December 2017 - NewsHausa NewsHausa: December 2017

Pages

LATEST POSTS

Sunday, 31 December 2017

Video Fim : Ciki Da Raino 3 & 4 Sabon Shirin Hausa Fim 2018

Wannan shine cigaban shirin Wato Ciki Da raino  3& 4 wanda ya samu shahararun jarumai kamar haka :

Adam  A Zango

Suleman bosho

Hadiza Gabon

Umma shehu

Falalu Dorayi

Tijjani assase .

Da dai sauransu.

Domin downloading sai ku latsa link na kasa.


Download video here


Video fim: Ciki Da Raino 1& 2 Sabon Shirin Hausa Fim 2018

Albishirin ku ma'abota ziyarta wannan shafi a a yau munzo  muku da wannan fim wanda nasan zakuyi maraba da shi to Alhamdulillahi yau ga shi nan sai ku kalla domin dariya. 

Wannnan fim ba wane fim bane illa "CIKI DA RAINO" hausaloaded a ko yaushe suna faranta muku da labarai da wakoki da fina finai na musamman.

Domin downloading  kuma sai ku latsa wannnan link na kasa. 


Wannan Style Duk A Kannywood Fati Washa Itace ta Farko Da wannan Style

Wannan sabon style ne na hotu wanda jaruma fati washa na buga amma duba ka gani.

Wakokin fina-finan Hausa 5 da Suka Fi Shahara A Shekarar 2017

Wakokin fina-finan Hausa 5 da Suka Fi Shahara A Shekarar 2017
Hakika wakoki na daga cikin al'adar malam bahaushe inda tun asali aka same shi da su.
Sai dai wakokin a wannan zamanin sun canza sabon salo inda mutane suka zamanatar da su ta hanyar yin su da kayan kade-kaden zamani.

Haka zalika ma a bangare guda za ku samu cewa fina-finan Hausa ma da ake yi sukan saka wakokin hausa a cikin su domin nishadantar da masu kallo da kuma sauraro.

Arewafresh.com ta samu daga BBC Hausa inda ta zakulo wakokin Hausa guda 5 da jama'a su ka fi saurare a wannan shekarar ta 2017, daga cikin dimbin wakoki na mawaka daban-daban. Wakokin sun shafi jigon soyayya ne da kuma siyasa da biki.

Wakokin sun shafi jigon soyayya ne da kuma siyasa da biki.

1. UMAR M. SHARIFF (tare da Murja Baba) - " Jirgin So" (daga fim din 'Mansoor') Wakar "Jirgin So" fito ne a fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu.

Fitaccen mawaki Umar M. Shariff ne ya rera ta, tare da fitacciyar zabiya Murja Baba. Haka kuma 'Mansoor' shi ne fim na farko da Umar ya fito a ciki a matsayin dan wasa.

Hasali ma dai shi ne jarumin fim din, inda ya fito tare da sabuwar 'yar wasa Maryam Yahya a matsayin jarumar shirin.

An yi ittafaki da cewa babu wata wakar soyayya da ta yi fice kamar ta a bana. An yada ta sosai a kafofin sada zumunta na zamani a yunkurin tallata fim din.

Hakan ya sa lokacin da fim din ya fito, matasa sun yi caa zuwa gidajen sinima domin su kalli yadda aka yi rawar wakar.

2. SADIQ ZAZZABI (tare da Maryam Fantimoti) - "Maza Bayan Ka" Jigon wakar "Maza Bayan Ka" ta Sadiq Zazzabi dai shi ne zambo, ba kambawa ba kamar yadda wasu ke zato.

Duk da yake mawakin bai ambaci wanda ya ke yi wa zambon ba, masu lura da siyasar jihar Kano sun san takaddamar da ake yi tsakanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da masu adawa da shi, musamman a jihar inda ya yi gwamna kafin zuwan sa Majalisar Tarayya.

Wakar na kunshe ne da kalamai na muzanta babban abokin adawar Kwankwaso.

Wani al'amari da ya sa wakar ta kara yin fice shi ne kama Sadiq Zazzabi tare da gurfanar da shi a gaban kotu da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta yi a bisa zargin ya saki wakar kafin hukumar ta ba shi takardar izinin fitar da ita.

3. ABDUL D. ONE (tare da Khairat Abdullah) - "Abin Da Ke Cikin Rai Na" (daga fim ]in 'Mansoor') Wannan wakar ita ce 'yar'uwar wakar "Jirgin So" ta Umar M. Shariff; dukkan su sun fito a fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu. Wakar soyayya ce.

Abdul D. One, daya daga cikin yaran Umar M. Shariff, shi ne ya rera ta tare da mawakiya Khairat Abdullah. Wannan waka dai ta fito daga Kaduna, akasin yawancin wakokin zamani da ke fitowa daga Kano.

Abin da ya kara daga wakar shi ne kasancewar ta cikin fim din Ali Nuhu mai suna 'Mansoor' wanda ya na daga cikin manyan finafinan shekarar 2017.

Wannan fim ya sha talla a shafukan sada zumunta, da yake Ali Nuhu, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Kannywood, shi ne ya shirya fim din kuma ya ba da umarni, sannan jarumin shirin, wato Umar M.

Shariff, mawaki ne mai dimbin masoya, wadanda ke so su ga yadda ya yi a fim din.

4. DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA) - "Buhari Ya Dawo" Fitaccen mawakin siyasa Dauda Adamu Kahutu, wanda ake yi wa lakabi da Rarara, ya fitar da wannan wakar ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga London, inda ya shafe watanni yana jinya.

Sanin kowa ne an yi ta shaci-fadi kan rashin lafiyar, saboda haka 'yan Nijeriya da dama sun zaku su ga dawowar sa.

Don haka sakin wakar a daidai lokacin na da wuya sai ta karbu a wajen masu saurare.

Rarara ya yi waar ne a matsayin martani ga masu adawa da Buhari, musamman masu cewa rashin lafiyar zai hana shi ci gaba da mulki. Da ma can Rarara magoyin bayan Shugaba Buhari ne.

5. UMAR M. SHARIFF (tare da Khairat Abdullah) - "Rariya" (daga fimdin 'Rariya') Umar M. Shariff ya ci gaba da rike kambin sa na kasancewa daya daga cikin manyan mawakan wannan zamanin da wakar "Rariya" wadda ta fito a cikin fim din 'Rariya'.

Shi da Khairat Abdullah suka rera wakar. Jigon wakar shi ne soyayya tsakanin saurayi da budurwa. A cewar saurayin, ya yi tankade da rairaya na soyayya da rariya ne, a karshe ya yi dacen samun budurwar tasa a matsayin "tsabar" da wannan tankaden ya samar.

Ya ce: "Tankade na yo na sa rariya, Ke ce ki ka zam tsaba, Zabi na a soyayya." Ita ma ta mayar masa da wadannan kalmomin, tare da nuna masa cewa za ta yi masa sakayya da ba shi zuciyar ta.

 Kalmomin soyayya da ake furtawa a wakar sun taba zukatan matasa matuka.

A cuci maza: Kalli yanda kwalliyar zamani ke karawa mata kyau




Irin yanda kwalliyar zamani ke canja kamannin mata kenan, irin wannan shine ainihin a cuci maza.

Video : Kalli Bidiyon Yan Shi'a suna rera waka a coci lokacin kirsimati

Lallai yan shi'a sun nunawa duniya cewa su musulmuƙa ne saboda taya zaka raira waka a lokacin bukin sallar addinin da baka so a duniya ko baka tare da su. Waka ta nuna so da kauna ga mutum yana nuna kana sonsa dari bisa dari. 

Saboda daman a lokacin da shugabansu zazakky ya sha ruwan harsashe, shuganan can yaje na jajanta mishi da jama'arsa sai yake cewa daman su da su dan jumma ne da dan jummai to gashi abun ya fito a fili. 

Sai ku saukar da wannan video domin kallon suna rera wannam wakar a cikin coci ranar kirsimati. 


Download video here

Siffofi Goma Na Matar Da Ba'a Mantawa Da ita A Rayuwa Har Abada -Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa



1, MATAR DA TA YARDA ITA MACE CE, DON HAKA TA TANADI DUK ABINDA AKE BUKATA A WAJAN MACE.

2, MACE MAI HIKMA, DA AZANCI, WACCE TA KARANTA MIJINTA DA KYAU, KUMA TAKE  KAUCEWA DUK ABINDA ZAI KAWO KARO TSAKANIN SU, 

3, MACE MAI TAUSHIN HALI, DA NUTSUWA, WACCE MIJI YAKE JIN NUTSUWA, IDAN YANA TARE DA ITA. 

4, MACE DA KUDI BAI DAMETABA, ITA MIJINTA KAWAI TAKE SO, KO DA AKWAI, KO BABU. 

5,   MACE MAI HAKURI DA JURIYA, BABU GUNAGUNI, BABU MITA, DA KAI KARA GA IYAYE KO KAWAYE. 

6,  MACEN DA TA DAUKI KANTA LIKITA, MIJINTA MARA LAFIYA, DOMIN YA SAMI KULAWA, TA MUSAMMAN, DA RIRITAWA.

7, MACE MAI SAURIN DAUKAN ISHARA, TANA GANE, SHIRU, DA MAGANA, DA MOTSI, DA YANA YIN SHIGOWA DA FITA, DA SAMU DA RASHI, DA YANA YIN DA AKE CIKI A DUNIYA KO A GARI. 

8, MACE MAI SAKAKKIYAR ZUCIYA, MARA KULLI DA RAMUWA, 

9, MACE MAI KARAWA MIJI KUZARI, DA KARFIN HALI,  AKAN MANUFAR SA, 

10 MACE MAI RIKON AMANAR AURE, DA SOYAYYA GA MIJIN TA KAWAI.

WANNAN MATAR TANA DA WAHALAR SAMU, IDAN KA SAMU IRANTA, KADA KA KUSKURA KU RABU. 

YA HALATTA KA AURI MACE FIYE DA DAYA, AMMA KA SANI, MACE DAYA CE KAWAI, TAKE YI MAKA TASIRI A RAYUWA, WACCE RANKA KULLUM YANA KANTA, SAI DAI WACECE WANNAN DAYAR? WANNAN SHINE ABINDA KO WACCE TAKE FATA TA ZAMA, SAI DAI MUYI ADALCI KUMA MU BOYE SABODA GUDUN RIGIMA.

Miji Mai Wahalar Samu Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa



Wani lokaci, Zaku dade da mace tsawon shekaru, amma dakun rabu zata manta da kai, wani lokacin kuma zaku zauna Dan lokaci da mace, amma sai ta rike ka azuci, har karshen rayuwa ta.
Mai yake faruwa?

Ga wasu siffofi da muke gani, sakamakon yau da gobe, suna yiwa mata tasiri idan mutumin da suka hadu dashi. Yana da su. :

1 Namiji wanda yasan kimar mace, da darajar ta,

2 Namiji da yake yabon mace da riritata da daukan ta da  MAHIMMANCI.

3 Namiji mai rikon amana wanda baya juyawa matar sa, baya, komai tsawon shekarun da suka dauka, da kowacce larura ta gamu da ita.

4,  Namiji da yake bawa mace cikakken lokaci, domin sauraronta da Jin raayinta.

5 Namiji mai kyauta.

6 Namijin da yake bawa mace hakuri kuma ya lallashe ta idan ya bata mata rai,ko ta shiga wata damuwa.

7 Namijin da ya tsaratar da mace daga wani Hadari da ta fuskanta a rayuwa.

8  Namijin da mace tasan zai iya mutuwa saboda ita.

9  Namiji mai faraa da murmushi da sakin fuska, da tafiye-tafiye da mace.


10 Namiji Mai tsafta da kwalliya, da  Lafiyar jiki musamman wajan biyar bukatar iyali.

Hadarin Butulci A Musulunci Daga sheikh Jabir sani maihula


Idan Allah ya hada ka da abokin zama, makwabci ne a unguwa ko wurin aiki, ko aboki ko abokin kasuwanci ko miji ko mata ko 'ya'ya  ko mahaifa, ko wani abu makamancin hakan, kamata yayi idan yayi ma ba daidai ba ka tuna alkhairan sa sai su mantar da kai sharrin sa. Babu wani abokin zama face yanada alkhairi da sharri. Idan aka tafiyar da zafin sharrin sa da sanyin alkhairin sa sai a samu Rayuwa Maidadi.

Babban Butulu shine wanda ya manta alkairan Allah na halittarsa da Allah yayi da bashi rayuwa da addini mai kyau da nunfashi da gani da ji da magana da sauran ni'iomin da basu kirguwa, amma kullun sai fadin sharri yake: akwai zafin rana, ba abinci, ba lafiya, ba ba ba....
Allah yana cewa, " [Ka ambaci lokacin] da Ubangijin ka yayi sanarwa: idan kuka gode zan kara muku, idan kuka butulce kuma lallai azaba ta mai tsanani ce."
Allah ya bamu ikon yafewa junan mu da godema ni'iomin sa.

Saturday, 30 December 2017

Wakoki Da Sunka Samu Karbuwa Da Shahara a wannan shekarar 2017 (karanta)



Daga IBRAHIM SHEME

Allah mai zamani; a bana ma ba a samu wasu wakokin gargajiya na Hausa da su ka yi fice kamar na zamani da ake bugawa da fiyano ba.
Masu son Mamman Shata da Musa Dankwairo da sauran mawakanmu na gargajiya sun ci gaba da sauraren mawakan saboda sabo da kuma rike al'ada, to amma wakokin da aka fi saye ko aka fi saurare a kafafen yada bayanai da su ka hada da rediyo, talbijin da soshiyal midiya su ne wakokin da matasa ke yi da kayan kida na zamani.
Bayan tsananta bincike, mun zakulo wakokin Hausa guda 10 da jama'a su ka fi saurare a wannan shekarar ta 2010, daga cikin dimbin wakoki na mawaka daban-daban.
Wakokin sun shafi jigon soyayya ne da kuma siyasa da biki.
1. UMAR M. SHARIFF (tare da Murja Baba) - "Jirgin So" (daga fim din 'Mansoor')

Wakar "Jirgin So" fito ne a fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu. Fitaccen mawaki Umar M. Shariff ne ya rera ta, tare da fitacciyar zabiya Murja Baba.
Haka kuma 'Mansoor' shi ne fim na farko da Umar ya fito a ciki a matsayin dan wasa. Hasali ma dai shi ne jarumin fim din, inda ya fito tare da sabuwar 'yar wasa Maryam Yahya a matsayin jarumar shirin.
Wakar 'Mansoor' ta yadu ne a dalilin ficen Ali Nuhu a industiri din fina-finan Hausa, da kuma kasancewar Umar M. Shariff daya daga cikin mawakan da su ka fi yin tashe a wannan lokaci.
"Jirgin So" wakar soyayya ce tsakanin saurayi da budurwa. A cikinta, gwanayen mawakan (Umar M. Shariff da Murja Baba) sun nuna kwarewa wajen karya murya da kuma zuba kalmomi na shauki.
An yi ittafaki da cewa babu wata wakar soyayya da ta yi fice kamar ta a bana. An yada ta sosai a kafofin sada zumunta na zamani a yunkurin tallata fim din. Hakan ya sa lokacin da fim din ya fito, matasa sun yi caa zuwa gidajen sinima domin su kalli yadda aka yi rawar wakar.


2. SADIQ ZAZZABI (tare da Maryam Fantimoti) - "Maza Bayan Ka"
Jigon wakar "Maza Bayan Ka" ta Sadiq Zazzabi dai shi ne zambo, ba kambawa ba kamar yadda wasu ke zato.
Duk da yake mawakin bai ambaci wanda ya ke yi wa zambon ba, masu lura da siyasar jihar Kano sun san takaddamar da ake yi tsakanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da masu adawa da shi, musamman a jihar inda ya yi gwamna kafin zuwan sa Majalisar Tarayya.
Wakar na kunshe ne da kalamai na muzanta babban abokin adawar Kwankwaso.
Wani al'amari da ya sa wakar ta kara yin fice shi ne kama Sadiq Zazzabi tare da gurfanar da shi a gaban kotu da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta yi a bisa zargin ya saki wakar kafin hukumar ta ba shi takardar izinin fitar da ita.

3. ABDUL D. ONE (tare da Khairat Abdullah) - "Abin Da Ke Cikin Rai Na" (daga fim ]in 'Mansoor')
Wannan wakar ita ce 'yar'uwar wakar "Jirgin So" ta Umar M. Shariff; dukkan su sun fito a fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu.
Wakar soyayya ce. Abdul D. One, daya daga cikin yaran Umar M. Shariff, shi ne ya rera ta tare da mawakiya Khairat Abdullah. Wannan waka dai ta fito daga Kaduna, akasin yawancin wakokin zamani da ke fitowa daga Kano.
Abin da ya kara daga wakar shi ne kasancewar ta cikin fim din Ali Nuhu mai suna 'Mansoor' wanda ya na daga cikin manyan finafinan shekarar 2017.
Wannan fim ya sha talla a shafukan sada zumunta, da yake Ali Nuhu, wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Kannywood, shi ne ya shirya fim din kuma ya ba da umarni, sannan jarumin shirin, wato Umar M. Shariff, mawaki ne mai dimbin masoya, wadanda ke so su ga yadda ya yi a fim din.
Masoyan Ali da na jaruman fim din sun taimaka wajen tallata wakar a Instagram ta hanyar yada bidiyon ta da kuma shirya nasu bidiyon na rawar wakar.

4. DAUDA ADAMU KAHUTU (RARARA) - "Buhari Ya Dawo"
Fitaccen mawakin siyasa Dauda Adamu Kahutu, wanda ake yi wa lakabi da Rarara, ya fitar da wannan wakar ne a daidai lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga London, inda ya shafe watanni yana jinya.
Sanin kowa ne an yi ta shaci-fadi kan rashin lafiyar, saboda haka 'yan Nijeriya da dama sun zaku su ga dawowar sa.
Don haka sakin wakar a daidai lokacin na da wuya sai ta karbu a wajen masu saurare.
Rarara ya yi waar ne a matsayin martani ga masu adawa da Buhari, musamman masu cewa rashin lafiyar zai hana shi ci gaba da mulki. Da ma can Rarara magoyin bayan Shugaba Buhari ne.

5. UMAR M. SHARIFF (tare da Khairat Abdullah) - "Rariya" (daga fim din 'Rariya')
Umar M. Shariff ya ci gaba da rike kambin sa na kasancewa daya daga cikin manyan mawakan wannan zamanin da wakar "Rariya" wadda ta fito a cikin fim din 'Rariya'. Shi da Khairat Abdullah suka rera wakar.
Jigon wakar shi ne soyayya tsakanin saurayi da budurwa. A cewar saurayin, ya yi tankade da rairaya na soyayya da rariya ne, a karshe ya yi dacen samun budurwar tasa a matsayin "tsabar" da wannan tankaden ya samar.
Ya ce: "Tankade na yo na sa rariya, Ke ce ki ka zam tsaba, Zabi na a soyayya." Ita ma ta mayar masa da wadannan kalmomin, tare da nuna masa cewa za ta yi masa sakayya da ba shi zuciyar ta.
Kalmomin soyayya da ake furtawa a wa}ar sun taba zukatan matasa matuka.
To amma ficen wakar ya samo asali ne daga kansancewar ta wakar da ta jagoranci fim din Rahama Sadau, fitacciyar jarumar da sunan ta ya kara yaduwa saboda korar ta daga Kannywood da kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN ta yi a shekarar da ta gabata.
Da yake 'Rariya' shi ne babban fim din da Rahama ta shirya a bana, masoyan jarumar sun yi mata kara wajen tallata wakar a shafukan su na Instagram.
Kwatankwacin dai yadda su ka yi wa wakokin fim din 'Mansoor' na Ali Nuhu, sun rika shirya bidiyo na rawar waka nasu na kan su, su na turawa.
Babu mamaki, lokacin da za a nuna fim din a gidajen sinima, matasa sun rika yin tururuwa zuwa wajen kallo, don su ga yadda aka yi rawar wakar.

6. ADO ISA GWANJA - "Ayyaraye Indosa, A Sha Ruwa"
An fi sanin Ado Isa Gwanja ne da wakar "Kujerar Tsakar Gida" wadda ta kasance waka mafi karbuwa ga matan biki a fadin arewacin Najeriya tun bayan da ya rera ta shekara biyu kenan.
Ba a daina jin "Kujerar Tsakar Gida" ba, sai kuma Gwanja ya so ya rike kambinsa na jagaba a wakokin gidan biki da wakar "Mata Mu kame kam".
To amma wakar da ta fi jan hankali a bana ita ce wakarsa mai taken "Indosa".
Akasin sauran, ita ba wakar rawar cashewa ko girgiza jiki ba ce; waka ce ta saurare wadda kuma za a iya rausayawa.
A cikin ta, Gwanja na yabon kan sa ne saboda ficen da ya yi a matsayin mawakin gidan biki. Ya yi nuni da cewa yanzu ya zama gamji a cikin mawaka, wato ya gagara a sare shi.
Ya ce duk da yake wasu na cewa mata ya ke yi wa waka, to ya tabbatar in har ya doka wakar sa, har mazan ma sai sun taka.

7. NURA M. INUWA - "Ranar Aure Na"
Nura M. Inuwa ya rera wakar "Ranar Aure Na" ne sakamakon auren da ya yi a wannan shekarar a Jihar Katsina.
A wakar, ya yi godiya ga Allah da ya nuna masa ranar aurensa da kuma jama'ar da su ka je bikin auren, tare da bayyana farin ciki da wannan al'amari.
Haka kuma ya tabo masu adawa da shi a kan wannan aure, ya nuna cewa Allah ya yi ko da su ba su so. Ita ma amaryar, ya yi addu'ar Allah ya ba su zaman lafiya.
Da yake Nura mawaki ne mai dimbin masoya saboda wakokinsa na soyayya, kuma an jima ana jiran ranar aurensa, wakar ta karbu sosai, musamman wajen matasa.

8. ASMA'U SADIQ - "Dolin-Dolin"
Asma'u Sadiq ta zama kallabi a tsakanin rawunna da wakarta ta "Dolin-Dolin". Waka ce ta gada. Jigon wakar shi ne soyayyar samari da 'yanmata, musamman a gargajiyance.
Wakar ta yi fice musamman saboda yawan saka ta da ake yi gidajen rediyo na FM a garuruwan Arewa.
Duk da yake an kira ta "Dolin-Dolin", wannan waka ba amshi daya ba ne ta ke da shi; hade-hade ce ta wasu wakokin gada guda biyar, wato "Dolin-Dolin", "Soriyalle Maigida Na", "Kacalle-Kacalle Mu Yi Gada", "Mai Zamani 'Yanmata", da "Warai-Warai".
A karshen wakar, zabiyar ta kawo wani baiti da ya yi kama da na wakokin hip-hop.

9. MORELL - "Aure"
Wakar "Aure" ta Morell ce kan gaba a bana cikin rukunin wakokin hip-hop. Duk da yake tun bara ya saki wakar, amma dai ba a samu wadda ta doke ta a fagen ba.
Wakar ta rike matsayin ta ne bayan fitar bidiyo ]in ta da ya faru a cikin wannan shekara ta 2017, wanda Moe Musa ya ba da umarni. Akwai Ali Nuhu a bidiyon.
Sunan Morell na asali dai shi ne Musa Jikan Musa, kuma ya yi wasu wakokin wadanda su ka hada da "Karota", "Borno", "Safay", "Ganga Da Garaya" da kuma "Ba Wani Bugatti".
Wakokin hip-hop na Hausa da su ka kara da wannan wakar sun hada da wadda marigayi Lil Ameer ya yi mai taken "Dance for Me - Ni Ameer Na Kowa Ne" da wakar "Arab Money" ta Nomiis Gee.

10. NAZIRU M. AHMAD - "Rawa, Rawa"
Naziru M. Ahmad ya yi fice wajen wa}o}in sarakuna da kidan gargajiya, musamman wajen yin amfani da tambura da tallaye da ganguna da algaitai.
Amma ya kan yi wakoki na soyayya ko na aure, da sauran su.
A bana, hazikin wanda ake yi wa lakabi da Sarkin Waka, ya rike mukamin sa ta hanyar sakin wakar "Rawa, Rawa".
Wakar biki ce wadda ya yi hikimar kawo ta da salon gargajiya, ana buga ganguna, sannan ga 'yan amshi su ma su na sako kalmomi kwakwankwacin yadda su Musa Dankwairo ke yi.

Friday, 29 December 2017

WASIYYA GA ANGO : Dabi'u Goma Da Ango Zai Mua'malance Su Domin Samun Zaman Lafiya Da Amaryarsa - Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa


Imamu Ahmad (RA) ya yi wa dansa wasiyya da wasu abubuwa guda (10) wadanda za su taimaka wajen zama da mace lafiya.

Yace ya kai da Na, hakika ba za ka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabiu (10) da za ka mu'amalanci matarka da su don haka ka kiyaye su.

NA DAYA DA NA BIYU:
Hakika su mata suna son tausaswa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun Karancin soyayya da kauna.

NA UKU: Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin data dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakanin ku.

NA HUDU: Hakika su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar daddadan kanshi, magana mai dadi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yanayin ka.

NA BIYAR: Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkin sa.

NA SHIDA: Dukkan mace tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, to kada kayi kokarin raba ta da danginta ta hanyar bats zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su.

NA BAKWAI: Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan hankalin da take yiwa maza, don haka kada ka hayayyaqo mata a lokacin da ta yi wani kuskure kana kokarin gyara ta ta karfin tsiya sai ka Karya ta, karya ta kuwa shine sakinta.

To kada kuma ka kyale ta tayi abinda taga dama ko kuma taci gaba da yin kuskuren, da sunan a karkace take, domin sai ta bijire maka daga karshe taki yi maka biyayya, kai dai ka kasance da ita baina baina.

NA TAKWAS: To kuma ka sani cewa su mata sun dabi'antu akan Kafircewa miji da yi masa butulci da kuma musun abin alheri. Idan da zaka kyautatawa mace tsawon shekara ko zamani sai wataran ka munana mata, za ta ce me ka taba yi min?. To kadaa wannan hali Nata ya sa ka kyamace ta gaba daya, domin idan ka kyamaci wannan dabi'ar daga gare ta to zaka yarda kuma da wasu halayen nata masu kyau.

NA TARA: Ita mace ba kamar Namiji bace, tana rayuwa ne cikin rauni na jiki dana ruhi, saboda haka ne ma Allah mds ya dauke mata wasu daga cikin farillan da ya wajabta mata a wadanban lokuta saboda wannan rauni na ta. Dubi yadda Allah ya dauke mata sallah kacokan a wannan yanayi ( na haila) ya jinkirta mata rama azumi har sai lafiyar ta ta dawo nishadinta ya daidaitu, to ka saukaka mata umarnika da hane- hanenka a wannan yanayi kamar yadda ubangijinta ya saukaka mata farillansa. 

NA GOMA: Ka sani cewa ita mace ribatacciyar baiwa ce a hannunka, don haka ka ji Kanta ka tausaya mata ka kuma dauke kai dangane da rauninta sai ta zamar maka kyak-kyawar abokiyar zama kuma mace ta gari.

Annabi (SAW) yace" Inai miku wasiyya da mata Ku rike su da alheri, domin ita mace an halicce ta ne daga kashi tankwararre kuma Mafi tankwarewar kashi shi ne sama , idan ka matsa sai ka tayar dashi to zaka karya shi, idan kuma ka barshi haka to zai dawwama a tankware kuma a karkace, to don haka inai muku wasiyya ta gari dangane da mata.

Kuma Annabi (SAW) yace" fiyayyenku shi ne fiyayyenku ga iyalansa kuma ni ne mafi alherinku dangane da iyalaina"

Allah ya bamu ikon zama da iyalan mu.

Daga shafin hukumar Hisba ta jihar Kano

Jaruma Jamila Nagudu Ta Fadi Matsayinta Na Korar Rahama Sadau da Moppan Tayi

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa dake yi wa lakani da Kannywood watau Jamila Umar wadda aka fi sani da Jamila Nagudu ta bayyana matsayar ta game da kin dake dakatarwar da akayi wa Rahma Sadau daga harkokin fina-finai duk kuwa da hakuri tare da nadamar da tayi.

Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da take ansa tambayoyi daga wasu matambaya a shafinta na dandalin sada zumunta na Facebook.

wani bawan Allah ne yayi mata tambaya kamar haka: "Abinda yafi jan hankali a kannywood yanzu shine, rigimar da akeyi tsakanin Ali Nuhu da kungiyar Moppan akan korar kare da akayiwa Rahma Sadau, Saboda wani hoton bidiyo da suka yo da mawaki Classiq. Duk da jarumar ta bayar da hakuri kuma ta nemi afuwar Gwabna Dr Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sunusi Lamido Sunusu II, amma anyi watsi da ita. Menene ra'ayin ki akan wannan dambarwa?


Sai jarumar ta kada baki tace: "Gaskiya ara'ayina abinda akayiwa Rahma Sadau ya yi tsauri da yawa. Domin duk wanda ya yi laifi ya gane kuskuren sa ya kamata ayi masa afuwa. Kuma suma Moppan din ai suna laifi. Wallahi da zamu tona masu asiri suma duk sai an canja shuwagaban nin kungiyar. Dan dai kawai tonon silili ba shi da kyau ne."

Thursday, 28 December 2017

karshen Tika,Tika tik : Saukar Da Audion UMAR IBN KHADDAB (R.A) KARE NE INJI ABDULJABBAR

Wannan shine audio da munka alkawanta muku da cewa ku kasance damu sai ku saukar a wayoyinku domin saboda nasan cewa wasu sunyi mana uzuri suna jira shin zamu kawo,ko karya ce muke to, Alhmdllh sai ku saukar a wayoyinku domin ji da kunnuwanku na basira.



Download Audio here

TO FAH :- UMAR IBN KHADDAB (R.A) KARE NE :- INJI ABDULJABBAR Nasiru Kabara




.
Kamar yanda daya daga cikin magabata ke cewa"Mu'awiya ibn Abu sufyan r.a kamar kyallen kofa ne duk wanda ya fara ta6a shi da sannu zai shiga zuwa ga ta6a manyan sahabbai" Hakane domin a lokacin da Abduljabbar Nasiru kabara ya fara ta6a mutuncin sahabi mu'awiya r.a malamai da dama suna cewa wallahi wannan mutumin shi'a ce yake dabaqawa ta karkashin kasa, sai ya sake fitowa da wata yaudara ta cewa wai yana kariyar ahlul baiti. Cikin wannan rigar ta ahlul baiti yake la6ewa yaci zarafin sahabbai, magabata da malamai. Amma yanzu zani rinka sawo muryarsa kowa yaji da kunnensa shi ya fada ba kage muka yi masa ba. Babbar matsalar Abduljabberi shine yiwa Annabi s.a.w tare da canza abinda ya fada kamar yanda zan kawo yanzu inda yake cewa sahabi umar r.a kare(dog) kuma har yake jaddada cewa annabi yace masa haka.kamar yanda zaku gani.
.
Abin mamaki da takaici shine akwai wani hadisi da mafi yawan yara masu karatu a islamiyya sun fahimce sosai, wannan hadisin shine"Annabi s.a.w yana mai komawa kyautarsa bayan ya bashe ta tamkar kare ne wanda idan yayi amai zai koma ya lashe shi" to amma shi Abduljebberi ba wannan ruwayar ya kawo ba. Ya kawo wace ta zo a cikin littafen bukhari hadisi na 2623.
حدثنا يحي بن قزعة:حدثنا مالك،عن زيد بن أسلم،عن أبيه:سمعت عمر بن الخطاب رضى الله عنه يقول:حملت على فرس في سبيل الله،فأضاعه الذي كان عنده، فأردت أن أشتريه منه،وظننت أنه بائعه برخص،فسألت عن ذلك النبى صلى الله عليه وسلم فقال،"لا تشتره وإن أعطاكه بدرهم واحد، فإن العائد في صدقيه كالكلب يعود في قيئه.
FASSARA:
Daga Yahaya ibn qaza'ata, daga Malik daga Zayd ibn As-lam daga babansa yace naji umar ibn khadab r.a yana cewa"na bada doki saboda Allah, sai naga wanda ni baiwa shi ya walakanta shi, sai nayi niyyar na saye shi daga garesa, kuma sai nayi zato zai ma saida mani shi da sauki(arha). Sai na tambayi annabi s.a.w shin ko zan iya sayensa? Sai Annabi s.a.w yace"kada ka saye shi koda ya saida maka shi darhami daya, sai annabi s.a.w yace"hakika mai komawa kyautarsa kamar kare ne dake komawa ga amansa.
.
To a wannan ba sai na tsaya sharhi ba don a duk hadisin nan ina ne Annabi s.a.w ya cewa Umar ibn khaddab r.a kare? Amma Abduljebberi cewa yayi"Annabi s.a.w ya cewa umar kare, wai harda maimatawa cewa Annabi s.a.w ya cewa umar ka zama kare subhanallah. Shin Allah bai yiwa Annabi karya ba? Bai canzawa Annabi s.a.w magana ba?  Ga hadisi "Mutawatiri"wanda sahabi  saba'in da biyar(75) ruwaito shi . Yana cewa"wanda duk ya yi mani karya‏ ‏da gan-gan ya za6i wurin zamansa cikin wuta.
من كذب علي متعمدا فليتبوء مقعده من النار‎  ‎
wannan karyar da gan-gan Abduljebberi ya fesa ta. cewa
العائد في صدقته كالكلب يعود في قيئه
A cikin sharhin littafen "Muwatta Malik" mai suna "Tanweerul Hawaleek" a karkashin wannan hadisi na 624 inda yake cewa
كالكلب يعود في قيئه: وجه التشبيه أنه أخرج في الصدقة أو ساخه وأدناسه فأشبه تغير الطعام إلى حال القيئ.
Misiltawa ne aka yi na dabi'ar amma ba'ana nufin mutum ba amma saboda kiyayyarsa da sahabbai ya fadi haka ga sahabi na biyu umar ibn khaddab. Allah ya karya makiya sahabbai.

Ku kasance da hausaloaded.com zamu kawo muku wannan audio inda malam abduljabar yace haka. 

Film :- Yadda Fim Din Yaki A Soyayya Zai kasace

@Regranned from @nafeesat_official -  Here’s BILKEES ABDULLAHI.... Once upon a time, she was a life saver!!! Producer
Nafisa Abdullahi 
Co-Producer 
Nasir Ali Koki

Directed by
Alpha Zazee Muhammed 
D.O.P
Murtala Balala
Nelcon Nel

Sound Engineers 
Saddiq Balala
Manniru A.zango

Costume
Nahaz Fashion House 
Set Design 
Tahir I.Tahir

Editor
Ibrahim Shehu

Makeup 
Nahaz Fashion House 
Welfare 
Tahir FKD

Story/Screenplay 
Abdul M.Shareef
Nafisa Abdullahi

Location managers 
Abubakar S.Muhammed
Suleiman Sir Zeesu 
Contunity
Musty Fashion 
Songs: Written and produced by 
Umar .M Shareef

Executive producer 
Nafisa Abdullahi 


Wednesday, 27 December 2017

YA TSOTSI NONON BUDUWARSA, KO ZASU IYA AURE ? Dr Jamilu Yusuf Zarewa


Tambaya? 

Assalamu alaykum. Tambaya  malam saurayi da budurwane shaidan yashiga tsakaninsu har yakaiga saurayin ya tsotsi qirjin budirwan har saida ruwa ya fito. Hakan yafaru ba so dayaba ba biyu ba amma bata taba ganin ruwanba sai ranar. To mallam yaya hukuncin aurensu, ya halatta suyi auren? 

Kuma minene hukuncin shan Ruwan da yayi 

Amsa:
Wa'alaykumussalam, 

To dan'uwa wannan abin da suka aikata mummuna ne, Tun da Allah ya haramta taba jikin matar da ba ka aura ba,  kuma kofa ce da za ta kai zuwa  zina, idan mutum ya tsotsi nonan mace bayan ya girma Amma babu ruwa a ciki, wannan ba zai haramta musu aure ba, amma idan akwai ruwa a ciki, to
malamai sun yi sabani akan hakan
zuwa maganganu guda biyu :

1. Ya halatta su angunce, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure
shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru
biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. “Shayarwar da
take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha
saboda yunwa” , Bukhari lamba ta : 5102,
ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga
nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan
ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba
zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita
ce maganar mafi yawan malamai.

2. Yana haramta aure, saboda ko da yaushe
mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare
shi, domin Annabi s.a.w. ya umarci matar Abu-
huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a
gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a
hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a
lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake
nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi
tasiri wajan haramcin aure.                 Zancen da ya fi karfi
shi ne nonon da mutum ya sha bayan ya girma ba ya haramta aure a tsakaninsa da matar da ta ba shi.
            
Don neman Karin
bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67.

Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya saba masa zai same shi a madakata.

                
Allah ne mafi sani.

26/12/2016 

*Dr Jamilu zarewa*

Labari Da Dumi Duminsa:- Dan Shugaba Buhari Ya Yi Hadari Da Babur


Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da cewa a halin yanzu dan Shugaban Kasa, Yusuf Muhammad Buhari ya kwance a wani asibiti da ke Abuja bayan ya yi hadari da Babur a daren jiya a yankin Gwarimpa da ke Abuja.

Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bayyana cewa Yusuf ya samu kariya a hannu da kuma rauni a kansa amma ya nuna cewa yana ci gaba da samun sauki. Ya kara da cewa Shugaba Buhari da Uwargidansa na barar addu'a ga dan nasu don ya samu lafiya.

Karanta Hotunan Yadda Tambayoyin Da Masoyan Rahama sadau da sunkayi mata har da Tambaya "ke Budurwa ce "? Amsa "A'a" Karanta

Labarinnan da shafin hausaloaded .com ya buga wanda ya watsu kamar wutar daji, watau wanda tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta bayyana cewa, ita ba cikakkiyar budurwa bace fil a leda: ta rasa budurcinta , ya dauki hankulan mutane akaita bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.

Akan idanmu aka fara tambaya da amsar tsakanin Rahama Sadau da masoyanta aka kuma gamata.

Rahamar ta bayar da mintuna talatin inda tace amata kowace irin tambaya akeso zata bayar da amasa, ranar Asabar din data gabata, mintuna taltin din har suka wuce amma tambayoyi nata kara durarrowa, wannan yasa tadan kara tsawon lokacin.

Anan dukkan tambayoyi da akawa Rahamar ne wadanda ta bayar da amsa, ciki hadda inda ta bayyana cewa ta rasa budurcinta, sau biyu ana tambayarta shin udurcinta na nan ko ya fashe?,

ita kuma tana bayar da amsar cewa "a'a na rasa budurcina".













                            B.           















































Akwai wasu tambayoyi da amsarsu da basu wuce hudu zuwa biyar ba da basa nan, sannan akwai kuma tambayoyin da aka mata wadanda bata amsasuba saboda lokacin data bayar ya wuce, suma basa nan.

All Image © HTDL

N’Golo Kante Wins 2017 French Player Of The Year Award

Chelsea midfielder N’Golo Kante has won the French Player of the Year award for 2017.
The former Leicester City star got 92 votes to beat Paris Saint-Germain teenager Kylian Mbappe to the award by five votes.

He had won back-to-back Premier League titles with Leicester City and then the Blues, and proved himself as one of the best midfield enforcers in the game.
Real Madrid striker Karim Benzema took third with 52 votes.

The poll, organised by France Football, included votes from four past winners including 2016 winner Antoine Griezmann, France boss Didier Deschamps and ex-Uefa president Michel Platini.

Kante has this year won the PFA Players’ Player of the Year and FWA Footballer of the Year awards.
This is in addition to landing Chelsea’s Player of the Year award as well as being included in the Premier League Team of the Season.

Sources:-okay

Monday, 25 December 2017

'Yan Kannywood sun zama dankali sha kushe' inji Hadiza Saima Muhammad

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Muhammad, wacce aka fi sani da Hadizan Saima ta ce masu yin fina-finan na Hausa sun zama abin nan da Hausawa ke cewa dankali sha kushe.

"Allah yana kallon abin da muke yi; idan muna yi don mu bata ko mu gyara mu fadakar, Allah ya sani.

"A cikin fina-finan da muke yi ana yin karatun Al-Qur'ani, ana jan baki a fassara, ana ce wa 'Allah ya ce, Annabi ya ce'. Shi ma duk wannan koya rashin tarbiyya ne?", in ji Hadiza, lokacin da take amsa tambayar da BBC ta yi mata kan zargin bata tarbiya da ake yi wa 'yan fim.
Ta kara da cewa: "Ka san mu dankali ne sha kushe, ana sonmu ana kushe mu. Amma haka za mu yi ta tafiya tun da haka Allah ya yo mu.

"Haka za a yi ta hakuri da mu, mu ma muna hakuri da masu kushe mu kuma a hankali za su fahimce mu. Na san wasu ma sun fahimta yanzu."
Jarumar, wacce akasari ta fi fitowa a matsayin uwa, ta kara da cewa ta soma sha'awar fina-finai ne tun lokacin da take da aure.

A cewarta, "Karance-karancen littafai da kallon fina-finan tarihi ne suka sa na soma sha'awar shiga fim.

"Na kalli fim din 'Ki Yarda Da Ni' a lokacin ina gidan mijina, kuma da aurena ya zo karshe sai na ji sha'awar shiga fim. Na soma fim ne sama da shekara 16 da suka wuce kuma na fito a fim fiye da 300.''

"Wani darakta ne marigayi Tijjani Ibrahim ya tambaye ni irin rawar da na fi so na taka a fim, ni kuma na ce masa na fi son fitowa a matsayin uwa.
"Shi ya sa tun daga wancan lokaci nake fitowa a matsayin uwa, tun ma ina da kuriciya ake yi min kwalliya irin ta uwa domin na taka irin wannan rawar."

Taurarin Fina Finan Hausa Sun Zama Jakadun Jamiar NOUN kalla a cikin Hotuna


@hutudole

Taurarin fina-finan hausa sun zama jakadun jami'ar nan ta koyi da kanka da ake kira da NATIONAL OPEN UNIVERSITY "NOUN" a takaice.

Reshen jami'ar dake jihar Kano ne suka shirya wani taron bita akan muhimmancin jami'ar a tsakanin al'umma.

Jaruman fina-finan Hausa da dama sun halarci taron kuma wasu daga cikinsu sun samu zama jakadun wannan jami'a.

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah da Al'amin Chiroma da Samira Ahmad da Umar Gombe da Bello Muhammad Bello(General BMB) da Hamisu Lamido Iyantama na daga cikin wadanda suka samu zama jakadun wannan jami'a.

Fatan mu Allah ya tayasu riko