Qur'ani na da harrufa 323,015
.
Qur'ani na da Juzi'i 30
.Qur'ani na da Hizbi 60
.Qur'ani na da rubu'i 240
.Qur'ani na da ushuri 480
.Qur'ani na da aya 6666
.Surorin Makkah 85
.Surorin Madinah 29
.Surarin da suka fara da 'Alhamdu' guda 5
.Surorin da suka fara da Tasbihi guda 6
.Surorin da suka fara da harrufa guda 19
.Guraren Sujjada a Qur'ani guda 15
.Farkon wanda ya fara bayyana karatun Qur'ani cikin Sahabbai a Makkah shi ne Abdullahi bn Mas'ud
Kalma mafi tsayi a cikin Qur'ani ita ce 'Fa'asqainaakum uhu' ta na da harrufa 11 a rubutun ta na larabci.
.
Qira'ar da tafi shahara wajen karatun Qur'ani ita ce ruwayar Hafs daga Aasim. Hafs ya bar duniya a shekara ta 180 H, Asim kuma 127H
.
Tsuntsaye da aka ambaci sunayen su a Qur'ani;
=> Alba'ubh
=> As Salwa
=> Al Guraab
=> Al Jarad
=> An Nahl
=> Al Hudhuda
=> Az Zubab
.
Sahabin da aka ambaci sunan sa a Qur'ani Zaidu bn Thabit a cikin Suratu Ahzab
.
Rabe-raben Qur'ani ; akwai Surori masu suna;
*As Saba'ud Diwaal- sune Bakara, Aali Imran, Nisa'i, Ma'ida, A'araf, An'am, Yunus. Su 7 ne, su suka fi tsayi.
*Akwai Almi'aini; daga bayan Yunus zuwa Surorin da suka
kai ayoyi 100 ko kusa da haka
*Almathani
*Almufassal su ne kananan surori daga 'Qaaf' ko 'Hujrat'
.
Surah mafi girma ita ce Suratu Fatiha
.
Aya mafi girma ita ce Ayatul Kursiyyu
.
Shugaban masu Tafsirin Qur'ani shi ne Imamud Dabariy
.
Annabin da aka fi ambaton sunan sa a Qur'ani shi ne Annabi Musa (AS) sau 136
.
Sura ta karshen sauka cikin Qur'ani ita ce suratun Nasr (Iza ja'a)
.
Aya ta karshen sauka a Qur'ani ita ce aya ta 281 a cikin Bakara (Wattaquu yauman) a magana mafi inganci
.
Surorin da aka ambace su da sunan dabbobi;
=> Baqara-Saniya
=> Namli-Tururuwa
=> Ankabut-Gizo Gizo
=> Nahli-Qudan Zuma
=> Fiyl-Giwa
.
Surorin da aka ambace su da sunayen Annabawa;
=> Suratu Yusuf
=> Suratu Hud
=> Suratu Ibrahim
=> Suratu Muhammad
=> Suratu Nuh
=> Suratu Yunus
.
Surorin da aka ambace su da sunayen su taurari;
=> Suratut Najm
=> Suratul Qamar
=> Suratud Dariq
=> Suratush Shams
=> Suratul Buruj
.
Surorin da aka ambace su da sunayen lokuta;
=> Suratul Fajr
=>Suratul Laili
=>Suratud Dhuha
=> Suratul Asr
.
Dabbobin da aka ambace su cikin Qur'ani;
=> Baqara Saniya
=> Ba'ubha Kwarkwata
=>Zubaab Quda
=>Namli Tururuwa
=>Hudhuda tsuntsu
=>Naaqah Raquma
=>Khail Doki
=>Bighaal Alfadari
=> Himar Jaki
=>Qusuurah Zaki
=> Jaraad Fari
=>Zi'b Kerkeci
=> Kalb Kare
=> Guraab Hankaka
=> Fiyl Giwa
=>Ankabuut Gizo Gizo
=> Nahl Zuma
=>Su'ban
=> Ibil Rakumi
.
Sunayen Mala'iku da ya zo cikin Qur'ani;
=> Jibril
=> Miika'iil
=>Maalik
=>Haruut
=>Maarut
.
Daular da aka ambace ta cikin Qur'ani ita ce daular Rumawa-Ruum
.
Qabilar da aka ambace ta a cikin Qur'ani ita ce kabilar Quraishawa-Quraish
.
Littattafan Tafsiri da suka fi shahara
=> Tafsirud Dabari
=> Tafsiru Ibn Katheer
=>Tafsiru Ruhul Ma'ani-Aluusiy
=>Tafsirul Qurdabi
=>Tafsiru Mafaatihul Gaib
.
Gurare 4 sunan Annabin mu Muhammad (SAW) ya zo a cikin Qur'ani;
=>Aali Imran aya ta 144
=>Ahzab aya ta 40
=> Muhammad aya ta 2
=> Fathi aya ta 29.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment