Fatawar Rabon Gado (95) Dr jamilu Yusuf Zarewa - NewsHausa NewsHausa: Fatawar Rabon Gado (95) Dr jamilu Yusuf Zarewa

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 31 January 2017

Fatawar Rabon Gado (95) Dr jamilu Yusuf Zarewa

Fatawar Rabon Gado (95)

Tambaya

Assalamu alaikum warahahamtullahi wabara katihu mutum ne ya mutu ya bar mata da yara 3, mata 2, namiji 1, sannan kuma mahaifi  da mahaifiyar shi duk suna raye da wasu daga cikin yayyin shi.
Don Allah ya za'a raba gadon wannan mutum.

                 Amsa

wa'alaikum assalam to dan'uwa,za'a raba dukiyar da ya bari kashi ashirin da hudu ,a bawa matar kashi ukku na dukiya(Thumun), mahaifinsa a bashi kashi hudu (sudus),mahaifiyarsa a bata kashi hudu (sudus), yaran kuma a basu ragowar goma sha ukku duk namiji ya dau kaso mata biyu.

Allah ne mafi sani

              Amsawa

DR JAMILU YUSUF ZAREWA

28/01/2017


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment