January 2018 - NewsHausa NewsHausa: January 2018

Pages

LATEST POSTS

Wednesday, 31 January 2018

Ado Gwanja Na Dab Da Angancewa Kalli hotunan Amaryasa

Duniya kenan shima ado gwanja yayi kusan angancewa wannan sune hotunan amaryasa wanda nan gaba kadan za'a auren limamin mata wato ado gwanja wanda nasan mata gari wa gari zasu halara wajen bukin babban mawaki .




Tuesday, 30 January 2018

Haukan Talakawan Nijeriya Ne Yasa Har Yanzu Suke Nuna So Akan Buhari Inji Ummi Zeezee

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee wadda sananniyar masoyiyar tsohon shugaban kasace, Janar Ibrahim Badamasi Babangida kuma a bayabayannan ta fara nuna goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar tayi wasu kalamai masu kaushi akan shugaba Buhari ta masoyanshi.

Ummi ta yi tambaya a dandalinta na sada zumunta da muhawara cewa idan ba atikuba wa kuke tunanin zai iya/ya kamata ya mulki Najeriya?, mutane sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan wannan tambaya ta Ummi. 
Daga cikinsu akwai wani bawan Allah daya ce shi yana ganin Atiku baya daga cikin wadanda suka cancanci zama shuwagabannin Najeriya.

Ummi ta mayarwa da wannan mutumin amsa kamar haka" Mutane da basa fahimtar turancin da bai taka kara ya karya ba, abunda nayi posting fa ba dogon magana nake so ba ko kushe wani dan takaran da ba naka ba. abunda post dina yake nufi shine, in Atiku ne dan takararka ka rubuta sunansa in kuma bashi bane ma ka rubuta sunan dan takaranka ko kuma ka rubuta nobody amma ba surutai na adawa nake so ba a comment pls dan in surutan adawa kuke so akan Buhari to ai in kuna da kunya baku da bakin magana domin a abubuwan da yayi alkawarin zaiwa kasa in an zabeshi har yanzu baiyi ko daya ba kuma duk wanda zaiji tsoron Allah ba tsoron Buharin ba yasan baiyiwa kasa komai ba in banda talauci da fatara da yunwa daya sa kasar a ciki ammah talaka da yake mahaukacine baisan ciwon kansa ba wai har yanzu shi yake so. Mtwssss Allah ya sauwake da yan Nigeria hausawa. Wallahi da a turaine bai isa yayi bakin milki irin wannan ba, da talakawan da kansu zasu ce a canja shi"

Sources Fimhausa

Sharhin fina finai Abubuwan Burgewa Da Kura Kurai Da A cikin Fim Din Hasashe

Suna: Hasashe
Tsara labari: Abdullahi Amdaz, Bashir Dan Rimi.
Furodusa: Nazir Auwal Dan Hajiya
Director: Ali Gumzak
Kamfani: Ali Nuhu Team
Jarumai: Ali Nuhu, Garzali Miko, Hafsat Idris Barauniya, Sadiya Adam, Bilkisu Abdullahi, Ammar Umar, Hajara Usman da Amina Maiduguri.

Abubuwan birgewa:

1-wakokin fim din sun yi dadi sun kayatar da masu kallo
2- Jaruman sun yi kokari wurin fito da labarin yanda mai kallo zai fahimta.

Kurakurai:

1- Shin wanene Najib? mai kallo kawai ya gan shi yana yaudarar ‘yan mata kuma daga bisa ni ya yi aure ko iyayensa ba’a taba nunowa ba ko anyi maganarsu ba.
2- Shin duk ‘yan matan da ya ke kulawa basu da gidan iyaye sai dai kullum a gansu a wurin shakatawa? sannan ya aka yi idan Najib yazo gurin shakatawa ‘yan matansa kullum ake arashi suke haduwa ko kuma sanar musu yake yi shi da ya ke abinsa a boye baya san asirinsa ya tonu?

3- Menene asalin sunan jarumin labarin acikin fim din (Garzali miko) masu kallo sunji wasu suna kiransa da Najib wasu kuma Kabir wasu kuma Abdurrashid har fim din ya kare ba’a tabbatar da tar tibin guda daya ba.

4- Akwai wurin da Najib yake chatting da burwarsa a gidansa kawai aka ga ya ajiye wayar ya ta shi matarsa kuma aka ganta ta zo ta dauka tana dubawa a wurin an nuna kamar don ta dauka ya ajiye ya ta, duk boye mata sirrikansa da yake.

5- An nuna Jawahir tana da karamin ciki a hotan gaba wanda aka kuma nuno su sai aka ga har ta haihu da aka kuma nuno su sai kuma aka ga har ‘yar ta girma dab da dab din ya yi yawa duk da fim ne ya kamata ace idan ma za’ayi haka to ace an rubuta bayan lokacin kaza.. sannan aga wani abin kuma ya faruwa.

6- Zaren labarin bai tafi ya dire ba sai ya dinga tafiyar hawainiya idan aka kunno matsala mai kallo ya karkatu akan ya ga ya abin zai karke sai kuma a sake kunna wata ba tare da an warware waccen ba har fim din ya kare abubuwa da yawa ba’a ga karshensu ba.

7- Camerar daukar hoto bata fita yadda ya kamata ba a fim din.
8- Bai kamata a ga mai aikin gidan mujahid ta ce masa wai bari ta shiga wanka ba shi kuma yace tohh a gaske hakan zai yi matukar wahalar faruwa menene alakarsu? tun da ba matarsa bace ina ruwansa da wankan ta.

9-Menene aikin da Najib ya fadawa budurwarsa zata yi masa a gidan Mujahid? tunda mai kallo bai ga wani abu da ta yi ba a zuwanta gidan na bincike ba kamar yanda Najib ya nuna.

10- A gaske zai yi matukar wahala budurwa ta yi wa saurayinta korafin yana kula kulan ‘yan mata sannan ya ce mata wai shi ba aurensu zai yi ba karya kawai yake yi musu kuma budurwar bata nuna wani bacin ranta ba, kawai ta yadda da abinda ya fadamata duk da an saka musu rana kamar yanda Najib ya fadawa Fadila.

Karkarewa:

Labari ne mai kyau amma bai sami tsari mai kyau ba shiyasa ya ruguje kuma an gaza wurin fito da ma’anar labarin sannan an gaza bai wa labarin karshe yanda ma mai kallo zai fahimci makasudin labarin. Allahu a’a lamu.

Monday, 29 January 2018

Ta Baro Jamhuriyyar Nijar Zuwa Nijeriya Don Ta Yi Ido Hudu Da Mawaki Umar M. Sharif


Daga Umar Ridwan

Wannan yarinyar da kuke gani sunanta Maryam. Ta niko gari tun daga Niger zuwa Nijeriya don ta ga shaharren mawakin finafinan Hausan nan dake jihar Kaduna, wato UMAR M SHARIF wanda ta ce yana bala'in burge ta shi ya sa ta keso mafarkinta na yin ido hudu da shi ya zamo gaskiya.

'Yar shekara 17 da haihuwa, Maryam ta ce suna zaune ne a Maradi. Ta kara da cewa iyayenta sun rabu kuma tana yawace-yawace wanda ke sa mahaifiyarta cewa yawon karuwanci ta keyi, abunda a cewarta ke ba ta mata rai, shi ya sa ta taho Kaduna a don ta yi waka da gogan nata Umar M Sharif ko za ta ji sanyi a ranta. Yau kimanin kwanta 2 kenan a Kaduna. 

Idan Allah ya sa akwai wanda ya san Umar M Sharif ya sanar da shi cewa wata masoyiyar shi na neman shi. Za mu saka cikakkiyar hirar gobe a cikin shirin GARI YA WAYE a tashar DITV/Alheri Radio Kaduna. Ku saka ido!

Sunday, 28 January 2018

MUHAWARA: Kuna ga mace zata iya zama babbar jaruma a yau ba tare da ta sadaukar da bangaren addinin ta ko al'adanta ba?

MUHAWARA: Kuna ga mace zata iya zama babbar jaruma a yau ba tare da ta sadaukar da bangaren addinin ta ko al'adanta ba?

A kwanakin baya ne jaruma Nafisat Abdullahi ta saka hoton yar film din India wato Deepika Padukone wanda sananne cewa Nafisa Abdullahi fan din ta ne.


Mutane da yawa sunyi korafi akan hoton domin mafi yawancin jikin jaruman a waje ne, wanne korafin ne yasa Nafisat Abdullahi ta maida martani cikin mamaki, tana cewa "Jaruma ma ce fa, meye kuke tsammani"

Shin kana ga mace zata iya zama babbar jarumar film a yau ba tare da ta sadaukar da bandaren addinin ta ko sana'anta ba?

Friday, 26 January 2018

kalli Hotunan Manyan Jarumai Sun Halarci Happy Birthday Taya Murna Zagoyowar Ranar Haihuwar Nafisat Abdullahi

Manyan masu ruwa da tsaki a harkar fina-finai hausa na masana'antar Kannywood sun halarci walimar taya murnar zagoyawar ranar haihuwar jaruma Nafisa Abdullahi.

A ranar laraba 24 ga watan janairu ne jarumar ta cika shekara 27 a duniya.

Domin nuna farin cikin zagoyowar wannan muhimmin ranar a rayuwar ta ta hada wata walima ta musamman wanda har ta gayyaci kawaye da abokan huldar ta a masana'antar kannywood.

Anyi wannan sharholiyar a dakin cin habinci na bristol palace hotel dake Kano.

Manya baki da suka halarci wajen walimar sun hada da shugaban hukumar tace fina-finai na jihar kano  Alhaji Ismail Na'abba Afakallah da masu shirya fina-finai Aminu Saira da Nazir Dan hajiya.

Ga hotunan jarumai da sunka halarci bukin 










Ku kasance da www.hausaloaded.com

Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau

Kalli wasu kayatattun hotunan Rahama Sadau



Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata da suka kayatar, tayi kyau sosai, muna mata fatan Alheri.


Thursday, 25 January 2018

Zafaffan Hotunan Jaruma Aisha Tsamiya Da Ta Sanya A Sabon Account dinta Na Instagram

Wannan sune sababbin hotunan da jarumar ta sanya a shafinta na insagram a sabon account, bayan yan shige da fice wato hackers sunyi hacking din account dinta.




More @hausaloaded.com

Wednesday, 24 January 2018

ZUWAN KWANKWASO KANO: Kwankwaso Ya Nada Dambazau Shugaban Kwamitin Tsaro


...Manyan tsoffin sojoji da na 'yan sanda za su yi masa rakiya

Tsohown gwamnan jihar Kano kuma dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar jihar Kano ta tsakiya Dakta Rabi'u Musa

Kwankwaso ya nada kwamitin mutane 19
da za su tabbatar da samuwar tsaro yayin ziyarar da zai kai a jihar ta sa ta haihuwa ranar 30 ga watan Janairun nan da muke ciki.

Kwamitin tsaron dai kamar yadda muka samu ya samu shugabancin
1.Janar Idris Bello Danbazau,

2  Barista Munir Dahiru ya zama sakataren kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da

  3.AirCommodore Ali Bebeji,

 4.Air Commodore Zakari Baffa

5.Colonel Usman Garun-Malam,

6.Air Commodore Salisu Yusha’u

7.Major General Ahmad Tijjani Jibril, da kuma

8.AIG Bala Abdullahi.

Haka zalika sauran sun hada da
9.Commander Sarki Aliyu Daneji,
10.Alhaji M.T Usman,

11.Hon. Lawal Sale Gaya,
 12.Alhaji Baba Umar,

13.Alhaji Tijjani Dambazau,
15.CP Rabi’u Mani,

16.Commander Kamilu Wudil,
  17.Alhaji Sanusi Surajo Kwankwaso,

 18.Alhaji Adamu Garko dakuma

19. Alhaji Muhammad Ado Danbatta.

Adon gani Ga fara'a Ga Hanci ga kuma zubi irin Na Yar fulani, Jaruma Zata Sa Maza Layi Ganin Wannan Hotuna

Ba sai ka wahalar da kanka ba, ganin hotuna fitacciyar jaruma Maryam Booth zaka hangi abun da Nura ya hango yayin da yake rubuta wakar shi.




Jarumar ta sako wannan hotunan a shafin ta na Instagram.

Ga kyau ga fara'a ga zubin irin yar fulani.


Sources:pulse.ng

Anyi turereniya wajen kallon fim din Adam A Zango Gwaska Returns a kano

Dinbim jama'a suka garzaya babban sinima dake Ado Bayero Mall a jihar Kano domin kallon sabon shiri fim da Jarumi Adam A.Zango ya fitar ranar juma'a.

Ma'abotan fina-finai hausa kuma masoyan babban jarumin shirin "Gwaska" sun fito kwar da kwarkwatan su domin ba idanuwar su abinci.

Abun kamar a turai ganin dinbim jama'a da suke turereniya wajen karbar tikitin shiga dakin kallo.

Wannan shirin wanda Adam Zango ya taka muhimmin rawa a ciki a matsayin shi na babban jarumin shirin yana daya daga cikin fina-finai hausa da aka fitar kwana-kwana nan wanda ya samu cinciridon mutane wajen haskawa a sinima.

Goyon bayan jarumai

Suma wasu daga cikin manya-manyan jaruman masana'antar Kannywood sun garzaya wajen fim din "Gwaska Returns" domin mara ma abokin aikin su baya.

Cikin su akwai mawaki Daudu Kahutu Rarara da babban mai shirya fim Hamisu Iyantama da Yakubu Muhammed da kuma Falalu Dorayi tare da Bello Muhammed Bello wanda ya fito a matsayin jarumi cikin shirin.

A bangaren mata ita ma Maryam Gidado da sabbin shiga watau tagwayen Kannywood suma ba'a bar a baya ba wajen kallo.

Masoyan Adam Zango sun nuna masa kara tare da jinjina masa bisa kokarin da yayi wajen fitar da wannan shirin fim wanda cigaban na farko na mai taken "Gwaska".

Sai dai abin mamaki Ali Nuhu da Jama'ar sa ba'a gansu a wajen ba, ta wata majiya hakan baya rasa nasaba da takun sakar da ake a tsakanin Jaruman Guda biyu.

Miji na ya barni inyi fim a gidansa" inji Saratu Gidado


Jaruma Saratu Gidado ta bayyana cewa mijin ta ya barta tayi film a gidansa kuma ta jawo hankalin sauran mazaje da suyi koyi da wannan sunnah.

Ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kafar BBC inda tace bata ga aibu wajen hada aure da sana'a ba koda sana'ar film CE.

"Miji na wayayyen mutum ne kuma yana da ilmin zamani dana addini, wannan ya bashi daman fahimtar cewa be wani aibu idan ya barni in ci gaba da film a gidanshi" inji

Tsohuwar Jarumar Finafinan Hausa, Abida Muhammad Za Ta Yi Aure A Ranar Juma'a Mai Zauwa

Tsohuwar Jarumar Finafinan Hausa, Abida Muhammad Za Ta Yi Aure A Ranar Juma'a Mai Zauwa

Abida za ta sake yin aure ne, bayan mijin ta Hamza Rijiyar Zaki ya rasu a shekarun baya.

Mafi Yawwan Hausawa Munafukai ne Inji jaruma Nafisa Abdullahi !!!

Shahararriyar jarumar nan ta dandalin shirya fina-finan Hausa wato Kannywood, Nafisa Abdullahi ta wallafa wani hoto na tauraruwar kasar Indiya, Deepika wanda hoton ya nuna tsiraicin jarumar.

Nafisa ta wallafa wannan hoto ne dai domin taya jarumar fim din Indiyan murnar zagayowar ranar haihuwarta, inda ta kuma kara da cewa da gangan ta sanya hoton da ta san sai wasu sun tofa albarkacin bakin su.

Hakan kuwa bai hana mutane tankawaba, inda wani ya bayyana cewa ta aikata hakan a banza, inda Nafisa ta maida masa da martanin cewa shima kuwa taga yana yiwa wasu jarumai da yakeso abubuwa a dandalinshi shima a banza.


Kannywood: Mafi akasarin Hausawa munafukai ne - Inji Nafisa Abdullahi
Wani da ya mara ma jarumar baya akan wannan al'amari yace, "Hausawa akwai munafurci wallahi, idan bakwason irin wadannan abubuwa daga gurin masu nishadantarwa to kawai a daina nishadantar daku, domin ita harkar nishadantar da mutane abinda ta kunsa kenan".

Bayan daya gama wannan batu nashi sai Nafisa ta rufamai baya da cewa" Rabu dasu.....Asalin munafukaima".

Dawo Da Rahama Sadau Harkar Fim; Akwai Sauran Rina A Cikin Kaba



 Rahama Sadau ta dawo Nigeria bayan tayi wata biyu a kasar Cyprus

Rahama Sadau ta sauka a Nijeriya a ranar 21 ga January bayan ta shafe watanni biyu da rabi ta na karatu a kasar Cyprus.
Fitacciyar jarumar ta sauka ne  da safe a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa babu wani dan wasan fim da ya kai Rahama Sadau jan hankali a kafafen watsa labarai a cikin shekarar 2017.

Hakan ya faru ne saboda ce-ce-ku-cen da aka sha yi a kan korar ta daga masana'antar fim ta Kannywood da kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN ta yi a cikin Oktoba, 2016.

Korar ta biyo bayan rawar da jarumar ta yi da mawakin hip-hop mai suna Classiq a bidiyon wakar sa ta "I Love You" inda su ka yi rungume-rungume.

Kungiyar ta ce bullar bidiyon wakar ya kara jawo wa masana'antar tsangwama a wajen jama'a, musamman masu cewa 'yan fim na bata tarbiyya.

Bayan shekara daya da korar tata, Rahama Sadau ta rubuta wa kungiyar wasika inda ta bada hakuri kan abin da ta aikata, tare da bada tabbacin cewa hakan ba zai kara faruwa ba.

A watan Nuwamba da ya gabata, kungiyar ta gayyato jarumar zuwa wani taro inda za su tattauna kan batun d'age mata takunkumin, to amma sai jarumar ta sanar da su cewa ita yanzu ba ta kasar, ta na Cyprus, kuma ba za ta dawo ba sai a farkon Fabrairu na 2018.

Hakan bai yi wa shugabannin kungiyar dadi ba saboda jarumar ba ta sanar da su cewa ta yi tafiya ba.

Da yawa daga cikin shugabannin kungiyar sun kalli abin da ta yi a matsayin "rainin wato" ga kungiyar.

Saboda haka su ka kauda duk wata magana ta yafe mata har sai ta dawo Nijeriya ta sake neman zama da su.

To amma a watan jiya sai Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bada sanarwar cewa ita ta yafe wa Rahama, kuma za ta duba duk wani fim da ta shirya ko ta fito a ciki.

Shugaban hukumar, Malam Isma'il Na'abba (Afakallahu) ya fada wa mujallar Fim a wata hira cewa hukumar sa ta yafe wa jarumar ne saboda ai ko Allah ma ana yi masa laifi Ya yafe, kuma ba za a dinga zama a haka ba tare da an yafe mata ba.

Furucin nasa bai yi wa MOPPAN dadi ba, har ta ce wannan karya alkawari ne Afakallahu ya yi.

Sakataren kungiyar, Malam Salisu Mohammed (Officer), ya ce hukumar ba ta da hurumin yafe wa Rahama, kuma ai hukumar ta amince da kudirin kungiyar na cewar sai kungiyar ce kadai za ta iya dawo da jarumar.

Officer ya tabbatar wa da mujallar Fim cewa kungiyar za ta maka hukumar a kotu idan har ta tsaya a kan cewar ta d'age wa Rahama takunkumin.

Shi ma shugaban kungiyar MOPPAN na Jihar Kano, Alhaji Kabiru Maikaba, ya bayyana cewa hukumar ba ta da hurumin yafe wa Rahama domin ai ba ita ce ta kore ta daga industiri ba.

Ya ce su a wurin su har yanzu Rahama korarriya ce, kuma ba su amince da yafewar da Afakallahu ya yi mata ba.

Maikaba ya nanata cewa kungiyar sa za ta dauki kwakkwaran mataki a kan batun cewar wai hukumar ta yafe wa jarumar bayan su MOPPAN ba su yafe mata ba.

Ya ce za su zauna tare da hukumar domin samun matsaya a kan lamarin.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ita dai Rahama Sadau ta nemi yafiya ne saboda ta samu damar fitar da sabon fim din ta mai suna 'Dan'iya' sannan ta fi gaba da fitowa a finafinan Hausa.
Yanzu haka ta sa ranar fara nuna shi a gidan sinima na Film House da ke Kano a watan gobe.

Mutane sun sa ido su ga yadda MOPPAN za ta hana nuna fim din tare da fitar sa a kasuwa bayan Hukumar Tace Finafinai ta bada izinin hakan.
©Zuma Times Hausa

Tuesday, 23 January 2018

Obasanjo Tsohon shugaban kasa ya caccaki gwamnatin Buhari, yayi kira na ya dakatar da maganar zarcewa

Yace shugaban yayi aiki ne kasa da yadda jama'a suka yi tsammani bisa ga haka ya dakatar da anniyar sa na zarcewa a zaben 2019

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatin shugaba muhammadu Buhari bisa ga rashin aiwatar da kyawawan ayyuka kana ya shawarce shi da kada ya nemi zarcewa a zaben 2019.

Tsohon shugaban kasa ya bayyana ra'ayin sa game gwamnatin shugaba Buhari a wata faifan takarda wanda aka fitar ranar talata 23 ga wata janairu 2018.
Cikin takardar mai taken "The Wat Out: A Clarion Call for Coalition for Nigeria Movement", Obasanjo ya bayyana wurare da gwamnatin Buhari ta gagara samun nasara musamman a bangaren kasuwanci.

Yace shugaban yayi aiki ne kasa da yadda jama'a suka yi tsammani bisa ga haka ya dakatar da anniyar sa na zarcewa a zaben 2019.

Tsohon shugaban kasa wanda yayi mulki tsakani 1999 zuwa 2007 yayi kira ga shugaba Buhari da ya zamanto mai bayar da taimako a shugabancin kasar nan gaba domin yin haka zai fi muhimmanci a kasar dama sauran kasashen duniya.

Bugu da kari Obasanjo ya soki shugaban bisa ga akidar nuna fifiko a gwamnatin sa tare da irin dabi'ar rikon-sakai- na ksashi na shugaban ke nuna ga muhimman abubuwa dake wakana a kasar.

Daga karshe Obasanjo yace shugaba Buhari baya da kwakwarar ilimin siyasar kasar kuma bisa ga wannan dalilin ya haifar da rarrabuwar kai a fadin kasar.

JIBWIS Sheikh Bala Lau ya samu mukami a turai

An nada shi a matsayin shugaban ahlus-sunnah na nahiyar turai baki daya

Shugaban kungiyar Izalatul bidia wa ikamatu-sunnah na Nijeriya Sheikh Bala Lau ya samu sabon mukami na zama shugaban ahlus-sunnah a turai.

Bayan gayatar da babba malamin ya karba daga kungiyar Sautus-sunnah na nahiyar turai kwanan baya an ka nada shi a matsayin shugaban ahlus sunnah na nahiyar kasashen turai baki daya.

"Mun yi nazarin kungiyoyi-kungiyoyi na Musulunci da Ahlus Sunnah a duniya, sama da kungiyoyi sittin (60), a kasashe daban-daban. Amma ba mu ga kungiyar da Allah Ya ba nasara cikin takaitaccen lokaci irin wadda Ya ba kungiyar Izala ba" inji jagoran kungiyar sautus-sunnah na kasar turai.

Bisa ga labarin da jaridar Rariya ta fitar, kungiyar sautus-sunnah ta kara gina ma kungiyar Izala ofishi karkkashin cibiyar ta.

Monday, 22 January 2018

Yadda na fara taku a masana'antar Kannywood da kafar dama - Sabuwar jaruma Hajarah Isah

Sabuwar jaruma Hajarah Isah ta fara shirin wasan Hausa da kafar dama

- Jarumar ta haska a wasan Hausa mafi tsada, Gwaska

- Jarumar ta ce tana matukar kaunar tufa

Hajarah Isah, sabuwar jarumar wasan Hausa, na samun karuwar farinjini da daukaka a masana'antar Kannywood bayan rawar da ta taka a shirin wasan kwaikwayon Hausa mafi tsada, Gwaska.


Masu nazarin wasanni masana'antar Kannywood sun tabbatar da cewar ba'a taba kashewa wani shirin fim din Hausa kudi ba kamar yadda aka kashe a shirin wasan Gwaska ba.


Sabuwar jaruma Hajarah Isah
Jaridar Premium Times ta tattauna da jarumar a Abuja. Mun tsakuro maku daga cikin tattaunawar.

An tambayi jarumar yadda ta fara shiri a masana'antar Kannywood da taka rawa a cikin fitaccen shiri kamar Gwaska.

Jarumar, mai shekaru 22 a duniya, ta ce "Gaskiya na yi matukar sa'a da masu shirya fim din Gwaska su ka ga cancanta da dacewa ta a cikin shirin. Shine shirina na farko. Adam Zango ya kashe fiye da miliyan bakwai wajen shirin fim din Gwaska."

Hajarah ta kara da cewar ta fito a cikin shirin a matsayin 'yar sanda, ta nuna gamsuwar ta da matakin da aka dora ta a fim din domin a cewar ta fitowa a shirin Adam Zango ba kankanin abin alfahari ne, kowanne irin mataki mutum ya taka a shirin.

Jarumar ta bayyana cewar babu abinda zai dakatar da ita daga cigaba da fitowa a shirin wasan Hausa, "burina na zama zabin kowanne Furodusa a masana'antar Kannywood tunda ina da karancin shekaru," a cewar Hajarah.

Hajarah ta ce burinta a masana'antar Kannywood ta zama shahararriyar jaruma kamar Jamila Nagudu da Hadiza, jaruman da ta ce su na matukar burge ta.

Hajarah ta ce tafi kaunar tufa a cikin nau'in abinci.

Nura M Inuwa :Wasika Da Manya Mata Albums

Assalamu alaikum warahamatullah yan uwana ma'abota ziyayar wannan shafiba yau nazo muku da labari mai dadi game da sababbin wakokin shahararren mawakin nanaye wato Nura M Inuwa game da ablums dinsa na wannan shekara.
wanda yayi ta baiwa masoyansa hakuri to ku kashe kunnenku kuji daga abinda mawakin a shafinsa na instagram.

"Wasika Da Manya Mata Albums saura kiris".

Kamar yadda kuke gani aiki ya riga ya kawo gaban koshi. 
Saboda haka muna taya wannan mawaki ganin ya fitar da wannan wakoki domin farantawa masoyansa rai.
Ku kasance da hausaloaded.com a ko da yaushe domin nishadantarwa, Fadakarwa, Ilimantarwa da kuma samun ingantattun labari da dadadan kade kade da wake wake.

Kiwon Lafiya: Amfanin Madara Ajikin Fatan Dan Adam

Kiwon Lafiya: Amfanin Madara Ajikin Fatan Dan Adam

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan fili na kwalliya. Madara na dauke da sinadaren da ke saurin gyara fata.

 Yawan bai wa yara madara na dada kaifin basira ga yaro. Bayan haka, shan madara na sanya fata sulbi da laushe da kuma kare fata daga gautsi.

• A sami madara sannan a kwaba ayaba. A zuba ruwan madarar da ayabar ta dan yi kauri kadan sannan a rika shafawa a fuska na tsawon minti goma sha biyar a rana sannan a wanke. Yin hakan na sanya sulbin fuska.

A sami madaran gari sannan a kwaba shi da ruwa sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sannan a gauraya a rika shafawa a fuska kafin a shiga wanka a kullum domin samun hasken fata.

• Madara na goge dukanin daudar fuskar; za a iya samin rabin kofin madara sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke.

Bayan hakan, sai a shafa a fuska da wuya a jira na tsawon minti 2 zuwa 3 kafin a wanke da ruwan dumi.

• Madara na sanya fata sulbi domin hakane ya kamata a rika amfani da shi a matsayin cleanser ; a samo auduga sannan sai a tsoma a cikin madarar ruwa. Sai a rika goge fuskar da ita, sannan sai a jira ta bushe kafin a wanke, yin hakan na rage maikon
fuska kuma da sanya fuska taushi da sulbi.

• Za a iya amfani da madara a gashi domin kara wa gashi lafiya. Musamman lokacin sanyi, gashi .

Sai a zuba madara a gashi ya taba tsagun kai, sai a jira na dan minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.

Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin hakan na hana fashewar fuska saboda sanyi.

Abun ba'a cewa komai Kalli kayan lefen da aka kai wa diyar gwamnan jihar Kano

Fatima Gandyje zata auri dan gwamna jihar Oyo Isiaka Abiola Ajimobi

Garin Kano ta samu manyan baki yayin da surukan gwamnan jihar daga jihar Oyo suka garwaya garin domin bada kayan lefen Fatima Ganduje.


Abu ba'a cewa komai, kayan dai kamar yadda majiya suka shaida mana da tireloli aka sauke su.
Kana an gudanar da wata biki domin karban kayan.
Gwamnan zai aurar da diyar shi Fatima zuwa ga
Idriss Abiola Ajimobi bana

Sunday, 21 January 2018

Wannan sune hotunan jaruma rahama sadau a cikin jirgi da tayi a lokacin da tana bisa hanya zuwa Nigeria

Wannan sune hotunan jaruma rahama sadau a cikin jirgi da tayi a lokacin da tana bisa hanya zuwa Nigeria .
Amma yanxu ta sauka lafiya wanda a can Cyprus ne take karatu a yanzu haka.