FITOWA TA BAKWAI (7)
Ya halatta a salwantar da wani bangare na dukiya domin a kubutar da sauran dukiyar daga salwanta,
kamar yadda ya halatta a yi hakuri da wata karamar barna domin a magance babbar barna.
Dubi yadda Khadir (A.S) ya lalata wani sashi na jirgin ruwan miskina nan domin ya kubutar da ilahirin jirgin ruwan daga fadawa hannun azzalumin sarki.
Ya aikata karamar barna (huda jirgi) domin magance babbar barna (kwace jirgi).
Allah ya hakaito mana maganar Khadir (A.S) yana cewa, “Amma dangane da wannan jirgin ruwan, ya kasance na wasu miskinai ne suna aiki da shi a cikin teku, sai na yi niyyar lalata shi, kuma a gabansu akwai wani sarki yana kwace duk wani jirgi (lafiyayye)”. [Al-Kahfi, 79].
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment