sport:- Mancherster United 'za ta nemi Mesut Ozil' - NewsHausa NewsHausa: sport:- Mancherster United 'za ta nemi Mesut Ozil'

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 3 October 2017

sport:- Mancherster United 'za ta nemi Mesut Ozil'

Rahotanni a Ingila na cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta nemi dan wasan Jamus Mesut Ozil a watan Janairu.
Labarin da jaridar the Independent ta wallafa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake kwan-gaba-kwan-baya kan sabuwar yarjejeniya tsakanin dan wasan da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.
Mesut Ozil ya koma Arsenal ne daga Real Madrid kan kudi fam miliyan 42.4 a shekarar 2013.
Yana daga cikin manyan 'yan wasan kungiyar da sukan sha suka a duk lokacin da ba ta yi katabus ba.
Sai dai ya sha nanata irin rawa da kuma kokarin da shi da sauran 'yan wasan kulob ke takawa a duk lokaicn da aka bujuro da irin wannan zargi.

bbchausa

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment