A lokacin da wasu ke yi wa kuri’ar zabe da cewar kuri’arka ‘yancinka. Shi kuma babba malamin darikan nan Shehu Dahiru Usman Bauchi ya ce tafi kyautuwa a ce ‘kuri’arka wukarka’, Shehu Dahiru Bauchi ya yi kira ga illahirin jama’ar kasa da cewar su tsaya tsayin daka wajen yin amfani da damarsu na zabe domin zabar mutum na gari wanda zai kare musu mutuncin addinsu da kuma kyautata musu rayuwa, a maimakon masu yi musu rufa-rufa da dan wani kaso na kudi su yaudaresu gabanin zabe, daga baya kuma sai lashe baki.
Shehu Dahiru Bauchi ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a birnin Bauchi a cikin bikin maulidin Fiyayyen Halinta Annabi Muhammad (S) wanda ya saba gudanarwa a duk shekara, taron na bana wanda ya gudana a babban sansanin wasanni na tunawa da Abubakar Tafawa Balewa Sitaduyum da ke tsakiyar Bauchi a shekaran jiya alhamis.
Shehun yake cewa “kuri’arka wukarka, ko ka zabi mutumin da zai yanka ka ne ko kuma ka zabi wanda zai kareka. Don haka, ina kira ga jama’a da su tabbatar da zabin mutum na gari wanda zai kare maka addininka ba mai yakar maka addini ba”.
Yake cewa, “wasu mutanen suna cewa kuri’arka ‘yancin ka, eh na yarda hakan ne, amma ni a waje na kuri’arka kamar wukace mai kaifi a gareka, walau ka yi amfani da wannan wukar taka mai kafi wajen zaben shugaban da zai yanka ka ko kuma ka zabi wanda zai daukaka ka”. In ji shi.
Ya ce wasu daga cikin ‘yan siyasan sukan zo da suffa mai kyau a lokacin da suke neman a zabesu, amma da zarar suka dale bisa karagar mulki kuma labarin sai ya zo ya sha banban “don haka ina kiramu mu hada kai dukkaninmu mu zabi mutumin da zai daukaka mana darajar addininmu”. ta bakinsa.
Malamin Darikar Tijjaniyya, da ya juna kan muhimmancin maulidi kuwa, ya bayyana cewar Manzon Allah rahama ne ga talikai ya kuma zo da hadin kai da kuma rahama ga dukkanin talikan bayi, a duk haka ne suke gudanar da maulidin domin koyi da halayen Manzon Allah na zaman lafiya, salama, kyautatawa, sadaka da kuma sauransu. Ya ce, a wajen maulidi ne suke samun irin wadannan halayen kwarai domin yin koyi da su.
Shehu Dahiru ya ce, suna gudanar da wannan maulidin ne domin nuna godiya wa Allah a bisa wannan babar kyautar da ya yi wa talikai na aiko musu da shiriya a cikinsu.
Rahoto:- Leadership a yau
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment