November 2016 - NewsHausa NewsHausa: November 2016

Pages

LATEST POSTS

Wednesday, 30 November 2016

HUKUNCIN SADUWA DA MAI CIKI |DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCI SADUWA DA MAI CIKI


Tambaya :
Malam na kanji wasu mutane na fadar cewa ba ya halatta idan
matar mutum tana da juna biyu yayi jima'i da ita har sai ta haihu meye gaskiyar maganar?

AMSA :
To dan'uwa ya halatta a sadu da mace lokacin da take da ciki, saboda fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud : 1847

Ibnul kayim yana cewa : "Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa" Tahzibussunan 1\193 .

Saidai masana likitanci suna cewa: Ba'a so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya akanta yana iya wahalar da yaron .

Sannan yawanci mata basu cika son yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a karanta saduwa a wadannan lokutan.

Allah ne ma fi sani .

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA


Tambaya :
Assalamu alaikum. wata tambaya nake da ita Dr. Wai shin meye gasiyar hukuncin wanda ya sayi kaya a lokacin da suke araha ya boye da niyyar in sunyi tsada ya fito da su ya sayar dan ya sami riba mai yawa? Allah shi dada budi amin

Amsa :
To dan'uwa ya zo a hadisi cewa : "Ba wanda yake boye kaya sai mai zunubi" Tirmizi ya rawaito shi a : 3\567, kuma ya kyautata shi, saidai malamai sun yi sabani akan irin kayan da ya haramta a boye da wadanda ba su haramta ba :

1. Akwai wadanda suka tafi cewa : duk wani abu da mutane suke bukatarsa to bai halatta mutum ya siya ya ajjiye ba, da nufin sai yayi tsada ya fito da shi, don haka har tufafi da magunguna bai halatta a boye su ba, saidai idan ya siya ne da nufin ya yi amfani da su nan gaba.


Ko kuma iyalansa, Wannan shi ne maganar Abu-Yusuf babban almajirin Abu-hanifa, kamar yadda yazo a littafin : Daurul-kiyam wal'aklak fil-islam shafi na : 295. Sannan ita ce maganar Malik a Mudawwanah kamar yadda ya zo a : 4\291.


2. Akwai malaman da suka tafi cewa ya halatta a boye abin da yake ba abinci ba ne da mutane za su ci su rayu, kamar barkono, zabibi, mai, da sauransu, saboda yawanci mutane suna cutuwa ne idan aka boye abinci. An rawaito wannan daga Abdullahi dan Mubarak da Sa'id dan Musayyib kamar yadda Tirmizi ya ambata a Sunan dinsa 3\567 sannan ita ce maganar Shafi'iyya da Hanbaliyya , kamar yadda ya zo a
Raudatu Addalibiina 3\411 da kuma Almugni 4\154


Wasu malaman suna rinjayar da maganar farko, amma idan ba siyan abin ya yi ba, ya mallake shi ne ta wata hanya, ko kuma ya noma sai ya boye har ya yi tsada sannan ya siyar, to wannan bai haramta ba, ko da kuwa abinci ne, har wasu malaman ma sun hakaito ijma'in malamai akan halaccin haka, kamar yadda ya zo a Jami'ussagir shafi na : 481


Allah ne mafi sani

    Amsawa
Dr jamilu zarewa

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA| DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA


Tambaya :
Assalamu alaikum. wata tambaya nake da ita Dr. Wai shin meye gasiyar hukuncin wanda ya sayi kaya a lokacin da suke araha ya boye da niyyar in sunyi tsada ya fito da su ya sayar dan ya sami riba mai yawa? Allah shi dada budi amin

Amsa :
To dan'uwa ya zo a hadisi cewa : "Ba wanda yake boye kaya sai mai zunubi" Tirmizi ya rawaito shi a : 3\567, kuma ya kyautata shi, saidai malamai sun yi sabani akan irin kayan da ya haramta a boye da wadanda ba su haramta ba :

1. Akwai wadanda suka tafi cewa : duk wani abu da mutane suke bukatarsa to bai halatta mutum ya siya ya ajjiye ba, da nufin sai yayi tsada ya fito da shi, don haka har tufafi da magunguna bai halatta a boye su ba, saidai idan ya siya ne da nufin ya yi amfani da su nan gaba. 

Ko kuma iyalansa, Wannan shi ne maganar Abu-Yusuf babban almajirin Abu-hanifa, kamar yadda yazo a littafin : Daurul-kiyam wal'aklak fil-islam shafi na : 295. Sannan ita ce maganar Malik a Mudawwanah kamar yadda ya zo a : 4\291.

2. Akwai malaman da suka tafi cewa ya halatta a boye abin da yake ba abinci ba ne da mutane za su ci su rayu, kamar barkono, zabibi, mai, da sauransu, saboda yawanci mutane suna cutuwa ne idan aka boye abinci. An rawaito wannan daga Abdullahi dan Mubarak da Sa'id dan Musayyib kamar yadda Tirmizi ya ambata a Sunan dinsa 3\567 sannan ita ce maganar Shafi'iyya da Hanbaliyya , kamar yadda ya zo a
Raudatu Addalibiina 3\411 da kuma Almugni 4\154

Wasu malaman suna rinjayar da maganar farko, amma idan ba siyan abin ya yi ba, ya mallake shi ne ta wata hanya, ko kuma ya noma sai ya boye har ya yi tsada sannan ya siyar, to wannan bai haramta ba, ko da kuwa abinci ne, har wasu malaman ma sun hakaito ijma'in malamai akan halaccin haka, kamar yadda ya zo a Jami'ussagir shafi na : 481

Allah ne mafi sani

    Amsawa

Dr jamilu zarewa

Tuesday, 29 November 2016

HUKUNCIN MIKEWA MALAMI KO SHUGABA SABODA GIRMAMAWA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN MIKEWA MALAMI KO SHUGABA SABODA GIRMAMAWA



Tambaya:
Mal. Ina tp ne yanzu, kuma idan na je aji yara suna mikewa damin gaishe ni mal. na barsu su cigaba ko na dakatar da su ?


Amsa :
To dan'uwa akwai malaman da suka ta fi akan cewa makaruhi ne a mikewa malami, akwai wadanda kuma suka halatta. Saidai maganar da ta fi ita ce bai hallata malami ya nemi a mike masa ba, saboda fadin Annabi s.a.w. " Duk wanda ya so mutane su mike masa to ya tanaji wurin zamansa a wuta" 

kamar yadda tirmizi ya rawaito shi kuma ya kyautata shi a hadisi mai lamba ta : 2755, Albani kuma ya inganta shi a silsilatussahih
ah lamba ta : 5957 Amma idan aka mikewa mutum ba tare da ya nema ba, to wannan babu laifi ga wanda ya mike da wanda aka mike saboda shi, domin ya zo a hadisi cewa : 


Annabi s.a.w. ya mikewa zaid bn haritha lokacin da ya dawo daga tafiya, kamar yadda ya zo a hadisin da tirmizi ya rawaito shi kuma ya kyautata shi a lamba ta : 2732,

saidai wasu malaman sun raunana wannan hadisin kamar albani a dha'ifuttirmizi 1\326

Allah ma fi sani

Amsawa
Dr jamilu zarewa

INA CIKIN SADUWA DA MIJINA A RAMADHANA SAI ALFIJIR YA KETO !|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

INA CIKIN SADUWA DA MIJINA A RAMADHANA SAI ALFIJIR YA KETO !


TAMBAYA :
Malam muna cikin saduwa da mijina a cikin wannan wata,sai muka ji kiran sallar asalatu , me ye hukuncin azuminmu ?


AMSA :
To 'yar'uwa mutukar kuna jin kiran sallar, kun maza da sauri, kun datse saduwar da kuke yi, to azumin ku yana nan, amma in har kuka ci gaba, da yi ko da na second daya ne, to azuminku ya karye, kuma za ku yi kaffara ku duka, idan kin yi masa biyayya, in kuma takura miki ya yi, to zai yi kaffara shi kadai.
Duba Almugni : 3\65

ALLAH MAFI SANI

Amsawa
Dr jamilu zarewa

Monday, 28 November 2016

MIJINA YA TAKURA MIN MUN SADU A RAMADHANA !|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

MIJINA YA TAKURA MIN MUN SADU A RAMADHANA !

 

 

Tambaya :
Malam yau ina cikin damuwa, saboda na kwanta baccin rana, kawai sai na ji mijina ya danne ni, na yi ta kokarin na kwace amma sai ya ci karfina ya sadu da ni, alhalin muna azumi, don Allah malam a taimaka min da mafita, Allah ya sanyawa zuriyarka albarka

 

 

Amsa :
To 'yar'uwa mutukar yadda kika siffanta, haka abin ya faru, to babu kaffara akan ki, saboda takura miki aka yi, kuma ba ki da laifi a wajan Allah




amma shi kuwa ya sabawa Allah, kuma ya keta alfarmar Ramadhana, 

 

kuma dole ya yi kaffara, ta hanyar 'yanta kuyanga, in bai samu ba, sai ya yi azumin sittin a jere, in bai samu dama ba sai ya ciyar da miskinai sittin, kamar yadda ya zo a hadisin Bukari mai lamba ta : 616.

 

 

Allah ne mafi sani.

     Amsawa

Dr jamilu zarewa

HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN HADA SITTU SHAWWAL DA RAMUWAR RAMADAN

Tambaya :
Malam idan ana binka ramuwar azimi za ka iya niyya biyu : wato da nufin sittu shawwal da ramuwar Ramadhana a guda daya ? don Allah mlm taimaka min da bayani.

Amsa :
To 'yar'uwa kowanne daban ake yinsa, saboda manufarsu ta banbanta, don haka ba za'a hada su da niyya daya ba, kamar yadda ake yi a wankan janaba da wankan juma'a, za mu fahimci haka, a cikin fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi :

"Duk wanda ya azumci Ramadhana sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal, Allah zai ba shi ladan wanda ya yi azumin shekara"
Muslim ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1164, kin ga wannan yana nuna Ramadan daban, sittu-shawwal daban.
Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi :

" Sannan ya biyar da kwanaki shida na Shawwal" ya sa wasu malaman sun tafi akan cewa : bai halatta ayi sittu-shawwal ba, sai bayan an kammala ramuwar Ramadan. Kamar yadda ya zo a : sharhurmumti'i 6\443

Allah ne ma fi sani

    Amsawa

Dr jamilu zarewa

Sunday, 27 November 2016

KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA ! !|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA ! !*

 

*Tambaya*

Assalamu alaikum mal dan Allah ga tambaya nan

Nice nai aure na ya rabu da mijina, wato ya bani takardan saki, kafin ya bani wannan takardar,mun samu matsala na bar gidanshi tsawon shekara daya da wata tara,kuma Daman tsawon zaman mu tare shekara bakwai ban taba samun ciki ba,yaya iddata zata kasance ?

 

*Amsa*

Wa alaikum assalam, Za ta jira tsarki uku, tun da sun taba kawanciyar aure kamar yadda aya ta 228 a Suratul Bakara  ta tabbatar da hakan.     

 

    

           Hukunce-hukuncen Saki suna farawa ne daga lokacin da aka yi saki, ba daga sanda aka samu hatsaniya ba.     


  Allah ya shar'anta idda saboda manufofi da yawa daga ciki akwai: bawa miji damar kome Idan saki daya ne ko biyu, ta yiwu wani daga cikin ma'aurata ya yi nadama, Tare da cewa babban makasudin shi ne tabbatar da kubutar mahaifa, Amma ba shi kadai ba ne.

 

Allah ne mafi sani

 

*Amsawa*

*DR Jamilu Yusuf Zarewa*
25/11/2016

FATAWAR RABON GADO (80)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (80)*

 

*Tambaya*

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh, malam ina da tambaya, mutum ne ya mutu ya bar matan aure biyu da yayye biyar *shakeekai* namiji daya, sauran hudun matane, yaya rabon gadon su zai kasance

 

*Amsa*

  Wa alaikum assalam,  Za'a raba abin da ya bari kashi:4, matansa biyu su dau kashi daya, Ragowar kashi ukun sai a bawa yayyensa tun da duk dakinsu daya, duk namiji ya dau rabbon Mata biyu.

 

Allah ne mafi sani 

 

24/11/2016

*Amsawa*

*DR Jamilu Zarewa*

FATAWAR RABON GADO (79)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (79)

 

Tambaya?

Assalamu alaykum, malam mutum ne ya rasu ya bar Mata 1, da diya Mace 1, sai kanne 6. ubansu 1, sai wasu kanne  7. Uwarsu 1, ya za'a raba gadon sa? 

 

Amsa:
Wa alaikum assalam,  za'a raba abin da ya bari gida: 8, a bawa matarsa kashi daya, 'yarsa kashi hudu, Ragowar kashi ukun sai a bawa 'yan'uwansa da suka hada uba daya.

 

Allah ne mafi sani

 

22/11/2016

Dr. Jamilu Zarewa

Saturday, 26 November 2016

SHIN SAYYIDINA UMAR YA TABA BINNE 'YARSHI ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

SHIN SAYYIDINA UMAR YA TABA BINNE 'YARSHI ?


Tambaya :
Assalamu alaikum malam, shin don Allah ina gaskiyar lamarin da ake cewa : Umar yana kuka wataran kuma sai a ga yana dariya, har aka tambaye shi, sai yake cewa : ya tuna 'yarsa da ya rufe a zamanin jahiliyya shi ne yake kuka ?

Amsa :
To dan'uwa tabbas wannan maganar ta yadu a wajan masu wa'azi da masu huduba akan minbarai, saidai ba ta da tushe, kuma karya ce, saboda abubuwa kamar haka :


1. Masana tarihi sun tabbatar da cewa : matar Umar R.A ta farko a rayuwarsa, ita ce Zainab 'yar Maz'un wacce ta Haifa masa Hafsan da Annabi s.a.w. ya aura, don haka Hafsa ita ce babbar 'yarsa, kuma da ita ake masa alkunya, don haka idan bai rufe babba ba daga cikin 'ya'yansa, ta yaya zai bunne wacce ta zo daga baya ?, tare da cewa :
ita kan ta Hafsan an haife ta ne kafin a aiko Annabi s.aw. da shekara biyar, ka ga kenan abin da ta riska na jahiiliyya ba shi da yawa .


2. Wacce ake cewa Umar ya bunneta da ranta, gaba daya littatafan tarihi ba su fadi labarinta ba, ko su kirga ta a cikin 'ya'yansa ba.
3. Sannan kabilar Adiy wacce Umar ya fito daga cikinta ba su shahara da binne 'ya'ya mata ba, a zamanin jahiliyya.


4. Dogon bincike ya nuna cewa : babu wannan kissa kwata-kwata a cikin littattafan Ahlussunah, asalinta daga littatafan 'yan shi'a aka cirota, don haka su ne suka kirkire ta, dama kuma sun saba yin kage ga sahabban Annabi s.aw.


Allah ne mafi sani .

Don neman Karin bayani duba : Dirasa nakdiyya fi shaksiyati Umar 1/111. ﺩﺭﺍﺳﺔ ﻧﻘﺪﻳﺔ ﻓﻲ ﺷﺨﺼﻴﻴﺔ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﻭﺳﻴﺎﺳﺘﻪ ﺍﻹﺩﺍﺭﻳﺔ 1/111 -

 Amsawa
 Dr jamilu zarewa

SHIN AZUMIN ASHURA YANA KANKARE MANYAN ZUNUBAI ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

SHIN AZUMIN ASHURA YANA KANKARE MANYAN ZUNUBAI ?


Tambaya :
Malam ina da tambaya, Irin ayyuka na azumin ashura arfa, Misali na ashura kaffarane na shekarar da ta gabata, Shin malam yana kankare manyan zunubai irin su shirka, mua'mala da kudin ruwa da sauransu, Malam yaya maganar magabata game da tambayata.


Amsa :
To dan'uwa hadisi ya tabbata daga Annabi s.a.w cewa : Azumin ashura yana kankakare zunubin shekara daya" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1162.

Malamai magabata suna cewa azumin ashura da na Arfa suna kankare kananan zunubai ne kawai, amma manya sai an tuba Allah yake gafarta su, sun kafa hujja da fadin Annabi s.a.w, inda yake cewa : 

"Salloli guda biyar da Ramadhana zuwa Ramadhana suna kankare abin da yake tsakaninsu, mutukar an bar manyan zunubai" Muslim a hadisi mai lamba ta : 233 .

Wannan hadisin yana nuna cewa : sallolin farilla da azumin Ramadhana ba sa kankare manyan zunubai, ka ga kuwa ta yaya azumin nafila kamar na ashura da na ranar Arfa zai kankare su ?
Wannan ita ce maganar Nawawy a littafinsa Alminhaj sharhin sahihi Muslim a 4/308, da kuma Ibnul-kayyim a littafinsa : Aljawabul-kafy shafi na : 13 .

Allah ne mafi sani .

       Amsawa
Dr jamilu zarewa

Friday, 25 November 2016

MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI !|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI !

Tambaya :
Aslm mlm dan Allah ina da tambaya : tun kafin a kama azumi uwata ba ta da lafiya har akayi sallah, rana ta 16 ga watan karamar sallah Allah yayi mata rasuwa, shin za mu ranka mata azumi ko ba sai mun ranka ba ? Allah ya saka da hairi.


Amsa :
To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba, saboda fadin Allah madaukaki :
"Kuma duk wanda yake mara lafiya ko matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban" Bakara aya ta : 185, wato bayan Ramadahana, 

idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka ga wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama ba, don haka sai ya saraya akan shi . .

Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta mutu, to sai makusancinta ya rama mata, saboda fadin Annabi s.a.w.

: "Duk wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa" . 

kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1851. Duba Fataawa nuru aladdarb lamba ta : 247.
Allah ne mafi sani
       Amsawa
  
    Dr.jamilu zarewa

NAMAN DOKI HALAL NE?|DR.JAMILU YUSUF ZAREWA

NAMAN DOKI HALAL NE

Tambaya :
Assalamu Alaikum dan Allah tambayar ita ce shin akwai wani hadith ko Aya wacce ta nuna cewa cin naman [doki] haramun ne?

Amsa :

To Dan'uwa babu wata aya baro-baro ko wani hadisi wanda ya haramta cin naman doki, kuma mafi yawan malamai sun tafi akan hallacin cin naman doki, saboda hadisin Asma'u 'yar Abubakar, inda take cewa :


"Mun soke wani doki a zamanin annabi s.a.w sai muka cinye shi"
Bukhari : 5191
Saidai Ibnu Abbas da Imamu Malik sun tafi akan haramcinsa, saboda Allah ya fada a cikin suratu Annahl aya ta : 8 cewa ya halicci doki ne don a hau, a kuma yi ado, wannan sai yake nuna ba za'a ci ba.


Zance mafi inganci shi ne hallacin cin naman doki, saboda hadisin da ya gabata, sannan ayar da Imamu Malik ya kafa hujja da ita ba ta fito baro-baro ta hana cin doki ba, domin kasancewar an ce ana hawanta ko ana ado da ita, ba ya hana a ci .

Don neman karin bayani duba tafsiri Kurdubi 10\68
Allah ne mafi sani
               AmsawaDr.jamilu zarewa

Thursday, 24 November 2016

NA SHA NONON MATATA , YAYA AURANMU ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

NA SHA NONON MATATA , YAYA AURANMU ? Tambaya : Don Allah malam ya matsayin mutumin da ya sha nonon matarsa, ya aurensu yake ?

Amsa : To dan'uwa Allah madaukakin sarki ya halatta maka jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take haila, don haka ya halatta ka tsotsi nononta mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan halaccin hakan zuwa maganganu guda biyu : 

1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. "Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa" , Bukhari lamba ta : 5102, ma'ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai . 

2. Bai halatta ya sha ba, saboda ko da yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.aw. ya umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure . 

Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya sha nonon matarsa, saidai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau, don neman Karin bayani duba : 

Bidayatul-mujtahid 2\67 Allah ne mafi sani 

Amsawa

 Dr jamilu zarewa






by Abuubakar Rabiu Yari

HUKUNCIN BIN SALLAH DAGA LASIFIKA|DR JAMILU YUSUF JAREWA

HUKUNCIN BIN SALLAH DAGA LASIFIKA Tambaya : Malam gidanmu yana kusa da masallaci, muna jiwo kiran sallah da ikama ta lasipika, ko ya halatta in bi sallar jam'i daga laspika ? 

Amsa : To 'yar'uwa wannan mas'alar ta kasu kashi biyu :

1- Idan ya zama dakinki yana like da masallacin, to tabbas wannan ya halatta, saboda nana A'isha ta bi sallar kisfewa rana daga dakinta, a zamanin Annabi s.a.w. kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta : 184, sannan Abdurrazak ya rawaito cewa : takan bi ragowar salloli daga dakinta" kamar yadda ya zo a littafinsa na Musannaf a hadisi mai lamba ta : 4883, 
saboda dakinta a jikin masallacin yake.



2.idan ya zama dakin ba ya hade da masallacin, to zance mafi inganci shi ne : bai halatta ki bi ba, saboda a zamanin Annabi s.a.w. sahabbai suna haduwa ne a wuri daya ne idan za su yi sallar jam'i, ba sa rarrabuwa, wannan sai yake nuna cewa, 

hakan shi ne siffar sallar jama'i, sannan jera sawu a sallah, wani yana bin wani, dole ne . Allah ne masani . Don neman karin bayani duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al- mushaikih shafi na : 50
   Amsawa
Dr.jamilu zarewa
BY Abubakar Rabiu Yari

Wednesday, 23 November 2016

KA'IDOJIN HADACE AL-QUR'ANI|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

KA’IDOJIN HADDACE AL- QUR’ANI.

• Ya wajaba Dalibi ya rinka yin hadda a wajan malami saboda ya dinga gyara masa. 

• Ka da Dalibi ya dinga haddace abu mai yawa, musamman farkon fara haddarsa, saboda wannan zai jawo ya yi hadda mara karfi, ya kamata ya dinga yi daidai yadda zai iya yin muraja’a sosai, don ya inganta haddarsa.

• Idan dalibi zai fara hadda ya fara daga suratu Annas saboda ta fi sauki.

•Ya rinka yin hadda da al- qur’ani iri daya, saboda zai sa shi ya dinga tuna gurin da kowacce aya ta ke, da kuma tuna inda kowanne shafi ya ke karewa.

• Ya wajaba ya ware wani lokaci na musamman domin muraja'ar abin da ya haddace. 
Dauba khuduwatun ilassa’adah

 Amsawa

Dr.jamilu zarewa

posting  by Abubakar Rabiu Yari

BAMBANCIN TSAKANIN RIIBA DA RIBA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

BAMBANCI TSAKANIN RIIBA DA RIBA

Tambaya :

Don Allah ina da tambaya: wai ma ye riba a musulunci? kuma idan mutum ya siyi abu nera 5 ya halatta ya saida akan nera 8 ? Amsa : To malama riba ta kasu kashi biyu :


1. Akwae ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.

2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa 'yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu. Duka wadannan nau'oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka. 

Amma idan mutum ya sayi abu naira 5, ya sayar naira 8, wannan ba'a kiran shi riba a musulunci, saboda yana daga cikin riibar da Allah ya halatta, saidai ana so idan mutum yana siyar da kaya ya saukaka, Annabi s.aw

yana cewa : "Rahamar Allah ta tabbata ga mutumin da idan zai siyar da kaya yake rangwame", kamar yadda ya zo a hadisin Bhukari mai lamba ta : 2076 

Allah shi ne mafi sani 

     Amsawa
posting by  Abubakar Rabiu Yari

HADISIN KIRAN SALLAH A KUNNEN YARO BAYAN AN HAIFE SHI BAI INGANTA BA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HADISIN KIRAN SALLAH A KUNNEN YARO BAYAN AN HAIFE SHI BAI INGANTA BA


Jiya na yi rubutu akan hukuncin kiran sallah ga yaran da aka haifa, saidai wasu sun yi magangaanu akai. Na gode sosai da bayanan wasu daga cikin 'yan'uwa, 

saidai kamar yadda wasu daga cikinku suka fada addini ba'a yinsa sai da hujja, don haka wadannan hadisai ba su inganta ba, 

shi ya sa ba za'a iya amfani da su ba, wasu daga cikin malamai sun yi amfani da kyautata hadisin da Albani ya yi, da kuma Tirmizi da ya inganta shi, wannan ne ya sa suke amfani da hadisin,

saidai shi Albani ya dawo daga rakiyar hadisin, ga abin da yake cewa : "Na taba kyautata hadisin kiran sallah a kunnen yaro ta hanyar SHAWAHID,
saboda ya zo da sanadi mai rauni a wajan Tirmizy,
sannan Baihaky ya rawaito shi da wani sanadin mai rauni a Shu'abul iman, to amma lokacin da na koma sanadin Shu'abul iman, sai na ga akwai maruwaita guda biyu wadanda ake zarginsu da karya, wannan ya sa na dawo daga rakiyar kyautata hadisin",

saboda a wajan malamai, hadisin da yake akwai MATRUK, wato wanda ake zargi da karya, ba zai karfafi dan'uwansa ba.

Allah ne ma fi sani. 

    *Amsawa*
Dr.jamilu zarewa
posting by Abubakar Rabiu Yari

MENENE HUKUNCIN YIN MASALLATAN JUMA'A GUDA BIYU A GARI DAYA ?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

M
ENENE HUKUNCIN YIN MASALLATAN JUMA'A GUDA BIYU A GARI DAYA ?

Babu wani hadisi ingantacce da ya hana hakan, saidai malamai sun yi sabani a cikin mas'alar zuwa maganganu guda uku:wa



cce ta fi inganci daga ciki, shi ne ya hallata ayi sama da juma'a guda daya a gari daya, mutukar akwai bukatar hakan, kamar ya zama masallacin farkon ba zai ishi mutane ba, ko kuma za'a samu wata fitina idan aka hadu wuri daya, ko ya zama akwai nisa tsakaninsu, ta yadda mutane za su sha wahala,

wajan isowa zuwa gare shi, idan babu bukata abin da ya fi shi ne yin masallaci guda daya a gari daya, saboda daga cikin hikimomin shar'anta juma'a akwai samun hadinkan musulmai, hakan kuwa zai fi tabbatuwa idan suka yi sallah a masallaci guda daya,

wannan itace maganar Ibnu Taimimiyya da Ibnu Bazz da kuma Ibnu Uthaimin, da wasu manyan maluma Allah ya yi musu rahama. 

Amsawa Dr.jamilu zarewa

posting by Abubakar Rabiu Yari

Tuesday, 22 November 2016

HUKUCIN BIN MASABUKI SALLAH|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCI BIN MASABUKI SALLAH Tambaya : Assalamu alaika 
warahamatullah  mallam.

Shin ya halatta abi wanda bai samu cikakken jam'i ba sallah?Misali,na zo masallaci na taradda jam'i na sallar asr saura raka'a 2, da aka idar na mike tsaye don karasa raka'a 2 da ta ragemin, sai ga makararre ya sake hada jam'i da ni.

Shin wannan jam'in na 2 ya halatta? Idan ya halatta,tare da hujjoji. Amsa :

To dan'uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas'alar zuwa zantuka guda biyu :
Malaman Hanafiyya da Malikiyya, sun tafi akan haramcin hakan, saboda ba'a samu magabata suna yi ba, sannan kuma shi masabuki ba liman ba ne, Annabi s.a.w.


kuma ya yi umarni da bin liman ne kawai, sannan hakan zai iya jawowa sallah ta yi karewa, tun da wanda ya bi masabuki, shi ma in ya gama yana ramako wani zai iya zuwa ya bi shi, don haka sai ya haramta . 

Duba Fathul-kadeer 1\277 da kuma Mawahibul-jalil 4\489.


Malaman Shafi'iyya da kuma Hanabila a mafi ingancin zancensu, sun tafi akan halaccin hakan, saboda hadisin Ibnu Abbas lokacin da ya ga Annabi yana sallah da daddare sai ya bi shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :666,

A wannan hadisin za mu fahimci cewa ya halatta mutum ya zama liman a tsakiyar sallah, ko da kuwa bai yi niyyar hakan ba tun daga farko, tun da Annabi s.a.w bai hana Ibnu Abbas ba lokacin da ya bi shi, tare da cewa ba su fara da shi ba, sannan kuma duk lokacin da masabuki ya rabu da liman to yana daukar hukuncin mai sallah shi kadai ne,

don haka sai ya halatta a bi shi .
Duba Nihayatul-muhtajj 2\233 da kuma Insaf 2\36.

ZANCEN DA YA FI INGANCI SHI NE ZANCE NA BIYU SABODA ABIN DA YA GABATA DA KUMA HADISAN DA SUKE NUNA FALALAR SALLAR JAM'I.
Allah ne mafi sani .

  Amsawa
Dr.jamilu zarewa
posting  by Abubakar Rabiu Yari

Monday, 21 November 2016

HUKUNCIN DILLANCIN AURE TAMBAYA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN DILLANCIN AURE TAMBAYA : Malam menene hukuncin 'yan matan da suke bada hotunansu ga tsofafi don su nema musu mijin aure ? AMSA Addinin musulunci ya haramta kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, amma ya halatta ka kalli mace, idan kana so ka aure ta, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" ABU DAWUD Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure : 1. Akwai wadanda suka ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai. 2. Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta. Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura. Ta hanyar bayanan da suka gabata, za mu iya fahimtar cewa aikin dalilin aure ya hallata, amma da sharuda, ga wasu daga ciki : 1. Ya zama hoton ya fito da asalin fuskar matar, bai KWARZANTA ta ba, ta yadda za'a iya yaudarar namijin, ko a rude shi. 2. Ya zama wacce za'a bawa hoton mai amana ce, ta yadda ba za ta nunawa wanda ba shi da nufin aure ba, saboda asali ya haramta ayi kallo zuwa ga matar da ba muharrama ba, sai in akwai lalura, sai ga wanda yake nufin aurarta, wannnan yana nuna cewa, bai halatta asa irin wannan hoton na neman aure ba , a face book, ko a jarida. 3. Ka da hoton ya kun shi fito da tsaraici, ya wajaba a tsaya a iya inda shari'a ta bada umarni. 4. Zai fi dacewa ace mace ce za ta yi dalilin aure, saboda in namiji ne, zai iya fitinuwa da hotunan da yake gani, sai barna ta auku, don haka ita ma macen ya wajaba ta ji tsoron Allah a cikin aikinta.
Allah shi ne ma fi sani
   *Amsawa*
Dr jamilu zarewa

HUKUNCIN ASKE GEMU|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN ASKE GEMU Tambaya : Malam menene hukuncin tsayar da gemu shin wajibi ne ko mustahabbi?, sannan aske shi haramun ne ko makaruhi ne ? wato yinsa banza barinsa banza . Amsa : To dan'uwa Annabi s.aw yana cewa : (Ku sabawa mushrikai, ku cika gemu, ku rage gashin baki), kamar yadda ya zo a hadisin Bukhari mai lamba ta : 5553 da kuma Muslim a lamba ta : 259. Wannan yasa da yawa daga cikin malamai suka tafi akan wajabcin tsayar da gemu da kuma haramcin aske shi, har ma wasu malaman kamar Ibnu Hazm sun hakaito ijma'in malamai akan haka, kamar yadda ya zo a littafinsa na maratibul ijma'i shafi na : 157. Malamai suna cewa har abin da aka rawaito daga wasu sahabbai kamar Ibnu Umar cewa suna rage gemu idan ya kai wani geji, to suna yi ne lokacin hajji saboda suna ganin hakan na daga cikin rage kazantar da alhaji yakan yi bayan ya gama aikin hajjinsa. Sannan gemu na daga cikin abubuwan da ke karawa namiji kwarjini da kyau, shi ya sa za ka ga wanda yake aske shi yana kama da tsohuwar da kyanta ya disashe, kamar yadda Sa'adi ya fadi a Bahjatu kulubul abrar shafi na : 50 Saidai malamai suna cewa idan mutum yana garin da za'a iya kashe shi idan ya bar gemunsa, to zai iya askewa saboda lalura, saidai ya wajaba kowacce lalura kar ta wuce gwargwadonta . Don neman karin bayani duba littafin : Wujubu I'ifa'ul liha . Allah ne mafi sani

FATAWAR RABON GADO (78)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (78)*
*Tambaya*
Assalamu alaykum
qanina ne ya rasu ya bar mata daya da yaransa mata guda uku da mahaifinsa
Shi ne nace ya gadonsu zai kasance ?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida:24, a bawa matarsa kashi:3, sai a bawa 'ya'yansa mata kashi:16, ragowar kashi biyar din sai a bawa mahaifinsa.                                                                      Kashi hudu a matsayin (sudus) dinsa, kashi dayan kuma saboda shi ne Asibi.
Allah nemafi sani
19/11/2016
*Amsawa*
*DR Jamilu Zarewa*

Sunday, 20 November 2016

INA RUBUTAWA DALIBAI WAEC,MENENE MATSAYINA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

INA RUBUTAWA DALIBAI WAEC, MENENE MATSAYINA ? Tambaya : Assalamu alaikum mallam shin ya matsayi na ya ke ? Ina taimakawa wadanda suka dade da gama makarantar sakandare wajen rubuta waec neco etc, kasancewar ba za su iya ba, ko kuma wadanda ba su samu backgorund mai kyau ba a sakandarensu, to shin mallam hakan da matsala? Amsa : To malam rubutawa wani jarrabawa zai shiga cikin algus din da Allah ya haramta, domin za'a baiwa wani aikin da wani ya yi, ba tare da lalura ba, Annabi s.a.w. yana cewa a cikin hadisin Muslim mai lamba ta : 279, "Duk wanda ya yi mana algus to ba ya cikinmu" Rubutawa wani jarrabawa yana da illoli masu dimbin yawa, daga ciki : zai sanya a samu malaman da ba su cancanta ba, sannan zai jawo a cutar da al'umma, domin yanzu idan ka rubutawa wanda yake a fannin liktanci jarrabawa, ka ga zai iya zuwa ya bada magani ko ya yi tiyata ba bisa ka'ida ba. Sannan lalurar da mutane suke kafa hujja da ita ta cewa : dalibai da yawa ba za su shiga jami'o'i ba, in ba'a taimaka musu ta wannan hanyar ba, ba zai iya zama hujja ba a shari'ance, domin za su iya ware wasu watanni su yi karatun mutukar sun yarda da bukatar su ta shiga jami'ar, ga shi kuma barnar da take cikin rubuta musu jarrabawar ta fi maslahar shigarsu jami'a girma, saboda haka sai abin ya zama ya haramta, domin idan kana so ka gane abu haramun ne ko halal, to ka kalli barna da maslahar da take ciki, in maslaha ta fi yawa to ya zama halal, in kuma barna ta fi yawa to ya zama haram, kasancewar za'a iya samun malaman da ba su cancanta ba, yana nuna girman barnar da take ciki, ga kuma kasancewarsa dangwashe da algus din da Allah ya haramta, ga shi kuma zai jawo mutane su zama kasalallu masu ci da gumin wasu. Allah ne ma fi sani.

DR JAMILU ZAREWA

HUKUNCIN YIN DILKA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN YIN DILKA Tambaya : Mace taba da jikinta ga mata yan'uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramunne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar'uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaaa. Amsa : To 'yar'uwa malamai sun yi sabani game da tsaraicin mace ga 'yar'uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai halatta 'yar'uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka. Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shi ne : al'aurar mace ga 'yar'uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al'aurar maza take a tsakaninsu. Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za'a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido . Allah ne maf sani BY
DR.JAMILU YUSUF
POST :
Abubakar Rabiu Yari Sokoto,sokoto state

HUKUNCIN ZAMAN MAKOKI|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN ZAMAN MAKOKI Tambaya : Malam mahaifina ya rasu, sai wani malamin islamiyyarmu ya ce min ba kyau zaman makoki, to gaskiya kaina ya daure, saboda na taso na ga ana yi, kuma idan ban yi ba za'a ce ban damu da mahifinmu ba, malam yanzu yaya zan yi ? Allah ya datar da kai zuwa dukkan alkairai . Amsa : To dan'uwa Allah ya ba mu dacewa gaba daya, tabbas malamai sun tattauna akan hukuncin zaman makoki, saidai sun kasu kashi uku : 1. Akwai wadanda suka tafi akan makaruhi ne, saboda hadisin Jarir RA wanda Imamu Ahmad ya rawaito cewa: "Mun kasance muna kirga taruwa yayin mutuwa da kuma yin abinci ga gidan da aka yi mutuwa daga cikin rurin da Allah da ya haramta" , Musnad : 6905, don haka suna cewa, saidai a hadu da wadanda aka yiwa rasuwa akan hanya ko a kasuwa, ko masallaci ayi musu ta'aziyya, wannan ita ce maganar Shafi'i a cikin Umm 1\318, haka Nawawy a Majmu'u 3\306 . 2. Akwai wadanda suka ta tafi akan cewa bidi'a ne, kamar Ibnul-kayyim a zadul ma'ad 1\527 3. Akwai malaman da suka tafi akan halaccin zaman makoki, saboda hadisin da nana A'isha ta rawaito cewa, lokacin da aka kashe Zaid dan Haritha da Ja'afar dan Abu-dalib Annabi s.a.w. ya zauna a wani wuri, duk wanda ya gan shi zai ga alamun bakin cikin tare da shi, sai wani mutum ya zo ya ce masa : ga matan Ja'afar can suna ta kuka, sai Annabi s.a.w ya umarce shi da ya je ya hana su, su kuma yi hakuri" Bukhari hadisi mai lamba ta : 1299. Wadannan malaman suna cewa : Za'a iya fahimtar hallacin zaman makoki a wannan hadisin a wurare guda biyu : A. Fadin nana A'isha cewa : ya zauna ana ganin alamun bakin ciki tare da shi da kuma zuwan wancan mutumin, dalili ne da yake nuna cewa : yana zaune ne a wurin da mutane suka sani kuma suke zuwa su same shi. B. Kasancewar bai hana matan Ja'afar taruwar da suka yi ba, kawai kukan ya yi umarni da a hana su. Wannan magaanar ta hallaci an rawaitota daga Imamu Ahmad kamar yadda ya zo a Insaf 5\565 da kuma Ibnu-Abdulbarr na Malakiyya,, kamar yadda ya zo a littafinsa na Alkafy 1\283, sannan wasu daga cikin Hanafiyya sun tafi akan haka kamar yadda ya zo a Binaya 3\303 Prof. Khalid Al-mushakih (daya daga cikin manyan daliban Sheik Bn Uthaimin) ya rinjayar da zance na uku, saidai za'a guji abubuwa kamar haka a lokacin wannan zaman : 1. Yawaita yin abinci, da masu karbar gaisuwa, zai yi kyau ya zama makusantansa ne kawai za su amshi gaisuwa. 2. Nisantar yin laccoci a wurin, domin hakan na daga cikin bidi'o'in da ba su da hujja. 3. Nisantar tsawaita zaman, a yi shi gwarwadon bukata. Duba : Fiqhunnawazil na Khalid Al-mushaikih shafi na : 75 Allah ne mafi sani.

Saturday, 19 November 2016

MP3 , WA'AZIN KASA A JAHAR SOKOTO 2016 MP3

JERIN WA'AZIN DARE NA SOKOTO MP3

sai kayi click (danna) a duk inda anka rubuta DOWNLOAD MP3 domin saukar da wa'azin
Mai waazi na farko
DOWNLOAD MP3
Sheikh Ahmad Muhammad Boyi
DOWNLOAD MP3
Dr. Ibrahim Abdullahi R/lemo
DOWNLOAD MP3
Imam Aliyu Telex
DOWNLOAD MP3
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto
DOWNLOAD MP3
Iman Abdullahi Niamey
DOWNLOAD MP3
Sheikh Kabiru Gombe
DOWNLOAD MP3
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
DOWNLOAD MP3
Sheikh Abdullahi Bala Lau
DOWNLOAD MP3
Ayi sauraro lafiya.
Ku cigaba da kasancewa da kasancewa a shafinmu na sadeeqmedia.ml

TUNKUDE ZARGI TUSHE NE A SHARI'A!!|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*TUNKUDE ZARGI TUSHE NE A SHARI'A!!*
*_Tambaya:_*
Slm, Malam,Mutum ne yake rike da dukiyar marayu, wadda yawanta ya kai a fitar da zakka, to Malam Ya halatta idan an fitar da zakkar ya rike  ya yi amfani da ita?.
*_Amsa:_*
Wa alaikumassalam, Ya halatta mutukar yana cikin wadanda suka cancanci zakka, Amma da zai dauki wani Bangare ya bawa wani daban zai yi kyau, saboda tunkude zargi tushe ne a shari'a.
Allah ne mafi sani.
Amsawa: *_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
18/11/2016

Friday, 18 November 2016

FATAWAR RABON GADO (77)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (77)
Tambaya?
Assalamu Alaikum!
Dan Allah a taimaka min da wannan tambayar :
Yaya Rabon gadon wadda ta mutu ba ta yi aure ba amma ta bar uwarta da yan'uwa shakikai da liabbai?
Amsa:
Wa alaikum assalam
za'a raba abin da taa bari gida: 6, a bawa babarta kashi daya, ragowar kashi biyar din sai a baiwa 'yan'uwanta shakikai in har akwai namiji a ciki, in kuma duk mata ne sai a ba su kashi: 4, ragowar kashi dayan a bawa 'yan'uba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani
17/11/2016
DR JAMILU ZAREWA

Maganar Gaskiya AKan Tsotar Al'aura Ga Ma'aurata ( Oral sex) Dr jamilu Yusuf Zarewa


MAGANAR GASKIYA AKAN TSOTSAR AL'AURA GA MA'AURATA ( Oral sex) :
By Anas Assalafy Fagge :

An tambayi dan uwa Dr Jamilu Zarewa dangane da halaccin tsotsar al'aura ga ma'aurata kuma Dr, Allah ya saka masa da alheri ya bada fatawar halacci, duba da dalilai da suke nuni akan haka.
Bayan yaduwar wannan fatawa a kafar sadarwa ta zamani ( social media) se daya daga cikin 'yan uwa malamai yayi rubutu akan wannan fatawar ta Dr Zarewa kuskure ce, shima ya kawo dalilansa,
Lallai wannan shine ilimi kuma haka manhajin mu yake.
Amma maganar gaskiya itace fatawar halaccin, kamar yadda Dr Zarewa yayi fatawa.
Ga kadan daga cikin dalilai akan halaccin hakan ( Oral sex) :

1- Imamaul-bahuty ya fada a littafin "Alkashf" 5/209:
" alkali Abu ya'ala alhanbaly yace : " sunbantar farjin mace ya halatta kafin jima'i, an karhanta bayan gama jima'i ".

2- imamul-mardawy ya naqalto a cikin Al-insaaf 8/33 yace : daga A'da' yace : " za'a iya lasar farjin ko sumbantarsa.

3- wannan itace fatawar Alfatuhy ya bayar a cikin Muntahal-iradaat 4/55.

4- Imamu Alqurduby ya naqalto a cikin Tafsirin sa 12/231 :
" mutane sunyi sabani wajen halaccin mutum yaga al'aurar Matar sa zuwa magana biyu : a ciki yake cewa " malam Asbag daga cikin malaman mu yace: " ya halatta ga Miji ya lashi (farjin) Matar sa da harshe".

5- Imam Assuyudy a cikin "shaqa'iqul-utrujj" shafi na 107:
" an tambayi Asbag : shin Miji ze iya kallar farjin Matar sa yayin jima'i? Se yace:
" eh, ze iya lasa, yana nufin da harshen sa, babu laifi.
Daga cikin malaman wannan zamanin wadanda suka tafi akan halaccin hakan akwai:

* As-sheikh Aliyu jum'ah
* ustazu Aldoktor Ahmad alkardy
* As-Sheikh Dr saleh bn Muqbil
A taqaice wannan itace magana ta gaskiya akan halaccin tsotsar al'aura ga ma'aurata.      

                                              27/1/2016
Allah ne mafi sani.

NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI!!!!|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

NAMIJI ZAI IYA YIN KUNSHI   ! ! ! !
Tambaya?
Assalamu alaykum Warahmatullahi, Da fatan malam yana lafiya,
Malam ya halatta namiji yayi kunshi?
Amsa:
Wa alaikum assalam
Ya halatta namiji ya yi kunshi a gemunsa da kansa, da launin da yake ba baki ba, kamar yadda Annabi  s.a.w. ya yi umarni a yiwa Abu-Khuhafa mahaifin sayyadi Abubakar R.A lokacin da ya musulunta ranar bude Makka a hadisin Ibnu Hibban mai lamba: 5472 Wanda Shuaibu Al'ar'na'u'd ya inganta.
Ya wajaba namiji ya nisanci duk wani kunshi da zai zama kamanceceniya da mata, saboda Allah ya la'anci namijin da yake kamanceceniya da mata kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 2784.                                                                                                                            Yana daga cikin ka'diojin da ya kamata a sani cewa: Kamanceceniya da mata yana iya banbanta daga wuri zuwa wuri, yana sabawa daga al'ada zuwa wata.
Allah ne mafi sani
15/11/2016
DR. JAMILU ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (76)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (76)*
*Tambaya*
Assalamu alaikum. DR barka da yamma......
Tambaya
Mutum ne ya rasu ya bar mata daya da 'ya'ya maza biyu da mata hudu, ya za'a raba abinda ya bari?
Allah ya saka da alkhairi
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida:8, a bawa matarsa kashi daya, ragowar sai a baiwa 'ya'yan nasa su raba, duk namiji zai dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi sani
14/11/2016
*Amsawa*
*DR Jamilu Zarewa*

Wednesday, 16 November 2016

FATAWAR RABON GADO (75)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (75)*
*Tambaya*
Assalamu alaikum. Allah ya karawa DR lafiya.tambaya : mutum ne ya rasu ba shi da uwa da uba, saidai ya bar yayyensa da mata da maza da yaro namiji da kuma matarsa yaya rabon zai zama ?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida takwas, a bawa matarsa kashi daya, Ragowar kashi bakwan sai a bawa dansa saboda shi asibi bi ne.                                                                                              'Yan'uwa ba sa gado mutukar mamaci yana da *DA* namiji.
Allah ne mafi sani.
10/11/2016
*Amsawa*
*DR Jamilu Zarewa*

Monday, 14 November 2016

ZAN IYA AURAN WANDA IYAYANSA BA MUSULMI BA ?|DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

*ZAN IYA AURAN WANDA IYAYANSA BA MUSULMI BA ?*
*_Tambaya:_*
Assalamu alaikum, Dr ya halatta mace ta auri wani wanda Baban shi ba musulmi ba ne?, amma Mahaifiyar shi musulma ce?
*_Amsa:_*
Wa alaikumus salam,  Ya hallata mana ko da kuwa duka iyayansa arna ne.     
Babban abin lura a wajan aure shi ne addinin Wanda ya zo neman aure, saboda fadin Annabi, sallallahu alaihi wa sallama: *_"Idan Wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku, to ku aura masa"._* Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 1084, kuma Albani ya kyautata.
In kika lura za ki ga hadisin ya yi magana ne akan mutumin ba iyayansa ba.                                                                Akwai sahabban Annabi, sallallahu alaihi wa sallama, da yawa wadanda iyayensu ba musulmai ba ne, amma wannan bai hana a aura musu 'ya'ya ba, irinsu Sayyadina Aliyu bn Abu-Dalib da Abu-Ubaidah da saurasu.           
Mahaifin sayyidina Aliyu Abu-dalib bai musulunta ba, Amma kuma an aura masa shugaban Matan Aljanna Nana Fadima, Allah ya kara yarda ga mata da mijin.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa: *_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
12/11/2016

BREAKING NEWS:Former Sultan of Sokoto Dasuki dies

The 18th Sultan of Sokoto Alhaji Ibrahim Dasuki has passed on. He died Monday night in an Abuja hospital, family sources confirmed to Daily Trust.
Details later...

LABARI MAI DADI:WA'AZIN KASA A JIHAR SOKOTO!!!!

WA'AZIN KASA A JIHAR SOKOTO!!!
Shugaban Kungiyar Izalar Naijeriya,
Ash'Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau
Shugaban Majalisar Malamai, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Daraktan 'Yan Agaji, Injiniya Mustapha Imam Sitti
A madadin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunna ta tarayyar Najeriya, Na gayyatar jama'a zuwa gagarumin wa'azi na kasa da za a yi Insha Allah a Sokoto cibiyar daular Usmaniyya ranar asabar 19 zuwa lahadi 20 ga watan nan na Nuwamba 2016 mai taken "GUDUNMAWAR MALAMAN ISLAMA WAJEN YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA "
A lokacin wannan wa'azi da malamai da alarammomi za su gabatar.
Dr.Mansur Ibrahim Sokoto zai gabatar da makala mai taken “ Gudunmawar daular Usmaniyya wajen yada Sunnah a nahiyar Afurka"
Sai kuma Prof. Isa Maishanu Yabo zai gabatar da takardar sa mai taken "Gudunmawar malaman Islama wajen yaki da cin hanci da rashawa"
Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe zai gabatar da na sa wa’azin da taken "Cin hanci da rashawa katafilar rushe al'umma"
Sauran Malaman da Ake sa ran zasu gabatar da wa'azi sune:
-Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe
-Sheikh Dr. Alhassan Sa'id Adam Jos
-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Habibu Yahaya Kaura
-Sheikh Rabi'u Aliyu Daura
-Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan
-Sheikh Barr Ibrahim Sabi'u Jibia
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Khalid Usman Khalid Jos
-Sheikh Abdulbasir Isah U/Kawo
-Sheikh Bello Yabo Sokoto
-Ustaz Albaniy Samaru Zariya
-Ustaz Ibrahim Idris Darus-Sa'ada
-Ustaz Imam Ibrahim Lawal Osama Abuja
-Ustaz Tajuddeen Ibadan
-Ustaz Abubakar Baban Gwale
-Ustaz Dr. Ibrahim R/Lemo
-Ustaz Dr. Rabi'u R/Lemo
-Ustaz Dr. Abdulmudallib Ahmad
-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Isma'il Maiduguri
-Alaramma Bashir Abubakar Gombe
-Alaramma Suleiman Azare
-Alaramma Ilyasu Birnin Gwari
Sanarwan ta fito ne daga Ofishin sakataren kungiya ta kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe
Allah ya bada ikon Zuwa Amin.
Jibwis Nigeria.
14/Safar/1438
14/November/2016

Thursday, 10 November 2016

FATAWAR RABON GADO (74)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*FATAWAR RABON GADO (74)*
*Tambaya*
Assalamu alaikum malam mutumne Allah yaimai rasuwa bashida kowa sai yaiyi guda uku kuma dakinsu daya dan Allah yaya rabon gadonsu zai kasance nagode
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari kashi uku, kowannensu ya dau kashi guda.
Allah ne mafi sani
09/11/2016
*Amsawa*
*DR Jamilu Zarewa*

Wednesday, 9 November 2016

YAUSHHE AKE RAKA'O'INN AL-FIJIR?|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

YAUSHE AKE RAKA'O'IN AL-FIJIR?
Tambaya?
Assalamu Alaikum Malam Allah ya kara illimi, Dan Allah tambaya nake akan lokacin yin raka'atul fajir?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
Annabi s.a.w yana yin Raka'o'i' Fajir bayan fudowar alfijir na gaskiya kafin ya yi sallar Asuba.
Wanda lokaci ya kurewa bai yi kafin sallar asuba ba, zai iya Ramawa bayan ya kammala sallar Asuba, saboda Annabi s.a.w. ya ga wani mutum yana sallah bayan kammala sallar Asuba, sai ya tambaye shi, sai ya ce rakatanil Fajir yake ramawa, sai ya kyale shi, Bai masa inkari ba.
                                                                  Allah ne mafi sani.
6/11/2016
DR. JAMILU ZAREWA

TANA YIWUWA DAN ADAM YA YI MAGANA DA ALJANI TA HARSHEN MARA LAFIYA|DR IBRAHIM JALO JALINGO

 .
Ahmad da Haakim suka ruwaito, da hadithin Uthman Bin Abil Ass. Da kuma maganganun Malamai, kamar maganar Imam Ahmad Bin Hanbal, da Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah, da Imam Ibnul Qayyim dukkansu suna nuna yiwuwar maganar mutum da aljani ta harshen mara lafiya.
Babban Malami Sheikh Abdul Aziz Bin Baz shugaban majalisar Malamai ta kasar Saudiyya a lokacin da yake raye ya ce cikin lattafinsa mai suna Iidhaahul Haqqi Fii Dkhuulil Jinniyyi Fil Insiyyi shafi na 6-7 ((Aljani ya cakuda da sashin Mata Musulmai a Riyadh, sai sashin Malamai ya karanta (Alkur’ani) domin fidda shi, ya kuma tunatar da Aljanin (girman) Allah, ya yi masa wa’azi, ya kuma ba shi labarin cewa zalunci haramun ne, kuma zunubi ne babba, ya kuma kira shi zuwa ga Musulunci ya musulunta. Daga nan sai suka zo gurina da matar, na tambaye shi (shi Aljanin) dalilin da ya sa ya shiga cikinta, ya ba ni labarin dalilan, ya yi magana da harshen matar amma maganar maganar na miji ne ba maganar mace ba. (Hakan ya faru ne) alhalin tana cikin wata kujera da ke kusa da ni, dan’uwanta, da ‘yar’uwarta, da wasu sashin Malamai suna shaidar hakan, suna jin maganar Aljanin a lokacin da yake tabbatar da musuluncinsa a fili, na yi masa nasiha, na yi masa wasiyyar takawar Allah, da kuma cewa ya fita daga wannan matar, ya nisanci zaluntarta, ya kuma karba mini hakan ya ce: Ni na gamsu da Musulunci. Na yi masa wasiyyar ya kira jama’arsa zuwa ga Musulunci. Ya bar matar da aka ambata, karshen kalmar da ya hurta ita ce: Assalaamu Alaikum, daga nan sai matar ta yi magana da irin harshenta da aka saba (ji), ta kuma ji lafiyar jikinta da samun hutu daga gajiyar da ya sanya mata. Daga nan sai ta sake dawowa gurina bayan wata ta kuma ba ni labarin cewa tana cikin alheri da lafiya)).
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya taimake mu. Ameen.

TARON SUNA GA MATA HALAL NE!!!|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

TARON SUNA GA MATA HALAL NE ! ! !
Tambaya?
Assalamu Alaikum, Malam don Allah menene hukuncin taron bikin suna a Musulunci ?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
A zahiri taron sunan da mata suke yi al'ada ne, tun da mata ba sa yinsa da nufin samun lada ko karawa abin da aka haifa albarka. Mata suna yinsa ne don taya juna farin ciki, da kuma nuna annashuwa saboda karuwar da aka samu, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amalolin mutane a bude yake, sai abin da sharia ta haramta.
Duk Wadda take taron suna ba tare da ta riya cewa ibada ba ce hana ta ko bidi'antar da taron yana da wuya, tun da ba mu da dalilin SHARIA da ya haramta.
Idan a cikin taron aka samu bidi'o'i ko kuma ayyukan da Allah ya haramta kamar fito da tsaraici, ko zancen da Allah ya hana, hakan zai iya zamar da shi haramun, saboda yana daga cikin sharudan lura da al'ada kar ta zama da sabawa nassoshin SHARIA, ko kuma ka'idojin da malaman musulunci suka cimma daidaito akan su, kamar yadda malaman Usul da na Kawa'idul Fiqhiyya suka ambata.
Allah ne mafi sani
7/11/2016
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

BREAKING Donald trump ya lashe zabe

Donald Trump, ya lashe zaben shugabacin kasar Amurka, abokiyar takarsa Hilary Clinton ta kira shi ta yi masa murnar lashe zaben da suka fafata.

Tuesday, 8 November 2016

BREAKING :Trump da Clinton na kan-kan-kan a muhimman jihohi

Donald Trump da Hillary Clinton na tafiya kan-kan-kan a muhimman jihohi da fafatawa ta yi zafi sosai.
Babu tabbas kan inda sakamakon zai kaya a jihohin da suka hada da Florida da kuma Virginia.
Tuni Mista Trump ya lashe kujerun jihar Ohio da gagarumin rinjaye.
Gidan talabijin na ABC News ya yi hasashen cewa Mista Trump ya yi nasara a jihohin Kudancin kasar, yayin da Hillary Clinton ta samu galaba a jihohin Arewa.
Har ila yau ana sa ran jam'iyyar Republican za ta rike rinjayen da ta ke da shi a majalisar wakilan kasar.
Ana bukatar dan takara ya samu kuri'u 270 daga cikin manyan kuri'u 538 (wato electoral college) domin samun nasara.
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta BBC ta nuna cewa Clinton na gaban Trump da maki hudu kacal.
Da sanyin safiya misalin karfe 06:00 ne aka fara kada kuri'a a Gabashin kasar, sai dai tuni wasu kauyuka a jihar New Hampshire sun riga sun kada kuri'unsu.
Duka Misis Clinton da Mista Trump sun kada kuri'unsu a mazabu daban-daban a birnin New York.
An samu dogayen layuka a wasu jihohin, abin da ke nuna yadda jama'a suka fito sosai.
Wasu wuraren kada kuri'ar sun samu matsalolin na'ura, abin da ya haifar da jinkiri.
Duka 'yan takarar sun yi gangamin yakin neman zabe a jihohin North Carolina da Pennsylvania da kuma Michigan, inda nan ne takarar ta fi zafi.
Sai dai tuni Amurkawa miliyan 46 suka jefa kuri'unsu a jihohin da suka bude rumfunan zabensu kwanakki gabanin wannan ranar ta zaben gama-gari.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan asalin Latin Amurka masu amfani da yaren Spaniya, wadanda ke goyon bayan Hillary Clinto, sun fito sosai.
Hillary Clinton da Donald Trump sun zagaye kasar domin neman kuri'un jama'a a 'yan kwanakin da suka gabata.