Yadda Amurka ta dakatar da Buhari shiga kasarta shekara 15 - NewsHausa NewsHausa: Yadda Amurka ta dakatar da Buhari shiga kasarta shekara 15

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 2 December 2017

Yadda Amurka ta dakatar da Buhari shiga kasarta shekara 15

Kasar Amurka ta dakatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari daga shiga kasar ta har na tsawon shekara 15 saboda zarginsa da takeyi a matsayin mai tsa-tsauran ra’ayin addini inji Atiku

A wata hira da editan jaridar ‘The Boss Newspapers’ , Dele Momodu yayi dashi mista Atiku yace duk da mista Buhari yayi ta musanta zargin amma bai samu sassauci ba.
Atiku yace a shekara ta 2001, Mista Buhari yayi jawabi ga yan kasa a inda ya bayyana cewa musulmi subi tsarin Shara’ar musulunci su zabi musulmi a lokacin zabe wanda hakan ya jawo masa suka daga yan adawa da kasashen waje har takai ga kasar Amurka ta sanya masa takunkumi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yayi wannan tone-tone ne bisa tambayar da dan jaridar yayi masa na cewa meye gaskiyar rade-radin da ake yi cewa a yanzu haka baya iya shiga Amurka saboda tsoron kamu.

Hausa Times ta ruwaito kasar Amurka na zargin mista Atiku da cin hanci da rashawa wanda hakan ya jawo kasar ta sanya masa takunkumi.
Atiku yace yana zuwa sauran kasashen Turai lafiya ba tare da wani kalubale ba kuma yasan duk ranar da yan Nigeria suka zabe shi mulkin Nigeria kasar Amurka zata daga mashi kafa ya rika shiga kasarta kamar yadda ta dagawa Buhari da fraministan Indiya kafa.

Yace da Buhari da farministan Indian, Narendra Modi, duk a da Amurka ta hanasu shiga kasar ta amma yanzu da suka dare kujerar mulki sai gashi ana yi masu tarbar alfarma, inji Atiku
Rahoto Daga:- Premier Times

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment