Bisa ga rahoton da BBChausa ta ruwaito, farfesan yace rawan maimaita jarumai a fina-finai hausa na Kannywood na gundarar yan kallo. Farfesan wanda ke koyar da darasi a kan yadda ake tsara fina-finai a jami’ar Ado Bayero dake Kano yace bai kamata nuna basira da baiwa su takaita a wajen wasu tsirarrun jarumai ba.
A cewar sa, matukar ba’a ba sabbin fuskoki damar nuna basirar su ta yaya masana’antar zata samu bunkasa. Wasu daga cikin masu shirya fina-finai a dandalin kannywood na da ra’ayin cewa yawanci fina-finai basu samun kasuwa idan masu kallo suka gan bakuwar fuska a matsayin jarumi. Da hakan Abdullahi Adamu yayi la’akari da masu shirya fina-finai a Amurka na Hollywood inda yace ya kamata a ba wasu dama suma su bada gudumawar su wajen nuna bajirtan su a harkan.
"Ka dauki kowanne jarumin Hollywood, babban jarumin Hollywood, kamar a ce Bruce Willis ko Arnold Schwarzenegger ko wani daban, za ka ga fim din sa da ya yi shi kadai ne ya fito."
"Kowa Allah ya ba shi basirarsa saboda haka sai an gwada wadansu, idan kuma ba a gwada din ba, to ba za a samu nasara ba” . Yace. Abdullahi Adamu yana ganin cewa yiwuwar haka shine mafi yawanci tsirarrun jaruman suke shirya abubuwansu da kansu. Yace indai ana samun masu shirya fina-finai daga wajen kannywood da sun rinka baiwa sabbin fuskoki dama domin cigaban harkar. A karshe dai manazarcin fina-finai ya bayyana cewa jami’arsa tana kokarin fara kwas a kan harkar shirya fina-finai domin bukasa fannin a kasa.
Kannywood:-Kalli Hotunan Bukin Auren Sarkin Waka Nazir Ahmad
Aminu SairaMai shirya fina-finai Hausa na Kannywood ya samu karuwa
Kannywood :- Fitattun Fina-finai Hausa 5 da ya kamata ku kalla
'Yan Fim Sun Taimakawa Malam Waragis Daidai Gwargwado,furodusa Inji Usman Mu'azu
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment