SANATA ALI NDUME YA FARA TONE-TONE.!!! - NewsHausa NewsHausa: SANATA ALI NDUME YA FARA TONE-TONE.!!!

Pages

LATEST POSTS

Thursday 26 January 2017

SANATA ALI NDUME YA FARA TONE-TONE.!!!

SANATA ALI NDUME YA FARA TONE-TONE.


An dade ana nuku nuku, anki a bayyana wa  Al'ummar kasar nan gundarin abunda Sanatoci suke kasaftawa, kuma manya suna sane sunyi shiru.

Jaridar premium times Hausa tace Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai, Sanata Ali Ndume yace yanzu lokaci yayi da majalisar za ta bayyana ma Sanatoci da mutanen Najeriya abinda ake kasafta wa majalisar a kasafin kasa.

Ndume ya kara da cewa hatta su yan majalisan basu san nawa ne majalisar ta ke samu ko kuma ta ke kashewa.

Yace bayan kudin adunkule da ake ware wa majalisar wanda ya kai naira biliyan 115 babu wanda ya san yadda ake kasafta shi.

Shugaban Majalisar dattijai da kakakin Majalisar Wakilai ne kawai suka san yadda suke kasafta kudin.

Ndume yace babu abinda zai sa ace dole sai hakan za’aci gaba da yi.

Ya kara da cewa dole ne kuma fannin zartaswa ta bada bayanai akan kasafin kudin bana saboda su san abin da za’ayi dasu da inda za’a kashesu.

Yace naira biliyan 40 da aka ware ma yankin Arewa maso gabas yayi kadan.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment