February 2018 - NewsHausa NewsHausa: February 2018

Pages

LATEST POSTS

Tuesday, 27 February 2018

Labari Mai Dadi : Gwamnatin tarayya ta fadi lokacin da zata fara biyan sabon tsarin albashi

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da zuwa karshen watan Satumba na wannan shekarar a matsayin lokacin da za ta fara biyan sabon tsarin albashi ga ma'aikatan ta a dukkan fadin kasar nan.

Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin bayanin maraba da babban ministan kwadago da samar da aikin yi na kasar Sanata Chris Ngige ya yi jiya Litinin lokacin da yake jawabi a lokacin bikin cikar kungiyar kwadago ta kasa shekara arba'in da kafuwa.

Ministan ya bayyana cewa tuni har shire-shiren tabbatar da sabon tsarin albashin yayi nisa saboda a cewar sa, wannan gwamnatin da kuma shugaba Buhari suna da matukar tausayin ma'aikatan kasar.

A wani labarin kuma, Fadar shugaban kasar Najeriya dake a unguwar Villa, babban birnin tarayya Abuja ta bayyana a jiya cewa su fa su shugaba Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo batun zarcewa bisa mulki a zaben 2019 ma bai dame su ba.

A maimakon hakan, kamar yadda muka samu daga fadar, an bayyana cewa su shugabannin kawo yanzu ba abun da ke a ran su irin tabbatar da samun cigaba mai dorewa a kasar tare kuma da jin dadin 'yan Najeriya.

Ba Za Mu Canja Ranar Zaben Shugaban Kasa Ba — INEC




Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta jaddada cewa ba za ta canja ranar zaben Shugaban kasa ba kamar yadda majalisar tarayya ta nema a garambawul da ta yi wa dokokin zabe.

A bisa jadawalin zaben 2019 da hukumar INEC ta fitar a ranar 9 ga watan Janairu, ta tsara gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar tarayya a ranar 16 ga watan Fabrairu na 2019 sai na gwamnoni da majalisunsu wanda za a yi a ranar 2 ga watan Maris amma kuma a gyaran da majalisar tarayya ta yi wa dokokin zabe, ta mayar da zaben Shugaban kasa ya zama na karshe.

Ba za a Mu yi Amfani da Fasahar Alkalanci Ba a Turai- Ceferin

Hukumar Kwallon Kafar nahiyar Turai ta ce, ba za ta yi amfani da fasahar bidiyon da ke taimaka wa alkalin wasa a kakar gasar zakarun Turai mai zuwa ba saboda tarin rudanin da ke tattare da fasahar kamar yadda shugaban hukumar, Aleksander Ceferin ya bayyana.

Ceferin ya ce, kawo yanzu babu wanda ke da cikakkiyar masaniya kan yadda fasahar ke aiki saboda rudanin da ke cikinta.
Ceferin ya kara da cewa, lallai wannan fasahar tana da kyau amma kar a yi garajen fara amfani da ita.

Kalamansa na zuwa ne a yayin da da Kwamitin Kwallon Kafa na kasa da kasa ya gudanar da wani taro a ranar Asabar don yanke shawara game da amincewa da fasahar kafin aiki da ita a gasar cin kofin duniya a Rasha a bana.
An dai yi amfani da fasahar a wasu kasahe kamar Ingila a gasar firimiya da Carabao da kuma Jamus a gasar Bundesliga, sai kuma Italiya a gasar Serie A.

Rauni zai hana Neymar Da Silva karawa da Ronaldo na Madrid

Ga alama gwarzon dan wasan PSG, wato Neymar De Silva ba zai samu damar buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Real Madrid ba a gasar cin kofin zakarun Turai, matakin kungiyoyi 16 zagaye na biyu saboda raunin da ya samu a kafarsa kamar yadda binciken likitoci ya tabbatar.

Neyma mai shekaru 26 kuma dan asalin kasar Brazil ya gamu da raunin ne a fafatawar da PSG ta doke Marseille da 3-0 a ranar Lahadi a gasar Lig 1 ta Faransa, lamarin da ya sa aka cincibe shi akan gadon daukan mara lafiya cikin hawaye.
Sai dai kawo yanzu, PSG ba ta tabbatar da tsawon kwanakin da zai yi na jinya ba.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi fatan warkewar Neymar cikin hanzari don samun damar fafatawa da ‘yan wasansa da suka hada da Christiano Ronaldo.
PSG ta siyi dan wasan ne daga Barcelona akan farashin Pam miliyan 200 a cikin watan Agustan bara, in da ya ci ma ta kwallaye 29 cikin wasanni 30.

Monday, 26 February 2018

MUSIC : Sabuwar wakar Aminu Dumbulum - Tashi Barci Kasa

WATA SABUWAR WAKAR AMINU DUMBULUM MAI SUNA

 "TASHI BARCI KASA"

A wannan wakar ya caccaki Dr Abdullahi ganduje sosai ya nuna cewa ba'a mulkin kano ana barci yayi kalamai sosai akan yadda gamnatinsa ke tafiya a jahar kano.

Wannan mawakin dai mawakin kwankwaso ne wanda ya nuna amanar kwankwaso amma ganduje ya nuna shi butulu ne.

Ga Wakar nan sai ku latsa domin sauraren wannan wakar.


Download music here

Sunday, 25 February 2018

Sharhin Fina Finai : Sharhin fim Din Sa'eed

Suna: Sa’eed

Tsara labari: Muhammad Sardauna

Furodusa: Sani Shu’aibu

Bada umarni: Muhammad Sardauna

Kamfani: D. Skuare investment Nig. Ltd & Dogon Yaro Movietone

Jarumai: Sadik Sani Sadik, Sulaiman Bosho, Aisha Aliyu Tsamiya, Musa Kalla, Ladidi Tubless, da Balarabe Jaji.

A farkon fim din an nuna Alhaji Buba (Sulaiman Bosho) da yaronsa Kalla suna magana akan wata yarinya da yakeso acikin kauyensu Kadija (Aisha Tsamiya) ‘yar gidan Malam Ladan wadda ita yarinyar ma batasan yana yi ba, yana fadawa Kalla cewar tunda yana da dukiya zai nuna karfin dukiyarsa ko da komai nasa zai kare gurin ganin ya mallaki yarinyar.
An nuna gidansu Kadija suna tsananin soyyaya tare da dan kanin mahaifinta Sa’id (Sadi Sani Sadik) an nuna yanda suke tsananin kaunar junansu kuma mahaifansu an nuna masu zumunci ne kuma suna son kulla alakar auren Kadija da Sa’id amma kuma a gefe guda iyayen su Kadija suna matukar ganin mutuncin Alhaji Buba saboda yanda yake taimakonsu da dukiyarsa domin duk su basu fahimci kudirinsa na kaunar Kadija ne yasa yake yi musu wannan taimakon ba, da Alhaji Buba ya kai wa Kadija kokon barar soyyayarsa yaga abun bazaiyu ba domin hankalin Kadija baya kansa sai ya hada baki da wani abokin Sa’id Alhaji Buba ya tura Sa’id birni kasuwanci domin ya sami damar aure Kadija shi Sa’id bai san dawar garin ba hakan tasa ya fara murna da kuma shirin tafiyarsa birni iyayensa ma suka taya shi murna sosai suka yi masa addu’a da fatan alkairi masoyiyarsa Kadija ce kawai bata son tafiyar Sa’id birni saboda batason rabuwa da shi amma a hakan Sa’id ya lallavata ya bata baki ya kama hanya ya tafi birni neman kudi kamar yanda Alhaji Buba ya tura shi.

Bayan tafiyar Sa’id Alhaji Buba ya sami damar vullowa da Malam Ladan da Malam Sunusi iyeyen su Sa’id maganar aurensa da Kadija dukkansu babu wanda ya bashi goyon baya saboda zumuncin da suke son kullawa tsakanin Kadija da Sa’id ganin haka Alhaji Buba ya saka yaransa cikin dare suka je suka kakkashe Kaf iyayensu Sa’id har iyayensu mata basu tsira ba itama Kadija da kyar ta samu ta tsira ta fice tabar garin ta sauka a gidan wani mutumi ya taimaketa ya riketa. bayan Sa’id yadawo daga birni ya tarar da abunda ya faru ya shiga cikin matsanancin tashin hankali na rashin iyayensa da kuma masoyiyarsa don shi duk a zatonsa ma itama Kadijar ta rasu kuma shi duk baisan Alhaji Buba ne ya kullamasa duk wannan makircin ba, shi kuwa Alhaji Buba tunda abun ya faru ciwo ya dirarar masa ya fara jinya sannan duk dukiyar daya mallaka masifa ta afkamata ta kare shi kuwa Sa’id kasuwanci ya havaka ya zama babban mai arziki har Allah ya hadashi da Kadija a hanya ya dawo da ita gida aka daura musu aure shi kuwa Alhaji Buba asirinsa ya tonu cewar shi ya kashe iyayen su Sa’id sanadin dawowar Kadija hakan tasa Sa’id ya saka hukuma ta kama Alhaji Buba da duk yaransa su Kalla.

Abubuwan Birgewa:

1-Jaruman sun yi kokari gurin isar da sakon.
2- An nuna illar zalunci da son zuciya
3- An nuna muhimmancin karfafa zumunci tsakanin ‘yan uwa.

Kurakurai:

1- sauti da camera basu fita yanda yakamata ba a fim din.
2- Shin garin babu shugabancine? anata maganar hakimi amma ba’a tava nunoshi ba duk da tavargazar da aka yi a garin yaci ace maganar ta je gaban hakimi.
3- shin Alhaji Buba ba shida gida ne wanda yake zaune da iyalansa? duk irin arzikinsa da ake fada amma kullum sai dai a ganshi a waje.

4-akwai gurinda Alhaji Buba yake zuwa da kujera ya zauna a kofar gidansu Kadija har iyayenta suke futowa su ganshi a matsayin Alhaji Buba na maikudi kuma cikakken mutum baikamata ace yana yawo da kujera a hannunsa da kansa ba.
5- A matsayin mahaifiyar Kadija na matar aure bai kamata ace ta dauki filo ta danne wuyan Kalla a kofar gida ba.

6-Akwai gurinda Kadija take futowa zance gurin Alhaji Buba a matsayinta na wadda batasonsa kuma iyayenta basa goyon bayan sonda yake yi mata yaya akayi Kadija ta fito? da kuma izinin wa? ko dama abunda suke fada duk ba haka bane?

7-Lokacin da Kadija tabar gida a gigice kuma kawai mai kallo sai ganta a wani gida mai gidan ya taimaketa kuma ana maganar bama a garin bane ba’a nuna ta yaya akayi ta tsira ba sannan da wana kudin motar tabar garin ita da ta fito cikin dare babu shiri.
8-shin duk su Malam Ladan basu da kowa ne ‘yan uwa ko abokan arziki kuma cikin gari irin wannan a wayi gari an kashe har mutum hudu amma babu wani mataki da aka dauka a hukumance?

9- shin Sa’id ba shida kowa ne daga shi sai aboki yake rayuwa? kuma wacce sana’a yake yi a birni da har ya yi wannan arzikin lokaci daya?
10- Akwai gurin da Sa’id yake haduwa da Kadija akan titi ita da wadda suka taimaka mata bayan ya fidda ran ta mutu daga nan kuma aka gansu a wurin wani shakatawa amma ba tare da wacce ya gansu tare ba shin ita wacce suke taren komawa gida ta yi? idan kuma daga baya ne ya kamata ace an nuno su tare da wanda ya taimaki Kadija saboda taimakon da ya yi musu.

Karkarewa:


Labarin fim din ya yi kyau amma akwai abubuwan da akayi yi su a dunkule ya kamata ace an bayyanawa mai kallo su sannan an takaita abubuwa dayawa. Wallahu a’alamu!

Akan Naira Dudu Bari Biyu Basu Sanya Ayi Lalata Dani Inji Maryam Both

Wani bawan Allah me suna Muhammad Usman ya turawa tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth sako inda yake rokonta cewa tazo suyi holewar hutun karshen mako tare a Abuja, yayi alkawarin cewa zai baka tsabar kudi naira dubu dari biyu idan ta yarda.

Saidai Maryam ta mayarwa da Muhammad martanin cewa dubu dari biyu ba komai bane a gurinta, ta kara da cewa idan ma yana son dubu dari biyu to ya aiko mata da lambar ajiyar bankinshi zata bashi domin shine matsiyaci, ita ba matsiyaciya bace.

Maryam dai ta kara da cewa tana kashe dubu dari biyun da yake tun kahon zai batane wajan sayan katin waya da alewa, dan ma kar yayi tunanin wai wata tsiyane a gurinta. Tace kai koda miliyan dari biyu yace zai bata ba zata yarda ba domin bata ganin girman mutane irinshi.

Maryam ta kara da cewa daga ji shi wannan Muhammad din sabon shigan wannan harkane, inda tace koda yake tarbiyya daga gida take farawa, babanshi ma haka yake shiyasa shima yayi gado, a karshe tace yaje ya nemi na kan titi domin jikinta da lokacin ta bana sayarwa bane, tana da aikinta, tana neman kudinta kuma tana alfahari da hakan.
A karshe ta kira Muhammad da matsiyaci inda tace watau shi gashi dan gidan masu kudin Duniya(zai nuna mata kudi), taso ace gaba da gaba ya gaya mata wannan magana da yasha mari.

Saturday, 24 February 2018

Sanata kwankwaso Yayi Bayyanin Yadda Mulki Buhari ke Tafiya

A wata ganawa da manema labarai na jaridar The Cable, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta na iyaka bakin kokarin ta wajen jagorantar kasar nan.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yayin tofa albarkacin bakin sa bayan da manema labarai suka tuntube sa dangane da yanayin shugabancin jam'iyyar APC.


Sai dai sanatan yana fatan cewa, gwamnatin zata kara hazaka kan hobbasan da ta yi a baya cikin shekarau uku da suka gabata, domin mutanen kirki na kasar nan su dugunzuma wajen kadawa jam'iyyar kuri'un su a zaben 2019.


Kwankwaso yake cewa, wannan shekarar ta karshe da ta yiwa jam'iyyar APC saura tana da matukar muhimmanci.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa, har yanzu bai yanke shawarar neman takarar wata kujera a zaben 2019, kuma baya da ra'ayin sauya sheka daga jam'iyyar su ta APC.

Sunayen 'Yan Matan Makarantar Dapchi Da Ake Zargen Boko Haram Suka Arce Da Su


1.Fatima Bashir
2. Aisha Kachalla
3. Zainab Abubakar
4. Falmata Wakil
5. Fatima Isa
6. Fatima Musa
7. Aisha Usman
8. Aisha Adamu
9. Fatima Isa
10. Hauwa A. Mohammed Idriss
11. Maryam Mohammed
12. Fatima Mohammed II
13. Hauwa Salisu
14. Hassana Gambo
15. Aisha Adamu
16. Adama Garba
17. Zara Grema
18. Maryam Daamkontoma
19. Zainab Bama
20. Fatsuma Abdullahi
21. Fatima Yahaya Tarbutu
22. Amina Yahaya Tarbutu
23. Amina Adamu
24. Hajara Ali
25. Fatima Abdullahi
26. Fatsuma Ali
27. Zara’U Mohammed
28. Salamatu Garba
29. Falmata Alh. Inuwa
30. Falmata Alh. Ali
31. Aisha B. Danjuma
32. Maryam Bashir
33. Maryam Aliyu Mabu
34. Fatima Modu Bamba
35. Aisha Modu Bamba
36. Hafsat Haruna
37. Rabi Alh. Nasiru
38. Hadiza Moh’D
39. Fatima Aji Hassan
40. Falmata Wakil
41. Aisha Wakil
42. Falmata A. Audu
43. Aisha Maina
44. Aisha Mohammed
45. Aisha Mamuda
46. Name missing on list
47.Zainab Usman
48. Hadiza Mohammed Taiduma
49. Maryam Ibrahim
50. Fatima M. Gira
51. Hafsat Ibrahim Gira
52. Maryam Ibrahim
53. Zara Tijjani
54. Amina Haruna
55. Fatima Adamu
56. Khadija Mai Sale
57. Khadija Ali
58. Habiba Musa Jakana
59 Fatima Bukar
60. Hajara Gidado
61. Maryam Basiru
62. Fatima Usman
63. Maryam Ibrahim
64. Leah Sherubu
65. Aisha Alh. Deri
66. Fatima Hassan Mustapha
67. Zainab Manu
68. Zara Tijjani
69. Zainab Bukar Abba
70. Hauwa Saidu Abubakar
71. Karima Inusa
72. Amina A. Abubakar
73. Yakura Sani
74. Rabi Yahaya Tela
75. Hajara Yahaya Tela
76. Marya Mustapha
77. Aisha Abdullahi
78. Maryam Adamu Mohammed
79. Bintu Usman
80. Fatsuma Mohammed
81. Salamatu Isiyaku
82. Hauwa Lawan
83. Aisha B. Danjuma
84. Aisha Moh’D Jakusko
85. Hauwa Bulama
86. Fatima Abubakar Jambo
87. Walida Adamu
88. Fanna Mohammed
89. Aisha M. Bukar
90. Maryam Usman
91. Aisha Abba Aji
92. Maryam Usman
93. Maimuna A. Hassan
94. Zara Musa
95. Maryam Mohammed Kaku
96. Khadija Suleiman
97. Habiba Nuhu Dan Inu
98. Fatima Isiyaku Aliyu
99. Sahura Jibir Mohammed
100. Khadija Grema Dabuwa
101. Zara Grema Dabuwa
102. Zara Mohammed Lawan.
103. Fatima Muhammad.
104. Fati Modu Aisami.
105. Fatsuma Ali.

MAJIYA: Rariya

Ana Rikici Tsakanin Mourinho Da Paul Pogba A Filin Daukar Horo

Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho da dan wasan kungiyar, Paul Pogba sunyi rikici a lokacin da kungiyar take daukar horo a filin daukar horon kungiyar bayan da Pogba yayi zargin cewa Mourinho yana kallonsa a matsayin wanda yasa kungiyar bata kokari.

Hakan yasamo asaline sakamakon halin da kungiyar ta shiga na rashin lashe wasanni a yan kwanakin nan bayan da kungiyar ta lashe wasanni biyu kacal cikin wasanni biyar da kungiyar ta buga.

Sau biyu Mourinho yana cire Pogba acikin wasannin da kungiyar ta buga sannan kuma sau uku yana ajiyeshi a benci wanda hakan yasa aka fara rade radin cewa akwai matsala a tsakanin mutanen guda biyu.

Wasu rahotannin sun bayyana cewa Mourinho yana zargin Pogba bias zakewa da yake wajen shiga aikin mai koyarwa abinda kuma Mourinho bayason.

Sannan an kuma bayyana cewa Mourinho yana gayawa dan wasan bakar Magana agaban ragowar yan wasan kungiyar wanda kuma Pogba yake ganin kamar yana wulakantashi.
Tuni aka fara rade radin cewa Pogba yafara tunanin barin kungiyar bayan daya bukaci wakilinsa daya fara neman kungiyar da zata siyeshi domin yana son barin kungiyar a karshen kaka mai zuwa.

Mece Ce Makomar Rahama Sadau A Kannywood?

Daga Sani Tahir Kano
Ga duk mai bibiyar masan’antar shirya fina-finan Hausa wato (Kannywood), ya kwana da sanin tirka-tirkar da ta ki ci ta ki cinyewa a game da shugabannin kungiyar MOPPAN da fitacciyar jaruma Rahama Sadau, tun kusan bara aka kore ta daga masana’antar, saboda laifin fitowa bidiyon wata waka wadda ta sabada al’adar malam Bahaushe da addinishi.

Korar ko dakatarwa da ta janyo rabuwar kan wasu mutane da dama, wadansu suna ganin a yi mata afuwa, wadansu kuma suna ganin kada a yi mata afuwa. Saboda a ganinsu ta karya doka. Ana cikin haka aka ji ta a wata kafar sadrwa tana mai nuna nadama da abin da tayi, inda ta neme gafarar gwamnan jihar Kano (Dr. Abdullahi Umar Ganduje da mai martaba sarkin Kano Mal. Muhammad Sunusi da al’ummar Kano da sauran ’yan Arewa.

A nan fa wadanda suka dage a kan sai ta rubuta takardar neman yafiya daga kungiya ta yi, kuma kwatsam tafiya ta kama ta zuwa tallar jirgin sama, bayan ta dawo ne su kuma kungiyar masu shiryawa wato (KAPAN). Suke ganin laifin shugaban hukuamr tace fina-finai da dabi’a Fahallahu bisa fadar cewa, zai ci gaba da duba fina-finai da jarumar ta futo inda suke ganin bai dace ba. Ko ma dai mene ne ya kamata a duba ke nan Rahama sadau. 

Dalili kuwa shi ne duk wanda ya yi laifi har ya fitoya nuna nadamar laifin da ya yi, ya kamata ai mai afuwa, don na san duk kusan nasarar da ta samu a rayuwarta dalilin harkar fim ce.

Ya kamata ita ma Rahama ta sake rubuta wa kwaminitin ladabtarwa, don durkusuwa wada ba gajiyawa ba ne. Na san mutane da dama suna yi wa kwamitin kallon kwamitin adalci. Wasu kuma suna ganin ai ko kadan ba za su yi adalci ba, suma ya kamata kungyar (KAPAN) dalilinsu duniya ta san Rahama Sadau har ake ba ta aiki, saboda irin kokarin da takeyi.

Ayuba Muhammad Danzaki a ra’ayinshi kuma a matsayinshi na marubucin fim, yana ganin bai dace a kore ta ba “Da an jawo ta jiki sai a yi mata nasiha ba wai a kore ta ba. Dalili kuwa in har an kore ta sai ta je ta yi abin da ya fi wannan, in ji shi.

Za a fafata karo Na 179 Tsakanin Man United da Chelsea

A ranar lahadin karshen makon nan ne za ayi zazzafar karawa tsakanin Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da takwararta Chelsea karkashin gasar Firimiya da ke ci gaba da gudana. Wasan dai shi ne karo na 179 da kungiyoyin biyu za su kara tsakaninsu.

Manchester United ce dai ta lallasa Chealsea sau 76 yayin da suka yi canjaras a wasa 49 sai kuma wasanni 53 da ita Manchester ta sha kaye a hannun Chelsea.

Kawo yanzu dai Manchester United din ita ke a matsayi na biyu a teburin Firimiya da maki 56 banbancin maki 3 tsakaninta da Chelsea wadda ke a matsayi na hudu.

Friday, 23 February 2018

Kalli zafaffan hotunan Jaruma Fati washa wani salon sai manya

Wannan wani sabon salo ne da anka fito da shi na daukar hotuna



Kalli Yanayin Da Rahama Sadau Ta Fito a Sabbin Hotuna

Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood wacce aka dakatar, Rahma Sadau ta bayyana a wasu sababbin hotuna.

Rahma ta dauki hotunan ne dauke da kwaliyyae zamani sannan kuma ba tare da ta sanya mayafi ko kallabi wajen rufe suman kanta ba.

Hakan ya ja hankulan mutane da dama a shafukan zumunta inda sukayi kira ga jarumar kan ta dunga rufe gashin kanta musamman a matsayinta na Bahaushiya kuma Musulma.

Kamar yadda kuka sani Musulunci ya koyar da cewa mace ta dunga killace duk ilahirin jikinta domin ko ina na jikin mace al’aura ne zai dai fuskanta da tafukan hannayenta.

Ga hotunan jarumar da ya ja hankali jama’a a kasa:

Sadau, ta bayyana a ranar Asabar din da ta gabata cewar, ta soma shiga matsalolin rayuwa ne tun bayan da ta fara fitowa a shire-shiren fina-finan kudancin kasar nan ta Najeriya da aka fi sani da Nollywood.

Thursday, 22 February 2018

Tuna Baya Matan Kannywood Da Suka Nishadantar Da Al'umma Shekarun Baya


Masana'antar Kannywood ta kai kusan shekara 20 da kafuwa kuma ta samu dinbim jarumai masu taka muhimmin rawa wajen nishadantar da al'umma.
A cikin tsawon shekarun da wannan dandalin ta samu asali an samu jarumai mata da dama da suka faranta mana rai da ire-iren rawar da suke takawa a idon telibijin.

Mafi yawancinsu a daina jin duriar su ne kasancewa shiga sahun gaba na rayuwar zamantakewar aure.

Domin martaba da raya wannan dandalin da take nishadantar damu a ko da yaushe bari mu waiwaya baya mu tuna wasu daga cikin tsofin jarumai mata gwarzaye da suka nishadantar damu shekarun baya kafin ire-iren su Hadiza Gabon da Rahama Sadau su amshi tutar raya masana'antar, 

Saima muhammad 
Saima muhammad tsohuwar jarumar masana'antar kannywood 
Abida muhammad 
Abida muhammad tsohuwar jarumar kannywood
Fati muhammad tsohuwar jaruma
kafin shigowar wasu jarumai mata da ake damawa dasu a yanzu a wannan farfajiyar an samu wasu da dama wadanda har yanzu ,masoya da masu bibiyar fina-finai hausa suna kewar su.

Sadiya Gyale 
Sadiya Gyale




Safiya musa

Safiya musa Albarka Aure Tare da Danta


Samira Ahmad 


Muhibbat abdulsalam

Albarkar aure tare da 'ya'yanta

Mansura isah tare Albarkacin aurenta 



Hafsat shehu ta farida jalal


Rukayya dawayya



Wadannan sun tare da wasu da dama sun taka rawar gaske yayin da ake damawa dasu a harkar fim kuma sun taimaka wajen inganta ki'imar al'adar arewa ga bainar jama'a.

Muna musu fatan alheri tare da jinjina masu bisa gudummawar da suka bada a masana'antar kannywood.

Source : naij.com








AUDIO : Falalar Boye Fushi Daga Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Kano


Manzon Allah s.w.a Yana cewa duk wanda yake da damar nuna fushi amma boye  fushi a gobe kiyama Allah zai sashi aljannah yace zabi  wanda kake so a cikin Hurul'ini

Boye fushi kamar sadaki ne na hurul'ini a gobe kiyama.


Manzon Allah yasan abu ne mai matukar wuya mutum yana da damar nuna fushi amma hadiye shi saboda abu ne  mai matukar kuna a wajen hadiyewa balanata yanzu mutum na neman zalunci su kadai balanta an tabashi.

Kaji kamar baka ji ba, ka gani kamar baka gani ba lallai abu ne mai samama mutum daraja a gobe kiyama.

Babu masu boye wannan boye fushi sai masu hakuri da imani.

Ga Audion nan domin saurare

Download Audio here

Tuesday, 20 February 2018

Zaman Aure Ya Fiye Mun Kudin Da Zan Samu Da Ma Komai Da Komai - Inji jaruma Hannatu Bashir

Jarumar tana daya daga cikin yan matan masana'antar Kannywood da zasu ajiye yin fim da zaran sunyi aure domin mayar da hankali wajen kula da iyali

Hirar ta da wakilin BBC Hannatu tana mai cewa Ko wace mace tana son ta ganta a gidanta kuma tana kula da iyalen ta. Idan ina da mijin yanzu idan nayi aure, ka gan zan fita da safe zuwa wajen aiki wa zai kula dashi? Idan kuma na fara tara yaya wa zai kula mun dasu?.

Ka gan ya zama dole in hakura da daya. Kuma harkar fim dinmu ba a iya kano kadai muke yi muna iya zuwa wasu garuruwa muyi.

Ina da miji zai barni in tafi wani gari inje inyi kwana biyar zuwa goma wajen daukar fim? kaga abu ne mai kamar wuya.

"Ni daia zaman aure ya fiye mun kudin da zan samu kuma ya fiye mun komai da komai ma".

Hannatu wanda ta kwashi sama da shekara bakwai a dandalin nishadantarwa tayi karin haske game da zargin da ake yawan yi ma yan fim na cewa su yan iska ne.

A cewar ta mafi yawanci mata dake aikata hakan bata-gari ne wadanda suke fakewa da cewa su yan fim ne.

Tace mafi yawanci katin bogi suke yawo dashi da yin karya cewa su yan fim ne domin idan aka bibiya sau da dama  jaruman basu san da zaman su ba a masana'antar.

Tace irin hakan yana faruwa sosai kuma mafi yawanci ire-iren yan matan da zarar an kama su sai su fake da cewa suna fim tare da nuna katin shaida na karya.


Jarumar wanda ta shirya shirin Sarauniya, Kukan Kurciya da Mairo da dai wasu fina-finai daban tace yin fim sana'a ce kamar sauran sana'o'i kuma yadda ma'aikata ke zuwa masana'antar su haka suma ke zuwa daban farfajiyar su.

Akalla fina-finai hamsin ta fito a ciki cikin tsawon shekara bakwai da tayi a dandalin nishadantarwa ta kannywood.

AUDIO: SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI Yayi Kakkausan Suka Ga Gwamnatin Buhari


Wannan wata Budaddiyar  Wasika ce zuwa ga Shugaban Kasa Buhari da Antoni Janar na Najeriya Abubakar Malami. Daga Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a yau juma'a 16-2-2018.

Shehin Malamin yayi Kira ga Shugaban Kasa cewa ina dokar nan ta Freedom of Religion. Ko bata aiki ne.

Wannan Gwamnatin ta yan Izala ce ko ta Al'ummar Nigeria.

Wallahi Gwamnati kada Ku kaimu bango domin fada da yan Tijjaniya baya da dadi.

Ga dai Audio din nan a saurara

Download Audiio here

Zainab Abdullahi Bayan Wasu Yan Shekaru, Zainab Indomie Ta Dawo Bakin Aiki




Jarumar wanda ta kwashi kwananki da dama ba'a jin duriarta a harkar fim dama kafafen sada zumunta ta sanar cewa ta dawo domin cigaba daga inda ta tsaya.

Fitacciyar jaruma wanda tauraoronta ya haska shekarun baya tana ma masoyan ta da masu bibiyan fina-finai hausa albishiri na cewa ta dawo bakin aiki.
jarumar wanda ta kwashi wasu tsowon shekaru ba'ajin duriarta a masana'antar shirya fina-finai ta sanar da haka ranar talata 20 ga wata a shafin ta na kafar sada zumunta ta instagram.




"Ina yiwa dukkannin masoyana albishir da cewa na dawo bakin aiki!! ALLAH ya bamu sa'a baki daya" rubuta a shafin ta".

Da wannan sabon sanarwa da tayi, wannan zai wanzar da jita-jita da ake ta yadawa kwanan baya na cewa ta rasu.

Dalilin Da Ya Sa Nake Fitar Da Albam Biyu Duk Shekara - Nura M Inuwa

Nura M. Inuwa yana daya daga cikin mawakan da duniyar fina-finan Hausa ta Kannywood take bugun kirji da su, inda baya ga wakokin fina-finai da yake yi, yana kuma shirya fina-finai masu dauke da dimbin sakonni. A hirar da Aminiya da shi a kwanakin baya da ya zo Jos, ya bayyana nasarar da ya samu a shekarar da ta gabata, kalubalen da yake fuskanta da kuma dalilin da ya sa yake fitar da albam biyu duk shekara. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Yanzu ga shi mun shiga shekarar 2018, yaya za ka kwatanta nasarar da ka samu a bangaren sana’arka ta waka da kuma shirya fina-finai?

Alhamdulillahi, abin da zan kwatanta a shekarar da ta gabata a gare ni shi ne, shekara ce ta musamman, dalilin da ya sa haka kuwa shi ne, na samu canje-canje a rayuwata, na ga wadansu abubuwa na daban, wadda dole in ce mata ta musamman, kama daga kan ayyukana zuwa rayuwata.

Ko akwai wani canji na musamman da za ka ce ga shi ka samu a shekarar 2017?

Canjin farko dai shi ne, a da ni kadai ne nake rayuwata, ban da nauyin kowa, daga na tashi na yi wanka, sai in wuce wajen aiki, inda kuma cikin ikon Ubangiji sai Ya kawo abokiyar zama, wadda tana daga cikin canjin da na samu kaina a cikinsa.
Ta bangaren fim ma sai godiya, domin idan ka ga irin fina-finan da muke yi, za a ga akwai canji na yanayin kasuwanci a masana’antar, amma fina-finan kamfaninmu daidai gwargwado dai in an yi to ana saya, duk da cewa mun san mutane suna bibiyar irin abubuwan da muke yi masu ma’ana, shi ya sa kusan suke rububin fina-finanmu duk da yanayin da kasuwar take ciki.

Yawancin shafinka na Instagram za a ga kana sanya hotunanka da kananan yara, ko me ya jawo hakan?

A to, gaskiya halittata ce a haka, ina da son yara tun a baya tun kafin yanzu; yanzu abin da ya sa ya fito fili ake yawan ganin hakan, shi ne, dalilin social media, ita ta sa a da idan ina yi babu wanda ya sani, saboda haka ba a san ni da son yaran ba, sai dai wadanda suke tare da ni, amma saboda social media duk motsina za a ga na yi hoto da yara na sanya, abin da na fi kauna ke nan, kuma ina samun nishadi da jin dadin kasancewata da yara.

Kana daya daga cikin shahararrun mawaka da duniyar Kannywood take ji da su, duk da samun wannan shaharar a ganin wadanne kalubale kake fuskanta?

Ka san kalubale da za a ce ana fuskanta kawai wani abu ne da za a ce ya bi jiki, abin da ya sa na ce ya bi jiki kuwa shi ne, duk mutumin da ya samu kansa a irin wannan mataki na shahara, da ma ya san dole zai samu farin ciki da akasin hakan, zai hadu da masoyi, zai hadu da wanda ba masoyinsa ba, iri-iren wadannan idan za ka rika hadawa, idan ka samu makiyi, to idan ka dubi masoyi sai ka kawar da kai kawai, tun da ba dole ne kowa ya soka ba, idan wani ya so ka, wani zai ga ba kai yake ra’ayi ba, to wannan ba wani abu ne da zai dame ni ba.

Ko izuwa yanzu wani shiri kake da shi na fitar da albam?

Tun da mun shiga sabuwar shekara, kamar yadda shirina yake wato duk farko sabuwar shekara nake sakin albam guda biyu haka, to a wannan ma zan sake albam guda biyu a watan Janairu. Sunan albam din ‘Wasika’ da kuma ‘Manyan Mata’.

Mene ne dalilin da ya sa ka sanya wa albam din sunan ‘Wasika’?

Gaskiya ni idan zan yi albam, nakan yi kokari in cusa sakon da zai zo daidai da sunan albam din, ba wai kawai sunan ne yake mini dadi ba, don haka sai in rubuta don ya ja hankalin mutane ba, mutane su zo su dauka su ji sabanin abin da suka ji, inshaAllahu duk da cewa ka ji an ce wasika, akwai yiwuwar wani sako za a tura a cika, ko ma dai wani iri ne, su masu sauraro za su ji a cikin albam din.

Yanzu kasancewar ka samu abokiyar zama, wane yanayi ne ka fi jin dadin gabatar da ayyukanka?

Da yake ni da ma ba ni da wani yanayi ko lokaci da zan ce na fi so in yi waka ko rubuta waka, kodayake da ma ni rubuta waka ma bai dame ni ba, kawai da ma idan na fita studio da zil din yin waka, to inshaAllahu zan yi, idan kuma ba ni da zil din yin waka, to ko da na tukara kaina sai na yi waka, to a karshe dai zan tashi in bar ta, to kusan kowane yanayi da nake so in yi waka, wato daidai lokacin da nake fita wurin aiki, in na fita a wannan lokacin na san me zan yi, inda da na je zan fara, kuma cikin awannin da na dibar wa kaina inshaAllahu zan yi in gama, don haka samun abokiyar zama bai sa na na samu sauyi ta yadda na saba gudanar da ayyukana ba.

Kamar a yanzu kana da wani kuduri da kake so ka cimma?

To, a gaskiya kuduri wanda a halin yanzu nake so in cimma ni a nawa ganin duk abin da nake so in cimma Allah Ya nufa ya cimma, sai dai kawai, ban san me Allah Zai yi gobe ba, amma ni a yanzu duk wani mataki da nake so in kai, to Allah Ya kai ni, tun da idan na dubi daukakar da Allah Ya yi mini da irin matsayin da nake da shi da masoya da Allah Ya ba ni da kuma yadda masoya suke karbar abin da nake yi, har in fitar da wani tsari na cewa sai shekara-shekara nake fitar da albam, babu wanda ya taba yin hakan a harkar wakar Hausa, kodayake ban sani ba imma an yi dai, to a yanzu ni ne na sa wa kaina wannan tsarin, kuma hakan bai sa masoyana sun guje ni ba, suna ma kosawa ne albam din ya fito, abin da na dauka shi ne waka ba abinci ba ne da za a ce kullum sai an ci, su bukatarsu in kawo musu, su ji dadi, ni kuma tsarina ne, ina son shi, kuma ina so in rika tafiyar da shi a haka.

A karshe ko kana da wani kira da kake so ka yi ga masoyanka da kuma sauran jama’a?

Akwai abubuwa wadanda za ka ga sau da yawa ana dauko su a yaba mini, wani lokaci za ka ji an ce Nura ya mutu, wani lokaci ka ji an ce an sace ni, a baya kuma bayan na yi aure shi ma aka ce an dauke matata, to jan hankalin da zan yi ga mabiyana shi ne, sau da yawa akan kirkiro wadannan abubuwan don a rika daga musu hankali, ko kuma ni ma hankalina ya rika tashi, don in rika tsorata da wadansu abubuwa, hakan ya sa zai yi wuya a dauki lokaci mai tsawo ba a dauko wani abu da zai kawo razana a gare ni ko kuma ya tayar da hankalin masoyana ba, saboda haka su dinga hakuri da abin da suke ji, sannan idan sun ji to su dinga bibiya kafin su daga hankalinsu, wato su bi a saukake ba tare da sun tayar da hankalinsu ba, domin su tabbatar labarin da suka ji gaskiya ne ko karya ne, su kuma kiyayi watsa labaran karya.

Gane Mini Hanya : Hukumar SUBEB ta Hana Wazifa a Makarantun Tsangayar Bauchi

Rahotanni sun kawo cewa hukumar kula da ilimin bai daya wato SUBEB sashinj jihar Bauchi ta bukaci makarantun Tsangaya da su daina yin wazifa ko karanta salatul fatihi a hidimar makarantar.

A cewar hukumar hakan baya daga cikin tsarun makarantun a fadin jihar da ma tsarin hukumar UBEC ta fitar akan karatun Tsangaya.

Wannan bayani na tattare ne a wata takarda da shugaban hukumar ta SUBEB Yahaya Ibrahim Yaro ya fitar da sanya hannun sakataren hukumar Mahmeed A. Kari.


An saki wasikar ne a ranar 5 ga watan Fabairu mai taken wasikar dakatar da wazifa da salatil fatihi mai addireshi kai tsaye zuwa ga Shugabannin makarantun Tsangaya-Tsanya da suke fadin Bauchi.



Hukumar ta yi bayanin cewar ta samu korafin cewar ana tilasta wa dalibai yin wazifa da salatil fatihi.

Jaridar Leadershin ta rahoto cewa wannan mataki bai yi wa mamallakin wannan makarantar Tsangayar Sheikh Dahiru Bauchi dadi ba.

Monday, 19 February 2018

Taƙaitaccen Tarihin Jaruman Masana'antar Kannywood Hassana Da Hussaina

Hassana Yusuf da Hussaina Yusuf fuskokinsu ba boyayyu ba ne musamman ga wadanda suke kallon fina-finan Hausa na Kannywood ko shirin wasan kwaikwayo na Dadin Kowa da tashar Arewa 24 ke haska shi inda ka fi saninsu da Gimbiya da Sa’adatu. A tattaunawarsu da Aminiya sun ce halayyar da aka ba su a wasan Dadin Kowa ta yi kusa da halayyarsu ta gaske. Kuma sun ce da zarar sun samu miji tare to za a daina ganin fuskarsu a fina-finai gaba daya:

Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarku a takaice?

Hassana da Hussaina: Mu ’yan asalin Maiduguri ne. Mun yi karatun firamare da sakandare, mun yi Diploma a can inda na karanta Halayyar dan Ada, (Sociology) a Jami’ar Maiduguri. Bayan mun gama sai muka taho nan Kano inda dama can muna zuwa wajen dangin mahaifiyarmu. Amma insha Allah za mu dora da digriri nan gaba don muna da niyyar komawa karatu a nan Kano ko a Maiduguri.

Aminiya: Yaya aka yi kuka fara fim?

Hassana da Hussaina: Tun muna sakandare muka nuna sha’awarmu ta shiga fim, sai aka ce mana to mu bari sai mun kamala karatunmu. Bayan mun kammala sai muka taso da batun sai iyayenmu suka amince. Kuma a gaskiya mun shiga fim ne don mun dauki harkar a matsayin wata hanya ta fadakarwa, sannan sana’a. Wannan ne ya ja hankalinmu.

Aminiya: Kasancewarku baki lokacin da kuka zo Kano wa ya shige muku gaba a harkar?

Hassana da Hussaina: Eh gaskiya mutanen da suka nuna mana harkar nan suna da yawa. Daga cikinsu akwai wani marubuci Nazir Adam Salihi shi ya hada mu da Darakta Falalu A. dorayi. To daga nan muka fara fim. A Lokacin ni kadai (Hassana) na fara fitowa tare da jarumi Adam A. zango a cikin fim din kudiri. Daga nan kuma muka ci gaba da fitowa a fina-finai daban-daban. Daga baya kuma sai tashar Arewa 24 ta nemi mu rika yi mata wasan kwaikwayo na Dadin Kowa wanda a yanzu ma an fi saninmu a can, domin duk wanda ya ganmu da sunan da muke fitowa a Dadin Kowa yake kiranmu. A takaice dai Dadin Kowa ya danne fina-finanmu na Kannywood.

Aminiya: Duk da cewa ku ’yan biyu ne, yaya aka yi dukanku kuke sha’awar fim?

Hassana: Eh to an sha yi mana wannan tambayar, amma gaskiya ba za mu ce ga dalili ba. Kawai dai kaddararmu ce iri daya. Akwai wani mawaki da ya taba ce mana me ya sa muke fitowo a fim gaba dayanmu? Me ya sa daya ba za ta yi waka ba, daya kuma ta yi harkar fim? Sai muka ce masa ai ba mu da muryar da za mu yi waka.
Hussaina: Amma ni gaskiya a yanzu ina so in yi waka. Idan zan samu wanda zai shige min gaba zan yi. Misali idan na samu wani mawaki wanda zai koya min harkar sosai zan yi.

Aminiya: Zuwa yanzu fina-finai nawa kuka yi?

Hassana/Hussaina: Gaskiya suna da yawa ba za su kirgu ba, tunda wasu sai ka gama aikinsu sai a sauya musu suna. Tun daga 2015 da muka fara fim zuwa yau akwai su da yawa wasu ma yanzu muna kan aikinsu.

Aminiya: Wane kalubale kuke fuskanta daga ’yan uwanku a Maiduguri musamman idan kun je ganin gida?

Hassana/Hussaina: Duk da cewa duk irin abin da mutum zai yi a rayuwa sai ya samu masu magana, amma alhamdulillah mu dai ba mu da wannan matsalar duk da cewa ba za a rasa ba. Kowa ya san muna da dangi a Kano an san kuma a hannunsu muke to ina ganin shi ya sa muka samu sauki.

Aminiya: Batun aure fa yaushe ake sa ran yi?

Hassana/Hussaina: Dariya….Ko yanzu Allah Ya kawo aure za mu yi insha Allah, saboda mu a shirye muke mu yi aure. Sai dai muna burin mu yi aure tare, hakan ne ma ya kawo jinkirin auren, domin da a ce daban-daban za mu yi da tuni mun yi. Muna jiran Allah Ya kawo mana maza nagari, mu je kuma mu yi bautar Allah. Mu kuma ajiye harkar fim gaba daya.

Aminiya: Duk da cewa akwai dan bambancin a kamanninku wane hali ne kuma yake bambanta ku?

Hassana da Hussaina: Eh kamar yadda kika sani dole za ki samu ’yan biyu daya na da hakuri, daya kuma na da fada. To muma haka muke. Hassana tana da hakuri. Hussaina kuma tana da dan zafi. Wannan ya yi kusan yin daidai da halayyar da aka ba mu a wasan Dadin Kowa, duk da cewa a wasan an dan kara yawan fadan da tsiwar na Hussaina.

Aminiya: Yaya mu’amalarku take da mutanen gari?

Hassana da Hussaina: Kasancewarmu muna fitowa a fina-finai a yanzu kowa ya san mu. Duk inda muka shiga sai ki ga mutane suna nuna mu. Ko yanzu da muka fito sai da yara suka biyo mu suna nuna mu ga Gimbiya da Sa’adatu. Duk da cewa wani lokacin akwai damuwa, amma ba ya bata mana rai. Mun dauki abin a matsayin daukaka ce daga Allah muna yabawa, domin babu zagi tsakanimu sai ambaton alheri. A mafi yawan lokuta mukan tsaya mu gaisa da mutane. Idan yara ne kuma mu daga musu hannu mu wuce.

Aminiya: Wane sako kuke da shi ga masoyanku?

Hassana da Hussaina: Tsakaninmu da masoyanmu sai godiya. Muna kuma yi musu albishir su kara sa ido nan gaba za su kara samun abin da suke so daga gare mu. Fatanmu Allah Ya bar mu tare. Mun gode, mun gode.
Daga Jaridar Aminiya

Ashe ba Ronaldo da Messi ne kan Gaba Wajen Yawan Dukiya Da Kudi a Cikin ‘Yan kwallon Kafa Ba

Faiq Bolkiah mai shekaru 19 a Duniya ya sha gaban har irin su Ronaldo

- Gidan wannan matashin ‘Dan kwallon ke rike da sarautar kasar Burnei

Kwanan nan mu ka gano cewa ashe wani yaro ne dabam ba manyan gwaraza irin su Ronaldo ba ne kan gaba wajen yawan dukiya a cikin jerin ‘Yan wasan kwallon Duniya ba. Iyayen wannan yaro sun taba biyan Marigayi Micheal Jackson Dala Miliyam 12 domin yayi masu wasa.

Ba Cristiano Ronaldo da Lionel Messi ne kan gaba wajen yawan dukiya ba
Dan kwallon da ya fi kudi a Duniya shi ne Faiq Bolkiah wanda da dama ba su da labarin sa don kuwa bai yi suna ba. Bolkiah mai shekaru 19 ma dai ko bugawa Kungiyar sa ta Leicester City bai taba yi ba a halin yanzu don kuwa yana sahun masu tasowa ne a Kungiyar.


Kamar yadda jaridun kasar waje ke bada rahoto, ‘Dan wasan ya mallaki abin da ya haura Biliyoyin Daloli. ‘Yan uwan wannan saurayi ne ke da rike da sarautar kasar Burnei wanda sun ba Dala Biliyan 20 baya tuni. Dan wasan ya bugawa Chelsea kafin ya koma Leicester.

An haifi wannan ‘dan gidan sarauta ne a Garin Los Angeles Kasar Amurka amma yanzu haka yana bugawa kasar sa ta Brunei inda har ya taba cin kwallo guda. Mahaifin wannan matashi yana da motoci sama da 2300 kuma mutum ne mai facaka da kudi kamar ba ya so.

MARTANI Duk Wani Mawaki Ko Dan Fim Da Za Ka Ji Yana kalubalantar Buhari Ko Gwamnatinsa Dan Maula Ne - Inji Saeed Nagudu



Da yawa daga cikin irin su suna zuwa Abuja wajen barayin Gwamnanti musamman Gwamnatin PDP da Allah ya kawar da zalincin ta a kasar nan. Ba za mu hana ku sukar Baba Buhari ba domin kuna da ra'ayi. Amma fa ku sani shi ra'ayi ba hauka bane. 

Mene ne laifin Baba Buhari dan ya hana satar kudin talakawan da ake diba a baku a banza?

Shi ne za ku dinga sukar Gwamnanti. Duk da cewa ra'ayi kowa da irin na shi, mma ni na san da yawan  mawaka da 'an fim dake sukar Baba Buhari ba mutanen kirki bane wallahi. 

Buhari shugaban kasa ne ba wai dan wasan fim ko waka ba, kamata ya yi mu wayar da mutane abin kirki ba wai sukar Buhari ba.

A Karshe idan kuna taya iyayen gidanku barayin Gwamnanti sukar Buhari ne, mu ma masoyan shugaban kasa Muhammadu Buhari da muke kannywood ba za mu yi shiru ba, ba za mu yi shiru mu zuba muku ido ba. Yadda kuke tutiya 'yan Nijeriya ne ku, mu ma 'yan Nijeriya ne, muna da 'yancin kare Gwamnantin Buhari.

Allah ya karam wa shugaban kasa lafiya da daraja. Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya a Nijeriya baki daya.

Sunday, 18 February 2018

Buhari Ya Gaza Kuma Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Mu Fada, Cewar Fati Muhammad


"Lokacin da muka dinga kashe kudin mu akan Buhari muna yakar Jonathan ba ku yi magana ba, sai yanzu za ku zo kuna zagin mu don mun fadi ra'ayinmu a kansa?

"Buhari ya gaza kuma babu wanda ya isa ya hana mu fadar albarkacin bakin mu tunda doka ta ba mu dama", inji Fati.

AUDIO : Shi'a Ba Addinin Musulunci Bace Kafirci Ne Tsantsa: Inji Yayan Zazakky Yakubu Yahaya Katsina


Hujja Takobin Ahlul Sunnah ba ma karya ba ma yarfe sai dai muna fadin abinda mutun ya fadi da bakin shi.



Wannan Lecture ce da Yakubu Yahayya yayi bayan dawowar shi daga Iran kuma wannan shine a zuciyarshi Shi'a ba Musulunci bane amma yayi maku halin naku na munafurci wato TAKIYYA.

Shi yasa lokacin da Zakzaky yasa yaran shi sukai ma Atullahi Burtai rashin kunya yaki zuwa Zaria lokacin hasalima ya tafi amma da yaji linzami yafi karfin bakin kaza sai ya dawo yaki ya ida isa.

Haka lokacin da aka kuresu daga Masallacin Masarauta sai ya dauke ma mabiyan shi zuwa Sallar Juma'a.

Jiya kuma mun sanya ido domin muga Malam ya fito domin zagayen Ashura amma shiru kamar mushiriki yaci shurwa.

Duk wanda ya saurari wannan lecture da ya gabatar yasan Malam yasan aikin banza ne suke dan haka ba zai yarda ba yakai kanshi ga mutuwar asara.


SAURARA KAJI

Download Audio here 

Allah ya kara shiryamu shiri na Musulunci

Duk Duniya Akwai Kasar Da Ta Fi Nijeriya Abun Mamaki Kuwa? Daga Hajiya Jamila (Yar Baba Mataimaki)


 1. A Nijeriya ne Wani Kifi Ya hadiye Jirgin ruwa yana dauke da man fetur ganga dubu.

2. A nijeriya ne beraye suka kori shugaban kasa daga ofis.

3. A nijeriya ne wata macijiya ta hadiye naira miliyan talatin da shida.

4. A nijeriya ne aka baiwa wani ajiyan  man fetur kafin a Je a dawo aka tarar akuya  ta shanye rabin man.

5. A nijeriya ne aka zo da 'budget' ga shugaban kasa ga mataimakinsa ga 'yan majalisa amma ake nemi budget din sama ko kasa aka rasa Shi.

NI TSORO NA DA NAKE YI KADA WATA RANA A CE MANA BERAYE SUN SACE CBN.

 GASKIYA NE NIJERIA AKWAI ABIN MAMAKI KWARAI.

Ɗan Jihar Katsina ya jawowa Najeriya abin alfahari a Duniya

Bashir Dodo yayi wani nazari da zai agazawa masu cutar idanu

- Dr. Bashir Dodo Malami ne Matashi ‘Dan asalin Jihar Katsina ne

- Wannan bincike da aka yi ya ci lambar yabo a wata Jami’ar waje

Mun samu labari cewa wani hazikin Matashi da ya fito daga Jihar Katsina yayi suna a Duniya inda ya kammala karatun sa na Digiri na uku watau PhD a wata Jami’ar kasar waje kwanan nan.


Binciken Dodo yayi zarra a wata Jami’ar Kasar waje

Bashir Isa Dodo wanda Malami ne a Jami’ar Katsina a fannin ilmin komfuta ya kirkiro wata hanya da za a bi ta taimakawa masu fama da larurar rashin lafiyan ido a Duniya. A Jami’ar ta Birnin Brussels wannan ta sa Dodo ya karbi lambar yabo.



Wannan bincike na Bashir Dodo ta sa ya karbi kyauta a kasar inda aka tashi taron BIOMAGING na masana a shekarar bana babu kamar sa. Binciken na sa zai taimaka wajen gyara sashen retina da ke cikin idanun ‘Dan adam nan gaba a Duniya.

Likitocin idanu a Duniya za su amfana da wannan gudumuwa da Dr. Bashir Dodo ya kawo. Bashir asalin ‘Dan Jihar Katsina ne kuma yayi Digiri da Digirgir a fannin Komfuta inda ya kamalla a 2012.

Hukumar Tsara Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sakandire (JAMB) Ta Tsayar Da Ranar Yin Jarrabawar Gwaji


Shugaban Hukamar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede

- A sanarwar da hukumar ta fitar ta bakin jami'inta na hulda da jama'a, Dakta Fabian Benjamin, ta ce za a yi jarrabawar gwajin ranar 26 ga watan nan

- Ana saka ran dalibai 245,753 zasu zauna jarrabawar gwajin daga cikin dalibai 1,652,795 da suka yi rijista da hukumar

Hukumar tsara jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta sanar da ranar 26 ga watan Fabrairu da muke ciki a matsayin ranar da hukumar zata yi jarrabawar gwajin ga daliban da suka yi rijista da hukumar.

Shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ya sanar da hakan a yau, Lahadi, a garin Legas.


Benjamin ya ce ana saka ran dalibai 245,753 daga cikin dalibai 1,652,795 da suka yi rijista hukumar ne zasu zauna jarrabawar gwajin.

"muna masu farincikin sanar da jama'a cewar hukumar JAMB ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da jarrabawar gwaji ga daliban da suka yi rijista da ita. Mun tsayar da ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2018, a matsayin ranar da za a gudanar da jarrabawar gwajin," inji Dakta Benjamin.

Dakta Benjamin ya kara da cewar yajin aikin da ma'aikatan jami'o'in kasar nan ke yi ba zai shafi jarrabawar hukumar ba.

"Nan bada dadewa ba zamu aika sakon da duk daliban da suka yi rijista da mu zasu yi amfani da shi domin fitar da katin shaidar rubuta jarrabawar," inji Dakta Benjamin.

Dakta Benjamin ya tabbatar wa da daliban da zasu zauna jarrabawar cewar wannan shekarar ba za a fuskanci wahala wajen rubuta jarrabawar ba kamar yadda aka fuskanta a shekarar da ta gabata ba, domin hukumar ta yi gyare-gyare a kan dukkan da daliban suka fuskanta a bara.

Hukumar JAMB ta ce ta sayar da takardar jarrabawar wannan shekarar ga dalibai 1,966,918 kuma ana saka ran za a gudanar da jarrabawar hukumar a ranar 9 ga watan Maris mai zuwa.

Kalli zafaffan Hotunan Jaruma Maryam Yahya Na wannan Shekara 2018

Wannan sune  zafaffan hotunan maryam yahya na wannan shekara 2018 wanda jaruma maryam yahya ta fitar a shafinta na instagram ga hotunan kamar haka