Fati Mohammed Ta Zama Daraktar Mata Na Gidauniyar Atiku Reshen Arewa Maso Yamma - NewsHausa NewsHausa: Fati Mohammed Ta Zama Daraktar Mata Na Gidauniyar Atiku Reshen Arewa Maso Yamma

Pages

LATEST POSTS

Monday 2 October 2017

Fati Mohammed Ta Zama Daraktar Mata Na Gidauniyar Atiku Reshen Arewa Maso Yamma

Tsohuwar jarumar finafinan Hausa, Hajiya Fati Muhammad ta samu karin matsayi a gidauniyar Atiku Abubakar, inda yanzu ta samu matsayin daraktar mata na gidauniyar a shiyyar arewa maso yamma.

 Kafin wannan matsayi Fati ita ce daraktar mata na gudauniyar reshen jihar Kaduna.

Jihohin da Fati za ta jagoranta sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto, Jigawa da Zamfara.

Gidauniyar ta Atiku ta kasance tana tallafawa marasa karfi, wadanda suka hada da talakawa, marayu, 'yan gudun hijira da sauransu.
Ga hotunan domin gasgatawa:-







Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment