabon da mahaifinta


Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wannan hoton tare da mahaifinta,

 ta bayyanashi a matsayin masoyinta na farko, muna fatan Allah yakai Rahama kabarinshi, muna mata fatan Alheri.

Friday, 10 August 2018

Kalli Wasu Kyawawan Hotunan Rahama Sadau


Tauraruwar fina-finan hausa da turanci, Rahama Sadau kenan a wadannan kayatattun hotunan nata da ta sha kyau.