Ministan yada labarai da al'adu na Najeriya ya ce ba shugaban kasar ne ya sa a cigaba da tsare jagoran 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky ba.
Ministan ya ce maimakon shugaban ya yi katsalandan a harkokin jami'an tsaron kasar, bari yake su dauki matakan da suka ga sun dace.
Alhaji Lai Muhammed ya ce gwamnatin za ta ci gaba da daukar kwararan matakai akan duk wata kungiyar mai tada zaune tsaye a kasar.
Ya kuma nanata cewa shugaba Buhari na da koshin lafiyar ci gaba da mulkin kasar.
Alhaji Lai Muhammed ya ce gwamnatin za ta ci gaba da daukar kwararan matakai akan duk wata kungiyar mai tada zaune tsaye a kasar.
Ya kuma nanata cewa shugaba Buhari na da koshin lafiyar ci gaba da mulkin kasar.
Alhaji Lai Mohammed ya yi wadannan bayanan ne a yayn wata ganawa da yayi da shugaban sashin Hausa na BBC Jimeh Saleh a birnin Landan.
A kan batun dalilin da ya sa har yanzu aka ji shiru game da bincike kan zargin cin hancin da aka yi wa sakataren gwamnatin Buhari, Babachir David Lawal, ministan ya ce: "Bai zauna a kan rahoton ba, kuma na tabbata cewa zai bayyana sakamakon binciken, da hukuncin da ya yanke a lokacin da ya shirya".
Ya kara da cewa "Abu mafi muhimmanci shi ne bai yi wata-wata ba, ya dakatar da sakataren gwamnatin tare da shugaban hukumar bincike ta NIA".
Akan batun yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaba Buhari ta lashi takobin aiwatarwa, ministan ya ce "Shawarar gwamnati ta kafa kotuna na musamman da zasu rika kula da masu laifukan cin hanci da rashawa, ina ganin wannan ita ce hanyar tabbatar da ana yakin a dukkan sassa na kasar nan".
Alhaji Lai Mohammed kuma ya kare masu cewa Buhari mutum ne mai salon mulki na kama karya, wanda ba ya mutumta 'yancin 'yan Adam.
Ga yadda sauran hirar ta kasance:
Tambaya: Lokacin da Buhari yake yakin neman zabe, wani batu da ya taso shi ne wasu na fargabar cewa shi Buhari mutum ne mai salon mulki na kama karya, ba ya mutumta 'yanci 'yan Adam. Zaka bayyana Buhari a yanzu a matsayin mai mutumta hakkin bil Adama?.
Lai Muhammed: Ko shakka babu.
Tambaya: Amma in haka ne, mabiya Shi'a ba zasu yarda da kai ba.
Lai Muhammed: E, ba zasu yarda da ni ba saboda akwai wani daidaito tsakanin hakkin bil Adama da tsaron kasa.
Tambaya: Shi yasa kenan ake cigaba da tsare shugabansu duk da cewa kotu ta ce a sake shi?
Tambaya: Shi yasa kenan ake cigaba da tsare shugabansu duk da cewa kotu ta ce a sake shi?
Lai Muhammed: Ina ganin mun bayyana dalilanmu a lokuta masu yawa a baya. Na san ba abu ne da zai kara mana farin jini ba, amma idan ana batun tsaron kasa, 'yancin wani dan kasa zai iya kasancewa bayan na sauran al'ummar kasa.
Tambaya: Shi ne ya ba wa jami'an tsaro umarnin a cigaba da tsare shi, ko kune kuka ba shi shawarar kada yayi aiki da umarnin kotu?
Lai Muhammed: Shugaban kasa baya shiga cikin aikin ma'aikatun gwamnatinsa. Ina ganin da kashin kansu suke daukan matakan da suka dace.
Tambaya: Bari mu yi magana a kan Muhammadu Buhari. Kana ganin yana da koshin lafiyar Ba Buhari ne ya sa a cigaba da tsare Zakzaky ba - Lai Mohammeda zai iya ci gaba da mulkin Najeriya kamar yadda yayi alkawari tun farko, kuma ya cika wa 'yan kasar alkawurran da ya dauka?
Lai Muhammed: Haka ne, ko shakka babu. Zaka ga hujjar haka a yadda muke yakan kungiyar Boko Haram da yadda muka fitar da kasar daga koma bayan tattalin arzikin da take fama da shi, da nasarorin da muka samu wajen yaki da cin hanci da rashawa. Amma abu mafi muhimmanci shi ne mun fitar da kasar daga koma bayan tattalin arziki ba domin mun sami karuwa kudaden shiga daga man fetur ne ba.
A hakikanin gaskiya, fannonin noma da ma'adanai da kirkire-kirkire da kere-kere.
A hakikanin gaskiya, fannonin noma da ma'adanai da kirkire-kirkire da kere-kere.
Tambaya: Yanzu idan na baka takarda da alkalami, na ce ka rubuta masa sakamakon mulkinsa, daga daya zuwa goma - nawa zaka ba shi?
Lai Muhammed: Na gwammace in fadi abubuwan da ya yi. Sai in kyale mutane da kansu su yanke hukunci. Na fada maka cewa yayi alkawarin zai kawo karshen rashin zaman lafiya, kuma ya ce zai yaki cin hanci da rashawa kana ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar nan, kuma ya sami nasarori a dukkan wadannan fannonin.
Tambaya: Bari mu yi magana game da abin da yake faruwa a yankin yamma maso gabashin Najeriya, inda ake da matsalar kungiyar IPOB da mutanen da ke ganin gwamnatin Buhari ba ta kyautata musu. Gaba daya, mene ne ra'ayinka game da matsalar IPOB da abubuwan dake faruwa a gabashin Najeriya?
Lai Muhammed: Kaga kungiyar IPOB ba tana fafutukar samar wa 'yan kabilar Igbo makomar siyasa ba ne.
Da badun ta mayar da gwagwarmayar ta zama yadda ta kasance ba, da gwamnati ma bata soke ta ba. Ai kungiyar MASSOB ta fi ta dadewa wajen fafutukar neman kasar Biafra, amma IPOB ta zama kungiyar 'yan ta'adda, shi ne yasa aka soke ta. IPOB ta kafa wasu bangarori kamar na jam'ian tsaro nata da hukumar leken asiri nata.
Ta rika kai wa sojojin Najerya hari, kuma ta kan tilasta wa mutanen da basu ji ba basu gani ba su bata kudade. Wannan shi ne ainihn dalilin da yasa aka soke kungiyar, ba domin tana fafutukar samar wa 'yan kabilar Igbo kasarsu ne ba.
Tambaya: A yanzu kun ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. Kana cewa kenan abin da ya faru ga kungiyar Boko Haram shi zai faru da su?
Lai Muhammed: A'a. Ina ganin wannan fahimtar tana da rauni.
Tambaya: A yanzu kun ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. Kana cewa kenan abin da ya faru ga kungiyar Boko Haram shi zai faru da su?
Lai Muhammed: A'a. Ina ganin wannan fahimtar tana da rauni.
Tambaya: Amma kun ayyana su a matsayin 'yan ta'adda.
Lai Muhammed: E mana, ai da zarar an ayyana kungiyaa matsayin ta ta'addanci, to bata da sauran damar da zata fito tayi fafutuka ko tayi zanga-zanga game da ko wane irin batu. Ka tuna a baya IPOB kan fito a binar jama'a ta hana ma'aikata fita zuwa wuraren ayyukansu, kauma ta tabbatar da hakan ya kasance. Amma wannan duka zai kau daga yanzu.
Tambaya: Saboda haka da Boko Haram da IPOB duka a sahu daya suke kenan?
Lai Muhammed: A matsayinsu na 'yan ta'adda?
Lai Muhammed: A matsayinsu na 'yan ta'adda?
E, hake ne.
Tambaya: Kuma za ku dirar musu kamar yadda kuke dirar wa 'yan Boko Haram?
Lai Muhammed: Duk wata kungiyar da aka ayyana ta a matsayin ta ta'addanci, kuma ta nemi tayar da zaune tsaye, zata fuskanci mataki irin wanda ya kamata daga hukumomi. Kuma ko ina a duniya haka batun yake.
Tambaya: Amma su maganar da suke yi ita ce, Buhari baya son su. An nada shugabannin manyan hukumomin gwamnati, basa ciki ba a ba su ba. Suna ganin Buhari baya son su.
Lai Muhammed: Ina ganin akwai kuskure a wannan tunanin. Mutane da dama na mantawa da cewa muna gudanar da tsarin tarayya ne a Najeriya, inda muke da fannoni uku na gwamnati - muna da kananan hukumomi da gwamnatocin jihohi, sai kuma gwamnatin tarayya.
A yankin gabashin Najeriya, muna da kananan hukumomi da 'yan kabilar Igbo ke iko da su gaba daya. Kuma a matakin jiha, suna zaban 'yan kabilar Igbo ne su wakilce su a majalisun jihohinsu. Saboda haka ya kamata su daina nuna wa tamkar Najeriya na gudanar da tsarin mulkin gwamnati daya tilo ce a tsakiya. Tsarinmu na tarayya ne, kuma a wannan matakin, babu wanda zai iya cewa ana danne shi.
A yankin gabashin Najeriya, muna da kananan hukumomi da 'yan kabilar Igbo ke iko da su gaba daya. Kuma a matakin jiha, suna zaban 'yan kabilar Igbo ne su wakilce su a majalisun jihohinsu. Saboda haka ya kamata su daina nuna wa tamkar Najeriya na gudanar da tsarin mulkin gwamnati daya tilo ce a tsakiya. Tsarinmu na tarayya ne, kuma a wannan matakin, babu wanda zai iya cewa ana danne shi.
Tambaya: Kai a ganinka, Buhari ya tsani 'yan kabilar Igbo?
Lai Muhammed: Ban yarda da wannan magana ba. Idan ka duba ministocin dake wannan gwamnatin, akwai 'yan kabilar Igbo a cikinta suna rike da mukamai manyan mukamai. Alal misali, ministan harkokin kasashen waje dan asalin kabilar Igbo ne daga jihar Enugu. Ministan Ciniki da Masana'antu daga jihar Abia ya fito. Ministan Kwadago daga jihar Anambra ya fito.
Wadannan manyan ma'aikatun gwamnati ne. Kaga karamin ministan Ilimi daga jihar Imo ya fito. Dukkansu 'yan kabilar Igbo ne. Idan da shugaba Buhari baya kaunarsu da bai nada su a wadannan manyan ma'aikatun ba.
Bbchausa
Bbchausa
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment