[Boko Haram] An Kama Wasu ‘Yan Boko Haram A Kano - NewsHausa NewsHausa: [Boko Haram] An Kama Wasu ‘Yan Boko Haram A Kano

Pages

LATEST POSTS

Monday 4 September 2017

[Boko Haram] An Kama Wasu ‘Yan Boko Haram A Kano

A jiya Lahadi ne jami’an tsaro a jahar Kano suka cafke wasu mayakan Boko Haram.




                Image © Alummata
Wannan ya na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnati Kano ta fitar ta hannun mai magana da yawun gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Tanko Yakasai.

Yakasai ya ce tuni aka aika mayakan zuwa Abuja inda za a ci gaba da yin bincike akan su.

Ya ce jami’an tsaron sun kwace makamai da dama da alburusai a wajen mayakan, kuma suna bada hadin kai wajen bada bayanai da za su taimakawa jami’an tsaron.

Ya kara da cewa kamen ya yiwu ne a sakamakon bayana sirri da mutanen gari ke samarwa jami’an tsaro
A don haka ne ya yi kira da jama’a da su kara mayarda hankali ta na su bangaren a yunkurin da suke da tabbatar da tsaro.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment