Assalamu alaikum warahamatullah mallam,wai gaskia ne mace mai haila (period) zata iya rike Alqur'ani izu goma?
Amsa
wa'alaikum assalam,
Abin da yafi zama dai dai shi ne: kar mai haila ta taba ko da wani bangare ne a Alqur'ani saboda hadisin Amru Bn Hazm, wanda wasu malaman hadisin suka inganta ,inda Annabi s.a.w yake cewa: (kar wanda ya taba Al'qur'ani sai mai tsarki),kamar Albani a sahihi dha'ifil jam'i hadisi mai lamba ta 13738.
Amma ya halatta ta karanta ta hanyar kallo, saboda hadisan da suka hana mai haila karatun Al'qur'ani ba su inganta ba
Allah ne mafi sani
4/01/2017
Dr jamilu yusuf zarewa
posted by Abubakar Rabiu Yari
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment