Yan Film Ya ya Ne Kamar Naku Na Gida – Inja Saima Muhammad - NewsHausa NewsHausa: Yan Film Ya ya Ne Kamar Naku Na Gida – Inja Saima Muhammad

Pages

LATEST POSTS

Monday 2 October 2017

Yan Film Ya ya Ne Kamar Naku Na Gida – Inja Saima Muhammad

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywwod Saima Muhammad ta fito ta shaidawa da duniya a wani irin salo na maida martani da babbar murya cewar su ma fa ‘ya ‘yane kamar dukkan sauran mata.

Jarumar tayi wannan kalaman ne a yayin wani taron da fitattun matan fim din suka shirya da zummar kafa kungiyar su a wani dakin taro dake a cikin garin Kano.
Saima Muhammad dake jagorantar tafiyar ta kungiyar ta fada a cikin jawabin nata cewa makasudin kafa wannan kungiyar tasu shine domin fadakar da al’umma irin darajar da matan fim suke da ita kamar sauran mata.

A cewar ta: “Mu ma mata ne masu daraja da kima tamkar wadan da iyayen su ke killace su ko kuma su kaisu kasashen waje yin karatu.”
Ta cigaba da ciwa daga cikin manufofin kungiyar ta su za su rika kai ziyara asibiti tare kuma da taimakwa marasa lafiya da sauran marasa galihu a cikin al’umma.
NAIJ HAUSA

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment