'Ba zan sayar da kasona na Arsenal ba' - NewsHausa NewsHausa: 'Ba zan sayar da kasona na Arsenal ba'

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 7 October 2017

'Ba zan sayar da kasona na Arsenal ba'

Alisher Usmanov ya ce bai tattauna da Stan Kroenke kan zai sayar masa da hannun jarinsa na Arsenal ba.
An ruwaito cewar Kroenke wanda yake da kaso 67 cikin dari, ya tuntubi Usmanov kan zai sayi kason Usmanov na 30 cikin dari.
Usmanov mai shekara 64, ya ce hannun jarinsa ba na sayar wa bane, kuma ya dade yana kaunar Arsenal.

A ranar Laraba ne Usmanov ya ce kason da yake da shi mai mahimmaci ne da zai kare bukatun magoya bayan kungiyar.
Duk da hannun jarin da Usmanov keda shi a Arsenal, baya cikin manyan daraktocin kungiyar ko masu yanke shawara.

A baya can Usmanov ya soki Kroenke kan kasa taka rawar gani da Arsenal keyi a wasanninta.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment