Farfadowa Daga Kariyar Tattalin Arziki: Dole Sai Talaka Ya Shaida - Buhari - NewsHausa NewsHausa: Farfadowa Daga Kariyar Tattalin Arziki: Dole Sai Talaka Ya Shaida - Buhari

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 6 September 2017

Farfadowa Daga Kariyar Tattalin Arziki: Dole Sai Talaka Ya Shaida - Buhari



Majalisar Dattawa Ta Yi Maraba Da Wannan Mafita

Dole A Yi Takatsantsa - Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tattalin Arziki


Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa Farfadowa daga kariyar tattalin arziki da Nijeriya ta yi zai yi tasiri ne kadai idan talakawa sun shaida ta hanyar samun saukin rayuwar yau da kullum.

Shugaban ya yi wannan ikirarin ne a garin Daura inda ya nuna Jin dadinsa ga wannan sabon rahoto yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta yi guiwa kasa na ci gaba da kokarin ganin talakawan kasar nan sun samu saukin rayuwa daga Tsadar kayayyakin bukatun yau da kullum.

Haka ma, majalisar Dattawa ta nuna Jin dadi ga rahoton Farfadowar tattalin arzikin Nijeriya inda majalisar ta yi nuni da cewa matakan da gwamanti ke dauka kan farfado da tattalin arziki sun fara yin tasiri sai dai majalisar ta nuna cewa a yanzu za ta hada hannu da gwamnati wajen samar da ayyukan yi da kuma ganin an rage radadin talauci da ya addabi mafi yawan al'ummar kasar nan.

Sai dai a nasa bangaren, Mai Ba Shugaban Kasa Shawarwari kan Harkokin tattalin Arziki, Adeyemi Dipeola ya nuna cewa dole a yi takatsantsa saboda har yanzu tattalin arzikin Nijeriya na tangal tangal duk da rahoton cewa ya farfado daga kariyar da ya yi inda ya nuna bukatar ci gaba da aiwatar da manufofin da suka taimaka wajen kaiwa ga wannan nasara.

A yau Talata ne dai, Hukumar Kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta fitar da wani rahoto wanda ya nuna cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta fada. Rahoton ya ce tattalin arzikin ya bunkasa da kashi 0.55 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekarar 2017 idan aka kwatanta da rubu'i na biyu na shekarar 2016.
Hakan yana nufin cewa girman wannan bunkasa da aka samu ya haura wanda aka samu a rubu'i na biyu na shekarar 2016 da kashi 2.04 cikin 100.
Tattalin arzikin kasar ya samu wannan tagomashi ne bayan da ya kwashe rubu'i biyar yana ci gaba da tsukewa.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment