Kamar Yadda Muka Samu Sako Ta Hanyar Tun Tubarmu, Ga Wannan Bawan Allah Da Yayiwa Kungiyar “Kwankwasiya” Sabuwar Waka. inda Ya Baiyana Nashi Farin ciki Zuwa Ga Jama”ar “Kwankwasiya” Da Cewa Ga Wannan Tsarabar Waka Zuwa Ga “Dr Rabi”u Musa Kwankwaso” Da Kuma Jama’ar Sa Baki Daya.
Haka Kuma Mawakin Ya Kara Da Cewa insha Allah 2019 Muna Fatan ‘Baba Buhari ‘ Zai Tsaida Muna Kwankwaso A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa.
Ga Wakar Nan Ku Sauke Ta Akan Wayarku Ku Saurari Wannan Bawan Allah Yadda Yarera Baitin Waka Zuwa Jagaiya Kwankwasiya.
Wanna Ba Gaskiya Bane ‘Yan Uwa Duk A Cikin Film Ne, Yadda Suke Shiryar Da Film Kuma Idan Ka Duba Zakaga Jama’a Ke Kewaye Da Su.
Dan Allaj Jama’a Mu Daina Daukan Kita Jita Mutsaya Mufahimci Lamari Kamun Ka Aiwata.
Toh Jama’a Adade Anayi Sai Gaskiya Inji “Rahama Sadau ” A Cewarta Itafa Duk Masu Ce Ce Kuce Suyi Tayi, Muddin Ita Kan Gaskiyarta Take Wannan Sana”a Film Ba Wai Iskanci Takeyiba.
Haka Kuma Ta Kara Da Cewa ita Tanayin Nollywood Ne Don Sha’awa Ba Don Wani Abu Da Jama’a Ke Cece Kuce Akai Ba. Domin Idan Mutun Yace Ya Biye Jama’a To Hatta Kansa Bazai Mora Ba,
Wannan Shine Dan Gajeren Zance Daga Jarumar ‘Rahama Sadau’ Ku Dannah Kan Download Below Domin Sauke Video Zuwa Kan Wayoyin Ku.
Har yau bayan kwana goma da dawon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, masoya da magoya baya na cigaba da gudanar da gangami dama shirya walima a garin Bauchi domin nuna godiyan su ga Allah da ya dawo da Shugaba Buhari, gida lafiya daga birnin Landan.
A makon da ya gabata Shugaban matasan jam'iyan APC, na jihar Bauchi haka kuma jagoran masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a jihar Bauchi wato Alhaji Nasiru Umar Gwallaga ya jagoranci Mata da maza na garin Bauchi, inda suka gudanar da gagaruman gangamin da ya dauki hankalin Nijeriya.
Inda a wannan gangami ne jagoran wannan gangami ya soke rakumi aka yi sadaka da naman duk dai domun godiya ga Allah da ya bawa Shugaban kasa Buhari lafiya ya dawo gida lafiya.
Bayan wannan gangami na jagoran masoya Buhari, a Bauchi wasu matasa sun gudanar da walima da addu'oin murnan dawowar Buhari da samun lafiyar sa a garin Bauchi.
Yau kuma an shirya wani gagaruman taron murna da nuna goyon bayan 'yan Nijeriya da dawowar Shugaba Buhari.
A wannan babban gangami na yau ya samu halartar manyan mawakan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadanda suka hada da Dauda Adamu Kahutu Rarara, da wasu mawakan dama 'yan fim din Hausa da suka hada da Jamila Nagudu da Rabiu Daushe da dai sauransu.
Mawaka da 'yan fim din Hausa sama da mutum talatin ne suka samu halartar gangamin. Da 'Yan Fim Sun Gudanar Da Gangamin Murnar Dawowar Shugaba Buhari Yau A Bauchi
Daga Ahmadu Manaja Bauchi
Har yau bayan kwana goma da dawon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, masoya da magoya baya na cigaba da gudanar da gangami dama shirya walima a garin Bauchi domin nuna godiyan su ga Allah da ya dawo da Shugaba Buhari, gida lafiya daga birnin Landan.
A makon da ya gabata Shugaban matasan jam'iyan APC, na jihar Bauchi haka kuma jagoran masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a jihar Bauchi wato Alhaji Nasiru Umar Gwallaga ya jagoranci Mata da maza na garin Bauchi, inda suka gudanar da gagaruman gangamin da ya dauki hankalin Nijeriya.
Inda a wannan gangami ne jagoran wannan gangami ya soke rakumi aka yi sadaka da naman duk dai domun godiya ga Allah da ya bawa Shugaban kasa Buhari lafiya ya dawo gida lafiya.
Bayan wannan gangami na jagoran masoya Buhari, a Bauchi wasu matasa sun gudanar da walima da addu'oin murnan dawowar Buhari da samun lafiyar sa a garin Bauchi.
Yau kuma an shirya wani gagaruman taron murna da nuna goyon bayan 'yan Nijeriya da dawowar Shugaba Buhari.
A wannan babban gangami na yau ya samu halartar manyan mawakan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadanda suka hada da Dauda Adamu Kahutu Rarara, da wasu mawakan dama 'yan fim din Hausa da suka hada da Jamila Nagudu da Rabiu Daushe da dai sauransu.
Mawaka da 'yan fim din Hausa sama da mutum talatin ne suka samu halartar gangamin.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murna da nasarar da 'yan kwallon kwando mata na Nijeriya suka yi a wasannin kwallon kwandon da aka kammala kwanan nan.
Da safiyar yau ne 'yan matan suka gabatar da nasarar da suka samu ga shugaban kasan.
Shugaban kasar ya yi murna sosai bisa nasarar da kungiyar ta Dtigers suka samu kuma ya bada umarnin aba kowace daga cikin 'yan wasan naira miliyan daya.
Bidiyon wata mata ce da aka kama a unguwar Kinkinau Gangare kusa da Masalachin Musabaqa dake Kaduna, wadda ake zargin take shiga gidajen mutane idan ba kowa sai tasa makullai ta bude gida ta kwashe komai har. A yayin da dubun nata ya cika, an same ta da makullai kala-kala sama da 50.
A cikin bidiyon za a ga yadda wasu maza suka dinga lakada mata duka har ta kai ga sun kusan yi mata tsirara.
Masu karatu ko abinda aka yi wa wannan baiwar Allah ya dace?
Saukae da wanannan video Wanda Jarumin nan kuma mawaƙin Umar m sharif ya rera .shu kuma Adam a zango ya hau rawar Wanannan wani sabon salon album ne ya fitar wanda za ƙaro wulaƙanci a ciknsa abindae sai ka gani
Tun farko gwamnatin Najeriya bai kamata ta yi sakacin sakin tsagera irin Nnamdi Kanu ba. Domin Nnamdi Kanu ba shi da bambanci da tsohon shugaban Boko Haram, Muhammad Yusuf.
Haka su ma wadanda suka tsaya masa wajen karbar belin sa a kotu ya kamata a kamo su.
Illar Nnamdi Kanu ta fi muni fiye da na jagoran Boko Haram Muhammad Yusuf, kudirinsu iri daya ne, su tarwatsa kasa su mutu su bar al'umma da bala'i. Amma gwamnatin Nijeriya ta yi shiru ba ta cewa komai a game da shi har yana nunawa gwamnati yatsa, amma an kasa cewa uffan, ko saboda ba dan Arewa bane ya sa aka kyale shi?
Bayan ya ketare duk dokokin da aka gindaya masa daga kotu kafin a bayar da belin sa, suma wadanda suka tsaya masa su kansu an kyale su ko tuntubar su ba a yi, bayan an ba su sharudda suma.
Idan kuwa har za a iya kyale shi ya ci gaba da wannan abin, to lallai gwamnati ta saki jagoran mabiya Shi'a Sheik Ibrahim Zakzaky.
Jarumar nan ta masana’antar Kannywood wadda kan fito a matsayin uwa a fina-finai da dama watau Hadizan Saima ta bayyana dalilin ta da ya sa ya zuwa yanzu bata marmarin sake yin aure kwata-kwata a halin yanzu.
Jarumar wadda a halin yanzu tauraruwar take matukar haskawa a farfajiyar masana’antar ta bayyana cewa ita yanzu sai dai tayi wa mutane bayanin menene aure don kuwa shekarar ta sama da ashirin a gidan miji kafin auren nata ya mutu.
Dandalin Mujallarmu.com ta samu cewar jarumar ta bayyana cewa ita tana mamakin yadda mutane suke tayi mata tsegumi a kan wai ta sake yin aure inda ita kuma a ko da yaushe take shaida masu cewa ai ita ta fadawa wasu sanin aure da kuma muhimmancin sa don kuwa ta jima a cikin rigar sa.
A wani labarin kuma mai karatu zai iya tuna cewa mun kawo maku labarin cewa ita ma dai jarumar nan ta wasan Hausa watau Nafisa Abudullahi ta bayyana cewa ita kuma ba zata taba iya auren dan fim ba kuma yanzu haka ma ta kusa yin auren.
Gyara ga masu musun sallar juma'a ranar idi : 1. Sallolin juma'a da na idi duka sunnonine masu karfi ba wai farilloli bane. 2. Wanda yake ganin idan yayi idi to ba sai yayi juma'a ba to ya dinga fadawa mabiyansa cewar sai fa sunyi sallar azahar kuma! 3. Wanda yake ganin za'ai sallolin biyu duka a rana daya to ya dinga fadawa mutane falalar sallolin guda biyu. Abin bai kai ga rigima ba. Kowa yayi abinda ya fahimta a addini da ikhlasi. Ka dai tuna idan anje lahira ba malam wane ne zaizo gaban Allah yayi jawabi akanka ba, kai da kanka zaka fadi dalilanka a gaban Allah na yi ko kin yin abu a musulinci Sources:sadeeqmedia.com.ng
Fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan Hausa Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho ya ce tsundumar da ya yi cikin harkar fim ce ta hana shi zama farfesa. "Na samo sunan Bosho ne saboda lokacin da nake makarantar sakandare ina yawaita karatu. Na kan kwashe kwana 15 ban yi cikakken bacci ba saboda yawan karatu. "Shiga ta harkar fina-finai ce ta hana ni zama farfesa," in ji Bosho, a hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa. Dan wasan ya ce sha'awarsa wajen karatu ce ta sanya yake amfani da wasu kalmomi na boko a fina-finansa. "Za ka ji ina yawaita cewa 'A shekarar 1778 da na je Ingila sarauniya ta bukaci a dafa min shayi amma na ce tuwo nake so' ko kuma na cewa 'wane ne ubanka a Northern Nigeria', in ji Sulaiman Yahaya. Bosho, wanda ya kwashe fiye da shekara 30 yana fitowa a fina-finan Hausa, ya kara da cewa ya rungumi bangaren barkwanci ne saboda shi dama mutum ne mai yawan son raha. A cewar Bosho, "Na soma fim tun lokacin da ake wasan kwaikwayo na dandali; ni mutum ne mai son bunkasa al'adun Hausa da addinin Musulinci, shi ya sa na zabi zama dan wasan kwaiwayo. "Na dauki al'adarmu da matukar muhimmanci kuma na soma fim ne tun lokacin da ake yin wasannin kwaikwayo a Gidan Dan Hausa da ke birnin Kano. 'Yan wasa irin su Danhaki da Mallam Mamman su ne gwanayena". Dan wasan na Hausa ya nuna bakin cikinsa kan yadda masu shirya fina-finan Kannywood ba sa mayar da hankali wurin bunkasa al'adar Hausa, yana mai cewa, "hakan ne ya zubar da mutuncinmu a idanun masu kallo". Ya kara da cewa saboda irin mummunan kallon da ake yi wa 'yan fim ya bude kamfanin hada fim wanda zai mayar da hankali wurin tallata al'adun Hausa. Bosho ya ce akwai dangantaka mai kyau tsakaninsa da marigayi Rabilu Musa Dan Ibro. "Ibro ya kan taso daga garinsu Danlassan ya zo nan [cikin birnin Kano] mu sha hira; shi mutum ne mai kokarin zumunci. "Ni ma na kan je garinsu na sada zumunci kuma har yanzu ina ci gaba da zuwa mu gaisa da iyaye da iyalansa. Kafin ya rasu mu kan bai wa juna shawara kan al'amur an rayuwa. Allah ya jikansa", a cewar Sulaiman Yahaya. Sources bbchausa.com
Daga Haji Shehu Wani matashi a Maiduguri ya yi nasarar kera Keke mai amfani da inji. Kamar yadda kuka gani a hoton nan, matashin ya yi amfani da injin babur da kuma tankin janereto wajen cimma burin shi na ganin Keken shi ya yi gudu ba tare da ya taka feda ba. Wannan sabuwar fasaha da matashin ya kirkira, za ta yi matukar saukakawa a jihar Borno, kasancewar har yanzu suna cikin dokar hana zirga-zirga da babur. Keken zai dauke ka zuwa waje mai nisa cikin kankanin lokaci ba tare da ka shan wahalar tuki ba. Sources:Rariya
Jami'an kasar Libya sun sanar da cewa mutumin da suka kama a matsayin kwamandan kungiyar Da'esh, yana aiki ne da kungiyar leken asirin Haramtacciyar Kasar Isra'ila ne ta Mosad. Tashar telbijin din al-jadid ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa; limamin masallacin mai suna "Abu Hafs" an kama shi ne a garin Banighazi da ke gabacin kasar Libya. Binciken da aka gudanar akan shi ya tabbatar da cewa mutumin bayahude ne dan haramtacciyar kasar Isra'ila kuma sunanshi na gaskiya shi ne; Benyamin Afrahim. Jami'an gwamnatin kasar ta Libya sun tabbatar da cewa; Afraham yana a karkashin rundunar leken asiri da ake kira "Masu kama da larabawa' da ke karkashin Mosad, aikinsu kuwa shi ne yin leken asiri a cikin kasashen larabawa. Afraham ya shiga kungiyar Da'esh, har ta kai shi ga zama kwamanda da mayaka 200 a karkashinsa, kafin daga baya ya zama limamin masallaci a Banighazi. Rahotanni sun nuna cewa aga cikin manufofinsa shi ne bude yaki a cikin kasar Masar.
Jamaa baraknku da wannan lokaci a kwanakin baya munyu wani post akan yanda xaka more kiran minti 240 akan N200 kacal, to ayau ma cikin ikon Allah zamuyi bayani akan yanda zaka more minti 60 akan N50 kacal. kamar dai wancan xaka fara sanya code din a layinka don kaga ko layin nadaga cikin zababbun layikan daxasu iya more wannan gara basar, idan layinka xayyi bayan kasanya code din zakaga sunyi maka reply kamar haka:- sorry you didn’t have sufficient balance to perform this transaction to kanada damar more wannan gara basar maana layinka xai iya more wannan garabasar,to sai kasanya N50 a layinka kasake sa code din Idan kaga akasin haka to layinka bazayyi ba , Ga code din kamar haka *341*1# Sources:arewamobile.com
Iya dafa abinci kadai ba ya tabbatar da zamowar ki gwarzuwa a kitchen, dole sai kin iya wasu dabaru na yadda zaki biyo da matsaloli idan sun taso, yadda zaki gujewa almubazzaranci, yadda zaki hana kayan hadin ki lalacewa da wuri, yadda zaki rage bata lokaci wajan girki, da dai sauran su.
Sai dai yawancin wadannan dabaru su kan dauki shekaru kafin a gano su, wasu kuwa ma in har ba fada miki su aka yi ba baza ki taba gano su ba
Wannan ya sa Mujallar Al’ummata ta tattaro miki manyan dabarun nan guda 12 domin samun saukin ki :
Kayan Lambu: Karas, Kabeji, Koren wake da Ganyayyaki
1.Karas da kabeji suna da saurin yamushewa, sau da yawa sai dai mu zubar da su idan sun yi kwana biyu. Abin da baki sani ba shine, idan da zaki jika su a ruwa na dan awanni kafin kiyi girki, toh za su kara tauri su kame kamar yanzu kika sayo su, musamman ma karas. shi kabeji idan za ki masa haka sai kin yayyanka tukun.
2. Shi kuwa koren wake, idan kina so ki tabbatar da bai canja kala ba a cikin girki, to ki dan jika shi a ruwan kanwa na dan lokaci kadan kafin ki zuba shi a dahuwar ki.
3. Idan kina son ajiye koren ganye kamar alayyahu ba tare da ya lalace ba, to ki hura ledar da zaki ajiye shi da iska kafin ki daure
Kwai da bawon sa
4. Bare kwai da yawa a lokaci daya akwai bata lokaci, saboda haka zaki iya zuba su gaba daya a kwano ki girgiza da karfi, zasu fasa kansu amma fa ba zasu fito da kyau ba. Wannan kuwa a gani na ba matsala ba ne idan yayyankasu dama za kiyi, kamar wajen hadin salad.
5. Zaki ga wani lokacin idan kika fasa danyen kwai, bawon sai ya faffashe a ciki, kuma cire su ya kan bada matsala saboda tsantsin da kwan yake da shi. To abinda zakiyi a nan shine, ki dan karyi bawan kwan da kika fasa me dan tsini, sai kiyi amfani da shi.
Ko kuma ki saka ruwa a hannun ki kafin ki cire, wannan zai rage santsin kwan.
6. Idan kina da ajiyayyun kwai amma baza ki iya banbance tsakanin lalacacce da mai kyau ba, toh ki zuba su gaba daya a cikin ruwa. Za ki ga wanda ya lalace ya yo sama. Masu kyan kuma sun kwanta a kasa.
Leman bawo
7. Idan ba kya son acid din da ke cikin Lemo ya tsarto miki idan kin zo barewa, za ki iya dan gasa shi a cikin microwave ko kuma ki mulmulashi a kasa da kyau kafin ki bare
Dankalin turawa
8. Kowa ya san bare shi akwai cin rai da daukan lokaci. Toh idan amfanin da zaki yi dashi yana bukatar dafaffen dankali ne ba danye ba, kamar idan zaki yi potato salad, toh abin ya zo da sauki.
Zaki fara dafa dankalin, idan ya dahu sai ki zuba masa kankara na dan lokaci, zaki ga bawon ya bar jikin dankalin, sai ki kwashe shi kawai za kiyi.
Albasa
9. Idan ba kya son yajin albasa ya shiga idon ki a lokacin da kike yanka ta, toh zaki iya dan cizar bredi a bakin ki, barin sa daya yana waje yayin da kike yankan. Biredin zai shanye gas din da yake fitowa daga albasa kuma zai hana shi isa idon ki
Ko kuma zaki iya daskarar da albasar, sai ki yanka ta a daskare. Tunda gas din ya daskare ba zai tashi ya shiga ido ba. Matsalar wanna shine ba zaki iya barin albasar ta huce ba saboda zata koma lubulubu.
10. Ba kya son warin albasa ko tafarnuwa a hannunki? Zaki iya shafa Leman tsami ko kuma baking soda sannan ki wanke.
Miya ko abinci mai borowa
11. Idan zaki dafa abinci ko miyar da kika san tana da zuba idan ta tafaso, kuma ba kya san bude tukunyar ki ki bar ta a bude, toh zaki iya dora cokali ko ludayin katako a kan tukunyar kafin ki rufe. Tunda katako baya jin zafi, wannan zai hana ruwan taba murfin.
Tsadar Tumatir
12. Kasancewar tumatir yana da lokacinsa na araha da kuma lokacin da baya sayuwa, ga wani dan dabara da zaki iya yi domin ajiye danyen tumatir na lokaci mai tsaho.
Zaki sayi danyen tumatir dinki da yawa kamar Kwando daya, ki markada shi ki dafa. Sai ki tsane ruwan ki shanya shi a rana ya bushe karau, sai ki zuba shi a kwali ki ajiye.
Idan lokacin amfani ya zo zaki dauki daidai yanda kike so, ki dauraye shi da ruwan sanyi. Sai ki zuba ruwan zafi ki barshi ya narke. Za ki ganshi yayi kyau kamar a lokacin kika niko. Sai ki kara attaruhun ki, da albbasa ki ja miyar ki.
Da fatan wadannan yan dabaru zasu saukaka rayuwarki su kuma taimaka miki wajen kara inganta gidan ki.
Saukar da wanannan Trailer of Gwaska Return film Wanannan film dai kamar yadda kunka sani Gwaska dae anyi film kuma ya kawatar to wanannan Gwaska ya samu ƙarin shahararren jarumai kamar haka:
Adam A zango.
Bello muhammad bello (BMB).
Tijjani faraga.
Hasfat idris (barauniya).
Usheere.
Dai dai sauransu wanda company Prince zango nigeria ltd yayi.
Fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan Hausa Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho ya ce tsundumar da ya yi cikin harkar fim ce ta hana shi zama farfesa. "Na samo sunan Bosho ne saboda lokacin da nake makarantar sakandare ina yawaita karatu. Na kan kwashe kwana 40 ban yi cikakken bacci ba saboda yawan karatu. "Shiga ta harkar fina-finai ce ta hana ni zama farfesa," in ji Bosho, a hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa. Dan wasan ya ce sha'awarsa wajen karatu ce ta sanya yake amfani da wasu kalmomi na boko a fina-finansa. "Za ka ji ina yawaita cewa 'A shekarar 1778 da na je Ingila sarauniya ta bukaci a dafa min shayi amma na ce tuwo nake so' ko kuma na cewa 'wane ne ubanka a Northern Nigeria', in ji Sulaiman Yahaya. Bosho, wanda ya kwashe fiye da shekara 30 yana fitowa a fina-finan Hausa, ya kara da cewa ya rungumi bangaren barkwanci ne saboda shi dama mutum ne mai yawan son raha. A cewar Bosho, "Na soma fim tun lokacin da ake wasan kwaikwayo na dandali; ni mutum ne mai son bunkasa al'adun Hausa da addinin Musulinci, shi ya sa na zabi zama dan wasan kwaiwayo. "Na dauki al'adarmu da matukar muhimmanci kuma na soma fim ne tun lokacin da ake yin wasannin kwaikwayo a Gidan Dan Hausa da ke birnin Kano. 'Yan wasa irin su Danhaki da Mallam Mamman su ne gwanayena". Dan wasan na Hausa ya nuna bakin cikinsa kan yadda masu shirya fina-finan Kannywood ba sa mayar da hankali wurin bunkasa al'adar Hausa, yana mai cewa, "hakan ne ya zubar da mutuncinmu a idanun masu kallo". Ya kara da cewa saboda irin mummunan kallon da ake yi wa 'yan fim ya bude kamfanin hada fim wanda zai mayar da hankali wurin tallata al'adun Hausa. Bosho ya ce akwai dangantaka mai kyau tsakaninsa da marigayi Rabilu Musa Dan Ibro. "Ibro ya kan taso daga garinsu Danlassan ya zo nan [cikin birnin Kano] mu sha hira; shi mutum ne mai kokarin zumunci. "Ni ma na kan je garinsu na sada zumunci kuma har yanzu ina ci gaba da zuwa mu gaisa da iyaye da iyalansa. Kafin ya rasu mu kan bai wa juna shawara kan al'amuran rayuwa. Allah ya jikansa", a cewar Sulaiman Yahaya. Sources:bbchausa.com
Wanan Waka Yahaya Madawaki Ke Dauke Da Baitin Wakar “Barayin Najeriya” A Cikin Wannan Waka Zakuji Irin Handama Da Baba Kere Da Manyan Mayan Najriya Ke Tabkawa A Cikin Wannan Kasa Tamu Najeriya.
Kamar Yadda Mawakin Ya Shedamun Cewa Bai Fadin Komai Ba A Cikin Wannan Wakaba Domin A Kwai Manyan Manya Masu Cin Kudin Talakawa.
Wannan Waka Dai Yayi Mata Lakabi Da Barayin Najeria Dodon Su Buhari Ne Ku Dai Sauke Wakar Ku Saurara Kuji Irin Yadda Yake Kiran Wa’yan Na Barayin Najeriya.
Saukar da trailer video daga cikin sababbin ablum na adam a zango zai fitar inda jarumin ya ƙaro wulakanci a cikin video abindae sai kagani. Kada ka bari a baka labarina ka saukar da wanannan video. Download video Now
Dandazon magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis sun gudanar da addu'o'i na musamman ga shugaban kasan a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata cikin birnin Kano don nuna farin cikin su da dawowarsa daga jinya da kuma fatan Allah ya kara masa lafiya.
Daga bisani dandanzon jama'an karkashin jagorancin hadimin shugaba Buhari kan kafafun sadarwa, wato Sha'aban Sharada sun dunguma zuwa fadar gwamnatin Kano, inda gwamna Ganduje ya tarbe su.
Gwamnan ya nuna farin cikinsa game da yadda ya ga dandanzon magoyan bayan shugaban kasan, wanda a cewarsa hakan ya nuna cewa har yanzu al'ummar jihar Kano na tare da shugaba Buhari dari bisa dari
Kalli hotunan dandazon magoya bayan shugaba muhammad buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a wata yarjejeniyar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda za ta fadada yaki da cin hanci da gwamnatinsa take yi da tsaron kasa da kuma bunkasa tattalin arziki. Yarjejeniyar ta yi tanadin musayar mutanen da suka aikata manyan laifuka tsakanin Najeriya da Hadaddiyyar Daular Larabawa. Shugaban ya bayyana al'amarin da wani muhimmin ci gaba ga kasar wanda zai taimaka wajen bunkasar tattalin arziki da tsaro da yaki da cin hanci da ciki da wajen kasar. Sabuwar yarjejeniyar za ta taimaka wajen tasa keyar wadanda aka samu da laifin aikata cin hanci a kasashen biyu. Ya ce an jinkirta fara aiki da cikakkiyar yarjeniya ne saboda bangarorin biyu ba su kammala cimma matsaya ba. "Wannan yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma zai taimaka wa hukumomin kasashen wajen gurfanar da wadanda aka samu da aikata laifin cin hanci da rashawa," in ji Shugaba Buhari. Sauran batutuwan da shugaban ya zartar a ranar Alhamis har da wata yarjejeniya da ta shafi yankin Tafkin Chadi da Kamaru da Janhuriyar Tsakiyar Afirka da Libya da kuma Jamhuriyar Nijar.
IDAN KUNNE YA JI... Mun Fara Sanya Ido Kan Masu Rubuta Munanan Kalamai A Kafafun Sadarwa Akan Gwamnati Da Rundunar Sojoji, Cewar Rundunar Sojoji Ta Kasa Daga Aliyu Ahmad Yanzu dukkan wasu al'amura da 'yan Nijeriya za su dinga yi a kafafun sadarwa game da rubuta kalaman batanci walau akan gwamnati, rundunar tsaro ko wanda zai raba kan kasa, zai kasance rundunar tsaro ta kasa za ta dinga biyayansu. Daraktan yada labarai na rundunar tsaro na kasa, Mejo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan ga kafar yada labarai ta Channels TV, inda ya ce daukar matakin ya zama dole don ganin an magance matsalar rabuwar kai a kasar nan.
Shahararriyar jarumar nan ta wasannin fina finan Hausa wadda kuma yanzu haka ke a matsayin korarriya a masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau ta bayyana cewa ita yanzu bata da saurayi don kuwa duka-duka shekarar ta 23 a duniya.
Jarumar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da tayi da manema labarai a game da rayuwar ta a dandamalin Kannywood.
NAIJ.com ta samu a firar ta da ta jarumar ta kuma bayyana cewar ba za ta taba fidda tsiraicin ta ba duk kuwa da cewar yanzu ta rungumi sana'ar yin fina-finan kudancin kasar nan gadan-gadan.
Haka ma dai jarumar yan asalin garin Kaduna ta kuma dauki dogon lokaci tana sharhi da kuma nuna rashin jin dadin ta game da yadda tace al'ummar hausawa nayi wa harkar tasu mummunar fassara inda ta kara jaddada cewa shifa fim, fim ne ba wai da gaske bane.
Tun farko dai, jarumar ta godewa dukkan masoyan da suka fito kwarsu da kwarkwata domin taimaka mata.