Tundaga ranar da 'yan ta'addan Boko Haram sukayiwa tawagar 'yan sanda harin kwanton bauna akan hanyar Damboa, suka fitar da video Shekau ya fito yace ya kama matan 'yan sanda dasu kansu jami'an 'yan sandan, kuma yace ba zai kashe su ba ya maidasu bayi, sai muka fahimci cewa lallai wannan wata sabuwar dabarace aka fito dashi domin a nemi kudi daga hannun gwamnatin Nigeria sannan a sake sakin wasu kwamandojin Boko Haram da ake rike dasu
Wannan babbar alamace da ya nuna mana cewa an gama cin riba akan batun 'yan matan Chibok, yanzu sun karkato zuwa kan matan 'yan sanda da kuma watakila wasu matan da za'a sake kamawa nan gaba
Babban abinda zamu lura dashi a cikin wannan sabon video da suka fitar shine kamar yadda Deborah Philimon tayi bayanin irin karramawar da 'yan ta'addan Boko Haram suka musu bayan an kamasu, wannan ya nuna cewa su suka tsara mata domin tayi irin wannan maganar, musamman matar da tayi jawabi a karshe wacce tace ita malamar makarantace tace tana son gwamnati tayi musu kamar yadda akayiwa 'yan matan chibok
Amma wai shin dagaske wadannan matan 'yan sandane kamar yadda Boko Haram da matan suka tabbatar?
Domin daga bangaren gwamnati ko ince hukumomin tsaro bamuga tabbataccen bayani officially cewa an kama matan 'yan sanda ba tun daga lokacin da akayi harin har zuwa yanzu, sannan bamuga labarin jami'an 'yan sanda da Shekau yayi alwashin ya kama ba
Nayi iya bakin kokari wajen bincike da tuntuba daga force headquarters Abuja ko zan samu bayanin cewar wasu jami'an 'yan sanda sun bata a hukumance amma babu bayanin abu makamancin haka, kuma da ace abu makamancin haka ya faru hukumar 'yan sanda zata fitar da signal a watsa zuwa kowace command, har divisions da formations na fadin kasarnan kamar yadda yake a ka'idah, amma babu abu makamancin haka
Babu shakka wadannan mata dai suna hannun 'yan Boko Haram, koma matan waye ne suna hannunsu, shiryawa akayi da matan domin a nemi kudi dasu aka kwasosu zuwa wajen 'yan Boko Haram ko kuma dagaske matan 'yan sandan ne shi dai wannan sabon video sahihi ne, kuma ko shakka babu suna samun kyakkyawan kulawa saboda ansan za'aci riba dasu
Hasashen abinda zai faru nan gaba shine kungiyoyin sharri zasu fito su zafafa kira da matsin lamba wa gwamnati, karshenta kuma gwamnati zata cika musu burinsu koda a boye ne, babu shakka akan haka
Yaa Allah Ka fi kowa sanin wadanda suka maida al'amarin ta'addancin Boko Haram hanyar kasuwanci da neman kudi, Yaa Allah Ka tona musu asiri Ka watsa al'amarinsu
Daga:Datti Salafiyya
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment