......Kazalika Shugaban Izalar yayi ƙira ga Al'ummar musulmi su saka 'an yankin Rohingya dake kasar Myanmar cikin muhimman addu'oin kariyar Allah a duk inda suke.
Daga: Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban Ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah wa iƙamatis-Sunnah ta tarayyar Nijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi ƙira da babbar murya akan gwamnatin tarayya ta ɗauki mataki na daƙile ƙisan gilla da Inyamurai ƴan a waren Ƙasar Biyafara suke yiwa Hausawa a garin Aba da wasu garuruwan inyamurai a kudu maso yammacin Naijeriya.
Shugaban yace zura ido ƴan ta'addan suna ɗauƙar doka a hannunsu bazai haifar da ɗa mai ido ba, lura da yadda Ƴan Ƙabilar Hausawa a jos suka fara ɗaukan doka akan wasu inyamurai waɗanda basuji ba basu gani ba a garin jos.
Sheikh Lau yayi ƙira da a tura jami'an tsaro su daƙile wannan ta'addancin da ƴan awaren suke yiwa Hausawa, kuma su zaƙulo waɗanda suka kitsa wannan rikici domin a hukunta su kamar yadda dokar ƙasa ta tanada, domin babu wanda yafi ƙarfin gwamnati" Inji Sheikh Bala Lau".
Shehin Malamin yayi ƙira ga matasan Arewa da suyi haƙuri kada su ɗauki doka a hannun su, saboda tabbacin cewa wannan gwamnati mai adalci bara ta zurawa ƴan ta'adda ido suna abun da suka ga dama a ƙasa ba.
A Ƙarshe Sheikh Bala Lau ƴa ƙira ga Limaman juma'a da Malamai masu karantarwa a masallatai da sauran Ɗaiɗaikun Jama'a da su sanya ƴan uwa Musulman yankin Rohingya na kasar Myanmar Cikin addu'oi na musamman, Kan kisan ƙare dangi daga maguzawa masu bin addinin Buddha suke musu.
A yanzu haka dai akwai ‘yan gudun hijira kimanin 400,000 da ke rakube a Bangladesh.
Sheik Lau yayi addu'ar Allah ya zaunar da Al'ummar musulmi lafiya a duk inda suke a faɗin Duniya, ya zaunar ƙasar mu lafiya, ya mana maganin waɗanda suke neman wargajewar ƙasar Amin.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment