HUKUNCIN WASAN KWALLON KAFA ! !
Tambaya:Malam ina tambaya ne akan kwallon qafa, a kwai wanda yake neman aurena sana'arsa kenan, da ita yake ci yake sha yake komai, so malam ina kokonto akan wannar sana'ar tasa, kada ya kasance sai anyi auren inji cewa ba halal bane, tunda ana biyansa idan sukayi wasa, to shine malam ko a taqaice a sanar dani wani abu akai, saboda musan makamar mu, nagode•
Amsa:
To 'yar'uwa ına rokon Allah ya baki miji nagari, malamai suna kasa kwallo gıda uku :
1.Kwallon da ake yi saboda motsa jiki, kamar mutum biyu su hadu, su yi ball don su tsinka jinin jikinsu, wannan kam ta hallata mutukar ba ta kautar daga ambaton Allah ba, ko kuma sallah idan lokacinta ya shiga .
2. Kwallon da kungiyoyi biyu ko sama da haka za su hada kudi su sayı kofi wanda a karshe kungiya daya za ta dauka, wannan kam bai halatta ba, saboda daidai yake da CACA, kuma yana sabbaba gaba da kiyayya a tsakanin 'yan kwallo.
3. Idan ya zama wani ne daban zai sanya Kofin, shi ma malamai sun ce haramun ne saboda asali musabaka da wasan tsere haramun ne, in ba abin da dalili na shari'a ya halatta ba, irin wannan kwallon kuma ba ta cikin abin da aka togace, sannan akwai barna mai yawa a cikinta, domin zai yi wuya a tashi irin wannan Kwallon wani bai ji ciwo ko ya karye ba, ga kuma haushi da kulewa da yake samun wanda aka kayar, wasu lokutan har da doke-doke tsakanin kungiyoyin guda biyu.
Idan ya zama mijin da za ki aura yana yın nau'i na na biyu ko na uku, to ya wajaba ki yi masa nasiha idan kuma yaki ji, to auransa akwai hadari saboda zai ciyar dake da haramun.
Don neman karin bayani duba Fataawaa Al-lajna Adda'imah 3/238 da kuma Fataawaa Muhammad bn Ibrahim 8/116. Allah ne mafi Sani.
Dr. Jamilu Zarewa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment