Buhari Ya Roki Gwamnoni Su Biya Albashi Da Fansho Na Ma'aikatansu - NewsHausa NewsHausa: Buhari Ya Roki Gwamnoni Su Biya Albashi Da Fansho Na Ma'aikatansu

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 12 September 2017

Buhari Ya Roki Gwamnoni Su Biya Albashi Da Fansho Na Ma'aikatansu


Shugaba Muhammad Buhari ya roki gwamnonin jihohin kasar nan kan su biya basussukan albashi na ma'aikata da kuma Fansho na wadanda suka yi ritaya inda ya koka kan yadda wasu gwamnoni suka sarrafa kudaden tallafi na Paris Club da aka ba su.

Shugaban ya yi wannan rokon ne a lokacin da ya karbi bakuncin majalisar sarakunan Arewa inda ya nuna cewa a kullum yana kwana ne da tunanin halin da kasar ne ke ciki musamman ma talaka don haka dole ne gwamnonin su rage masa wasu nauyin.

®Rariya

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment