MAI SABAWA IYAYE KA KUKA DA KANKA | SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA - NewsHausa NewsHausa: MAI SABAWA IYAYE KA KUKA DA KANKA | SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

Pages

LATEST POSTS

Monday 2 January 2017

MAI SABAWA IYAYE KA KUKA DA KANKA | SHEIKH AMINU IBRAHIM DAURAWA

MAI SABAWA IYAYE KA KUKA DA KANKA

Duk wanda yaga matsala tayi masa yawa ya bincika
alakarsa da iyayansa.
Duk wanda yaga baya samun Nasara a duk abinda
yasa gaba ya duba alaka da iyayansa .

Duk wanda baya jin dadin rayuwar sa, ya bincika
yadda yake zaune da iyayansa Duk wanda yaga makiya suna rinjaye a kansa, ya
tintibi zaman sa da Iyayansa.
Sabawa iyaye yana jawo dukkan matsala a rayuwa
1 Sa iyaye kuka, saboda bakin ciki
2 Yiwa iyaye tsawa, ko hantara ko tsaki ko gunguni
3 Kosawa da iyaye da gajiya da su ko tsanarsu
4 Daurewa iyaye fuska ko sha musu kunu
5 Yiwa iyaye kallon raini da hadarin kaji
6 Yiwa iyaye tsiwa, da daga murya akan su
7 Kushe iyaye, da daukar su gidadawa.
8 Kauda kai, idan iyaye suna magana .
9 Fifita mata akan iyaye
10 Fifita Abokai akan iyaye
11 Jawowa iyaye matsaloli da rigingimu
12 Gulmar iyaye
13 Zagin iyaye ko jawo musu zagi
14 Damun kiyaye da kade kade da wake wake
15 Rashin shawara da iyaye
16 Kauracewa iyaye
17 Tsagalgalewa iyaye da rashin kunya
18 Iyaye su dinka tsoran dan su
19 Kin amfani da sunan iyaye
20 Dukkan iyaye da gajiya da su
21 Fatan mutuwar su
22 Yi musu gori dan kayi wani abu.
23 Boyewa iyaye samu, ko wadata,
24 yiwa iyaye karya
25 Karyata iyaye
26 Yiwa iyaye sata,
27 YI musu gori
28 YI musu musu,
29 Rashin yi musu addua
30 Barin iyaye cikin kunci da wahala.
Allah kasa mu gama da iyayanmu lafiya, kayi musu
rahma kamar yadda suka yi mana tarbiyya tun muna
Yara.
Dangirman Allah katurawa group 3 shiyakenuni daka
sanarda wani abunda yan uwa abunda kasania


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment