March 2018 - NewsHausa NewsHausa: March 2018

Pages

LATEST POSTS

Saturday, 31 March 2018

Kalli Kyawawan Hotunan jarumi Ali Nuhu A Wajen Aikin Umrah

Wannan sune hotunan jarumi ali nuhu a wajen aikin umrah na wannan shekara.







Ƙura Takai Bango : Buhari ya bada umarnin harbe 'yan bindiga a Zamfara

Bayan kazamin harin da 'yan bindiga suka kai garin Bawar-Daji da ke jihar Zamfara a Najeriya, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane da dama, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa jami’an tsaro umurnin harbe duk wani mutun da aka gani da bindiga a fadin Jihar.

Gwamnan Jihar Abdul Azizi Yari ne ya sanar da umarnin, a lokacin da ya ziyarci fadar Sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad domin alhinin hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai a garin Bawar Daji a baya bayannan.

Umarnin na shugaban Najeriya ya ce kada jami’an tsaro su bata lokaci wajen kokarin gurfanar da ‘yan bindiga ko barayin da suka kama a kotu, kai tsaye kawai su bindige su.

Gwamnan jihar ta Zamfara ya ce matakin ya biyo bayan yadda matsalar hare-haren 'yan bindiga ta ki ci ta ki cinyewa.
Yari ya kuma bada umurnin tube Hakiman yankunan da ake zargi da bai wa 'yan bindigar da ke kai harin mafaka, yayin da ya ja kunnen sauran Sarakuna cewar duk wanda aka samu yana boye irin wadannan mutane a yankunansu, zai gamu da fushin hukuma.

Friday, 30 March 2018

Kungiyar Izala Ta Sauka Kasar Jamus Domin Gudanar Da Gagarumin Wa'azi (kalli Hotuna)


Wata tawagar malamman Izala daga Nijeriya da ta hada wasu fitattun malumai da suka hada:

Sheikh Bala Lau, Sheikh Kabiru Haruna Gombe, Sheikh Dr. Jabir Sani Mai Hula Sokoto, Sheikh Saifuddeen, (Daga Spain) Sheikh Mahmod da Sheikh Bature Amin.(daga UK) za su gabatar da gagarumin wa'azi mai taken 'Farfadowar Muryar Sunnah a  kasashen Turawa'.

Wanda za a yi a ranakun 31/3/2018 da 1-4-2018 Masjid Rahma Being, Gesunbrunnen 1 20537, Hamburng karfe 12:00 na safe da BuegerHaus Wilheems Burgh Mengestrasse 2021107 Hamburg 10:00-20:00.

Ga hotunan kamar haka


DA DUMIDUMINSA Wani Dan Majalisa Ya Sake Rasuwa



Dan majalisar tarayya daga jihar Kogi, mai wakiltar Lokoja/Kogi/Koton Karfe, Umar Buba Jibril ya rasu yana mai shekaru 57.

Majiya daga iyalan mamacin ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne a Abuja sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Rahotanni sun nuna mamacin ya jima yana fama da rashin lafiya, wanda hakan ya sanya ya dauki kusan shekara guda bai halarci zama a majalisa ba. Inda aka rawaito cewa rabon da ya halarci zaman majalisa tun lokacin da shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi.

I dan ba a mance ba a makonni kusan uku da suka gabata Sanata Ali Wakili daga jihar Bauchi ya rasu.

Ta Leko Ta Kuma : Wata Tsohuwa Ta Damfari Shugaban Kasa Muhammadu Buhari



A kwanakin baya hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari sun wallafa a kafafen sadarwa na zamani cewa, matar Marthin Luther King Jr sun karrama shi da kyauta mafi daraja da aka taba ba wa wani bakar fata a Afirka.

Sai dai daga baya Cibiyar The King Center, wacce ke adana tarihin fitaccen bakar fatar nan na Amurka, marigayi Martin Luther, ta nesanta kanta daga lambar yabon da aka bai wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Martin Luther King Jr. Ba'amurke ne kuma bakar fata, babban jagoran addinin Kiristanci, dan gwagwarmayar kwatar 'yanci, wanda ya shahara a duniya a matsayin gwanin iya sarrafa harshe, kana kuma ya zama jagoran fafutukar kwatar 'yanci daga 1954 zuwa 1968.

Coretta Scott King marubuciya ce kuma Ba'amurkiya, jagorar kungiyar gwagwarmayar kwatar 'yanci kana kuma matar Martin Luther King, Jr. Coretta Scott King ta taimaka wajen gwagwarmaya a shekarar 1960.

Thursday, 29 March 2018


Audio : Wannan Talla Ce ko Zubar Da Mutuncin Mata a kasar saudiya

Wannan talla ce ko zubar da mutuncin mata a kasar saudiya. 

Ku kalla da kanku gani ya kori ji. 

Abin tambayar ma shine aikin me take.

Samun ƙungiyyar Matan Masana'antar Kannywood Abu Mai Matukar Amfani - Inji Saratu Gidado

Sartu Gidado Daso ta bayyana qungiyoyin da mata yan film
ke samarwa a yanzu domin taimaka wa ’yan fim da sauran
jama'a a matsayin wani mataki na ci-gaba da harkar ta
samu.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin fitacciyar jaruma Hajiya
Saratu Gidado a lokacin da ta ke tattaunawa da wakilin
mujallar Fim dangane da irin yanayin da aka samu a cikin
masana’antar na bullowar wasu kungiyoyin mata da ke
taimaka wa jama’a marasa karfi.

Saratu (Daso), wadda a yanzu ita ce Jakadiyar Sarkin Kano,
ta ce, 

Wadannan kungiyoyi na taimaka wa marayu da
marasa karfi, musamman yara kanana da wasu da aka mutu
aka bar su. Wasu na yawon bara, wasu na yawon talla.

“To gaskiya kafa kungiyar ya burge ni. Na ji dadin yadda su
ka zauna su ka yi tunani su ka samar da wadannan
kungiyoyin.

Ka san babu mai iya wa mutum sai Allah. To amma dai ko
yaya ka samu ka taimaka wa na kasa da kai ka na da lada
mai yawa. Kuma kai ma da ka ke da hali ba ka san yadda
za ka kasance a gaba ba, amma dai alheri ba ya faduwa
kasa banza.”

Ta ci gaba da cewa, “Yanzu wannan aikin alheri da aka fara
mutane za su san cewa ’yan fim su na da tausayi, mu na
taimakon bayin Allah mu ma. Duk da ake yi mana kallon
wasu mutane na daban, mu ma mu na aimakon, don haka
yanzu mun fito mu na taimaka wa mutane kamar yadda ake
gani su na yi duk da dai ba na cikin kowace kungiya saboda
hidima ta ni ta yi min yawa don haka ni nawa taimakon ba
a bayyane na ke yin sa ba. Don haka ban shiga cikin
kungiyoyin ba, amma ina da labarin abubuwan da su ke yi,
kuma ina goyon bayan su dari bisa dari.”

A game da kasa kungiyoyin kashi-kashi, kowa ya na yin
tasa, Saratu ta ce, “To ai ba an rabu ba ne kuma ba ana
fada ba ne, kowa ya na da tsarin sa na yadda zai bayar da
nasa taimakon.
“Haka idan wata kungiya ta kai tallafi ga iyalan ’yan fim
da aka rasu aka bar su da kuma wadanda ba su da karfi,
wata kungiya kuma ta kai tallafi gidan marayu, wata kuma
ta kai tallafi asibiti, ka ga ai an samu ci-gaba. Kowa da irin
tallafin da ya ke ganin zai iya bayarwa ga jama’a. Don
haka samun karin kungiyoyi masu bada tallafi abu ne mai
kyau, kuma ci-gaba ne.”
Daga karshe Saratu ta yi kira ga al’umma da su bada
gudunmawar su, musamman ma ’yan fim, domin ganin
wadannan kungiyoyi sun samu nasarar da su ke bukata ta
taimaka wa mabukata.

Wednesday, 28 March 2018

Karanta Sabbin Tsarukan Da Aka Sanya ma Facebook


Kamfanin Sada Zumunta na Facebook ya kaddamar da sabbin tsare-tsare da za su bai wa masu amfani da shafinsa damar kare bayanansu na sirri cikin sauki.Wannan na zuwa ne bayan an kwarmato cewa, kamfanin ya yi wa mutane miliyan 50 kutse, abin da ya haifar da cecekuce a sassan duniya.

Sabbin tsare-tasren da Facebook ya kaddamar za su bai wa masu amfani da shi damar shiga cikin bayansu na sirri don sauya abin da suke so cikin sauki tare da sauke ko kuma share wasu bayanai da kamfanin ke adanarsu.

Kazalika kamfanin ya ce, tsare-tsaren za su bai wa jama’a damar kare bayanansu da kansu, in da za su rika zabar irin mutanen da suke so su rika duba bayanansu a shafin tare da dakatar ko kuma barin tallace-tallacen da ke bijirowa a shafukansu.

Shgaban sashen kare bayanan sirrin jama’a a Facebook, Erin Egan ya ce, sun samu bayanan da ke cewa, mutane na shan wahala wajen lalubo wuraren da za su latsa don kare bayanansu, abin da ya sa ya ce, ya zama dole su wayar da kan al’umma.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan kamfanin ya sha zazzafar suka jim kadan da samun labarin yi wa mutane miliyan 50 kutse a kundinsu, lamarin da ake ganin yana da nasaba da yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump a shekarar 2016.

Ko da dai shugaban kamfanin na Facebook, Marc Zuckerberg ya fito ya bada hakuri kan abin da ya faru, amma duk da haka ‘yan Majalisun Amurka sun bukace shi da ya bayyana a Washington don bada bayani kan batun.

Ita ma Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi daukan mataki nan gaba kan kamfanin, in da tuni Birtaniya ta kaddamar da nata binciken.

Kamfanin Facebook Ya Kaddamar Da Sabon Tsari A Shafin Sa

Kamfanin Sada Zumunta na Facebook ya kaddamar da sabbin tsare-tsare da za su bai wa masu amfani da shafinsa damar kare bayanansu na sirri cikin sauki.

Wannan na zuwa ne bayan an kwarmato cewa, kamfanin ya yi wa mutane miliyan 50 kutse, abin da ya haifar da cecekuce a sassan duniya.

Sabbin tsare-tasren da Facebook ya kaddamar za su bai wa masu amfani da shi damar shiga cikin bayansu na sirri don sauya abin da suke so cikin sauki tare da sauke ko kuma share wasu bayanai da kamfanin ke adanarsu.

Kazalika kamfanin ya ce, tsare-tsaren za su bai wa jama’a damar kare bayanansu da kansu, in da za su rika zabar irin mutanen da suke so su rika duba bayanansu a shafin tare da dakatar ko kuma barin tallace-tallacen da ke bijirowa a shafukansu.

Shgaban sashen kare bayanan sirrin jama’a a Facebook, Erin Egan ya ce, sun samu bayanan da ke cewa, mutane na shan wahala wajen lalubo wuraren da za su latsa don kare bayanansu, abin da ya sa ya ce, ya zama dole su wayar da kan al’umma.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan kamfanin ya sha zazzafar suka jim kadan da samun labarin yi wa mutane miliyan 50 kutse a kundinsu, lamarin da ake ganin yana da nasaba da yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump a shekarar 2016.

Ko da dai shugaban kamfanin na Facebook, Marc Zuckerberg ya fito ya bada hakuri kan abin da ya faru, amma duk da haka ‘yan Majalisun Amurka sun bukace shi da ya bayyana a Washington don bada bayani kan batun.

Ita ma Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi daukan mataki nan gaba kan kamfanin, in da tuni Birtaniya ta kaddamar da nata binciken.

Burina Shine Duniya Ta San ni - Inji Jaruma Asabe Madaki

ASABE Madaki, jarumar fim din ‘There is a Way’ da kuma sabon fim din ‘Sarauniya’, ta bada shawarar cewa ya kamata mu yi finafinai da Turanci don mu bada labarin al’adar mu da kan mu. Haka kuma ta fadi yadda a matsayin ta na lauya ta maida hankalin ta ga fitowa a finafinai.


Asabe kwararriyar lauya ce wadda ta ke da matsayin digiri na biyu kuma a yanzu ta na koyarwa ne a bangaren karatun aikin lauya din. Sai dai duk da matakin da ta kai na karatu da aiki a halin yanzu ta samu kan ta a cikin harkar fim, har ma ta fita a finafinai masu dama a Kannywood. Kwanan baya, wakilin mu ya hadu da Asabe a wajen daukar wani fim na Turanci mai suna ‘This is the Way’. Fim din ya na cikin jerin finafinai na Turanci da Kabiru Musa Jammaje ya ke shiryawa.
A hirar su da wakilin mu, Asabe Madaki ta fada masa cewa ita dai haifaffiyar Jihar Kaduna ce, kuma ’yar asalin Karamar Hukumar Jema’a. Ta yi karatun firamare a Command Children’s School da ke Kaduna, sannan a shekarar 2000 ta kammala karatun sakandare a Kwalejin ’Yanmata ta Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Gusau.
Asabe ta yi karatun digiri a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya daga shekarar 2002-2007 inda ta karanta aikin Shari’a (Law). Daga nan ta yi makarantar koyon aikin Shari’a, wato Law School, da ke Abuja. Sannan ta yi hidimar kasa a nan Abuja.
Don zurfafa ilimin ta, sai jarumar ta yi karatun digiri na biyu a kwas din aikin lauya a kasar Scotland.

Bayan na dawo kuma ina yin lakca ta rabin lokaci, kuma a yanzu na samu kai na a cikin harkar finafinai, musamman namu na Arewa da ake kira da Kannywood,” inji ta.

To, ko me ya ja hankalin Asabe Madaki zuwa shiga harkar fim, musamman idan aka yi la’akari da karatun ta na aikin lauya? Sai ta amsa da cewa: “Gaskiya mutane za su kalli haka, amma dai ko lokacin da na kammala digiri na na biyu a Scotland na dawo gida, na taba aikin lauya, amma a gaskiya tun lokacin da na ke makaranta ma hankali na ya fi karkata ga masana’antar nishadi, don haka daga baya na shiga harkar fim gadan-gadan.

Koda yake zan iya cewa tun ina makarantar firamare ina cikin kungiyar dirama da kade-kade da kuma wake-wake. Don haka zan iya cewa abin kamar a jini na ya ke; tun ina karama na ke burin na zama ’yar fim.”

Asabe na da wata ka’ida, wadda ta sa ba a ganin ta a finafinai barkatai. A cewar ta, “Ba kowanne fim na ke yi ba, sai wanda na ga ya na da ma’ana kuma ya ke kunshe da sakon da zai isar ga masu kallon sa. Don haka ba wai don ina son na yi fim ba sai kawai na fito a cikin kowanne irin fim. Don haka a yanzu finafinan da na yi wadanda su ka hada da na Turanci da Hausa su ne ‘Sarauniya’ da kuma ‘Gwaska’, na Turanci kuma sun hada da ‘Laraba’s World’, da ‘Queen Amina’ da ‘Make Room’ da ‘Light and Darkness’, sai kuma wanda ka same ni a yanzu ina yi, ‘This is the Way’ na kamfanin Jammaje Production.”

Da mu ka tambaye ta idan ta samu matsala da ta shigo harkar fim, sai Asabe ta ce, 
E to, ba zan iya cewa ban fuskanci matsala ba. Matsalar dai da na samu ita ce a fim din Hausa kasancewar ni ba cikakkiyar Bahaushiya ba ce, don haka wasu kalmomi na Hausa su na yi min tsauri sosai wajen furta su. Duk da cewar zan iya rubutawa da kuma karantawa, amma dai wajen furtawa wadansu za su gane ni ba cikakkiyar Bahaushiya ba ce sai dai a yanzu ina kokarin ganin Hausar ta tsaya a baki na, kasancewar ina da burin bayar da gudunmuwa ta ta hanyar finafinan Hausa.”

Kowane mutum ya na da buri da ya ke so ya cimmawa. Ita ma Asabe na da nata a matsayin ta na jarumar fim. Cewa ta yi: 

Buri na dai shi ne in taimaka wa al'umma ta ta hanyar finafinai masu ma'ana, kuma ina so na zama fitacciyar jaruma a duniya. Ina da burin na mallaki kamfanin da zai rinka shirya finafinai ya na fitar da su, kuma ina so na rinka taimaka wa mutanen da su ke shiga harkar fim.”

Wato dai watakila nan gaba a samu wata Lupita Nyong’o kenan daga arewacin Nijeriya; kamar yadda jarumar ’yar kasar Kenya ta bulla daga Afrika ta yi fice a duniya, haka Asabe Madaki ke so ita ma ta yi kenan. To Allah ba ta sa’a, amin.
To me za ta ce kan yadda wasu mutane su ke kallon ’yan fim din Hausa a matsayin masu bata tarbiyya? Lokacin da ta yanke shawarar shigowa cikin harkar fim ta samu kalubale a gidan su sakamakon wannan ganin da ake yi wa ’yan fim?

Amsar Asabe: “Zan iya cewa na samu, domin kuw matsalar farko da na samu a wajen mahaifi na na samu, inda ya ke ganin shi dai na tsaya na kammala karatu na domin ko lokacin da ina jami’a akwai wasu kamfanoni da su ka nemi na yi musu aiki, amma a gida sai iyaye na su ka hana ni don su na ganin hakan zai iya shafar karatu na. Amma da na kammala sai ya zama su na ba ni kwarin gwiwa wajen aikin da na ke yi na fim.”

Abin da ya fi bada mamaki game da Asabe shi ne kasancewar ta jarumar finafinan Hausa da na Turanci. Ko yaya ta ke kallon kan ta a haka?

To abu ne mai sauki, musamman ma a matsayi na na wadda na ke so na bayar da tawa gudunmuwar domin ci-gaban yanki na na Arewa ta hanyar finafinai,” inji jarumar.

Fim din ‘This is the Way’ aikin sa na Hausa ne, amma da Turanci ake yin sa. Yaya ’yar was an za ta kwatanta shi da sauran finafinan da ta yi? Sai ta ce: 

“To gaskiya wannan fim din fim ne da ya fita da wasu muhimman darusa a cikin sa wanda mutane ba su san su ba. Idan na ce ba a san su ba, ina nufin wadanda za su kalle shi da kuma yaren da aka yi shi. Ka ga shi labarin al'adar Hausa ne da mutanen Arewa, sai aka yi fim din da harshen Turanci. To ko ka ga ba Hausawa ba ne za su kalle shi, wasu al'umma ne da ba su san al'adar Hausa da mutanen Arewa ba za su gani. To ka ga wannan zai isar da sakon al'adar mu zuwa wata kasa da ba su san mu ba. Za su ga al'adun mu masu kyau da irin yadda mu ke gudanar da rayuwar mu. Don haka shi wannan fim din 'This is the Way' zai samar da fahimtar juna ga sauran al'umar mu da su ke ganin kamar ba mu waye ba ko ba mu iya Turanci ba. Yanzu idan ka duba fim din ‘There is a Way’, wanda shi ma an fitar da shi ya shiga kasuwa, ya bayar da ma’ana sosai wanda ina ganin hakan ce ta sa shi Kabiru Musa Jammaje ya samu karfin gwiwar da ya kara fito da fim din ‘Light and Darkness’ da kuma wannan da ake yi a yanzu, ‘This is the Way’.

Me ya fi burge jarumar a cikin harkar fim?
Asabe: “To abin da ya fi burge ni shi ne na ga an yi fim mai ma’ana da kuma isar da sako. Shi ya sa ma na ke jinjina wa Kabiru Musa Jammaje da kuma kamfanin sa, Jammaje Production, da ya ke fitar da finafinai na Hausa amma da yaren Turanci, domin kuwa wadannan finafinai da wadanda zai fito da su nan gaba su ne za su cike gibin da ya ke tsakanin Nollywood da Kannywood, domin ana ganin kama Turanci ne bambancin mu, to ga shi mu ma mu na yin, don haka duk wanda ya ke ganin Hausa kawai mu ka iya a Kannywood to a yanzu an san mu na yin na Turanci. Kuma finafinan mu za su shiga duniya a rinka ganin al’adun mu na Arewa ta hanyar wadannan finafinai, ‘There is a Way’, ‘Light and Darkness’ da kuma ‘This is the Way’.
Daga karshe, Asabe Madaki ta kira na musamman ga kamfanoni da ke shirya fim a nan Arewa, inda ta ce: 

Su yi koyi da wannan furodusa, Kabiru Musa Jammaje, wajen shirya fim mai dauke da al’adun mutanen Arewa kuma da harshen Turanci, don ta haka ne za a rinka sanin al’adun mu da kuma yadda mu ke gudanar da rayuwar mu ba tare da wasu su na bada labarin mu ba yadda mu ke ba.”

Sources :jaridar fimmagazine

Kamfanin Facebook Ya Kadamar Da Sabon Tsari A Shafinsa

Kamfanin Sada Zumunta na Facebook ya kaddamar da sabbin tsare-tsare da za su bai wa masu amfani da shafinsa damar kare bayanansu na sirri cikin sauki.Wannan na zuwa ne bayan an kwarmato cewa, kamfanin ya yi wa mutane miliyan 50 kutse, abin da ya haifar da cecekuce a sassan duniya.

Sabbin tsare-tasren da Facebook ya kaddamar za su bai wa masu amfani da shi damar shiga cikin bayansu na sirri don sauya abin da suke so cikin sauki tare da sauke ko kuma share wasu bayanai da kamfanin ke adanarsu.

Kazalika kamfanin ya ce, tsare-tsaren za su bai wa jama’a damar kare bayanansu da kansu, in da za su rika zabar irin mutanen da suke so su rika duba bayanansu a shafin tare da dakatar ko kuma barin tallace-tallacen da ke bijirowa a shafukansu.

Shgaban sashen kare bayanan sirrin jama’a a Facebook, Erin Egan ya ce, sun samu bayanan da ke cewa, mutane na shan wahala wajen lalubo wuraren da za su latsa don kare bayanansu, abin da ya sa ya ce, ya zama dole su wayar da kan al’umma.

Wannan matakin dai na zuwa ne bayan kamfanin ya sha zazzafar suka jim kadan da samun labarin yi wa mutane miliyan 50 kutse a kundinsu, lamarin da ake ganin yana da nasaba da yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump a shekarar 2016.

Ko da dai shugaban kamfanin na Facebook, Marc Zuckerberg ya fito ya bada hakuri kan abin da ya faru, amma duk da haka ‘yan Majalisun Amurka sun bukace shi da ya bayyana a Washington don bada bayani kan batun.

Ita ma Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi daukan mataki nan gaba kan kamfanin, in da tuni Birtaniya ta kaddamar da nata binciken.

VIDEO : Ramakon Gayya Official Teaser || Fim Din Adam A Zango Yayi Da Tsohuwar Matarsa (Nas)

White House Family Presents
RAMAKON GAYYA.....Teaser

DIRECTOR __Bello moh'd bello
ASS DIRECTOR__Saifullahi I. Idriss
PRODUCER__Kabiru A. Zango
STORY__Adam A. Zango
SCREEN PLAY__Nazir Alkanawi
CONTINUETY__Abba Kabugawa
MUSIC__Nura M. Inuwa__Husaini Danko
D.O.P Murtala balala
COSTUMIERS__Sadiqu Artist
MAKEUP__Nasiru Ishaq


Download video here

Sababbin Hotunan Umar M Shareef Dauke Da Magana Mai Muhimmanci

Sababbin hotunan jarumi kuma shahararren mawaki umar m shariff da ya saki a shafinsa na instagram a cikin kwana kin nan wanda a duk hotun yayi maganaai mai matukar amfani ga mai tunani ga hotunan kamar haka
"Karka damu da musu Kulla maka sharri,duk iya kokarinsu basu wuce zartar da kaddarar da Allah yayi akanka "
"Kada lamarin duniya ya dame ka domin duk abinda ke cikinta na Allah ne".
Abu nawa Allah ya baka, baka rokeshi ba,ka tabbata idan ya hanaka abinda ka roka to akwai dalili

Tuesday, 27 March 2018

Kalli Hotunan Bukin Auren Jaruma Sadiya Adam (Hasashe) Tare Da Mijinta

Albishirin ku Ina muku marhaba da lalle na shigowa wannan shafi a yau muzo muku da hotunan sadiya adam wanda anka fi sani da (hasashe) tare da agonta Allah ya bada zama lafiya amen. Ga hotunan




Sabbin hotunan rahana sadau


 Wannan sune sababbin hotunan jaruma rahama sadau da ta fitar a shafinta na instagram


BIDIYO Wani Bidiyon Harin Da Ake Zargin 'Yan Ta'addan Houthi Da Kaiwa A Jiya Lahadi A Garin Reyadh Dake Saudiyya


Wani Bidiyon Harin Da Ake Zargin 'Yan Ta'addan Houthi Da Kaiwa A Jiya Lahadi A Garin Reyadh Dake Saudiyya.

Daga Sani Hausawi.

Download video here

AL'AJABI: An Haifi Yaro Dauke Da Kur'ani Da Carbi A Jihar Bauchi: Wannan karamar Shehu Tijjani Ne Ta Kara Bayyana Ga Masu Inkarin Me Darikar Ta Tijjaniyya


...wannan raddi ne ga masu inkari da Annabi (S.A.W), cewar Sheik Dahiru Bauchi

Daga Maiwada B. Atake

Wata mata a garin Burga dake jihar Bauchi ta haifi yaro da Kur'ani da kuma carbi a hanunsa.

A yayin da matar ta zo da labarin al'ajabin zuwa gidan Shehin Malamin nan, wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ta shaida cewa, wannan yaro wanda aka rada masa suna Muhammad Auwal, haka ta haife shi. Ta kuma rantse da Allah cewa wannan lamari gaskiya ne babu kokonto.

A yayain hadubar Juma'ar da ta gabata da Sheik Dahiru Bauchi ya yi, ya ce "wannan ba komai bane a wurin Ubangiji illah raddi ga kafurai masu inkari da Annabi (SAW), don kara nuna musu cewa Manzon Allah gaskiya ne.

"Sannan ya kara nuna wa duniya irin mu'ujizar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Shine ya sa aka haifo wannan yaro da Kur'ani da kuma carbi".

Shehin Malamin ya kara da cewa "wannan carbi kuma ba komai bane face raddi ne ga masu inkarin Shehu Tijjani da darikarsa ta Tijjaniyya, don Allah ya kara nuna wa duniya cewa Dariku gaskiya ne.

Shehin ya kara da cewa duk ga alamomin Tijjaniyya a jikin wannan carbin. Wannan karamar Shehu Tijjani ne ta kara bayyana ga masu inkarin me Darikar ta Tijjaniyya.

A karshe Shehin ya yi addu'ar Allah ya kare Musulunci Da Musulmai, ya kuma zaunar da Nijeriya lafiya tare da kare ta daga dukkan bala'o'i.

Larabci Yafi Ko Wane Yate Dani A Duniya - Ummi Zee

Tsohuwar jarumar masana'antar kannywood wato ummi zee tayi bayyanin yare kala kala ko wane da nasa fanni a nata ra'ayi ga abinda tace

"Larabci,yafi ko wani yare dadi a wajen maganah"indiyanci,yafi ko wani yare dadi a wajen waka”turanci yafi ko wani yare lankwasa harshe a wajen maganah”chainanci yafi ko wani yare wuya a wajen maganah”bakin mutum kuma yafi kowani yare wajen saurin fahimtar yaren da ba nashi ba a karamin lokaci,dan zaka iya ganin bakin mutum yana indianci sosai ba mistake aciki sai kace yarensa .#MASHAA ALLAH AM SO PROUD TO BE AFRICAN. "

Monday, 26 March 2018

AUDIO : Amsar da Dr. Sani Umar R/Lemo Ya Mayar Ma Yan Shi'a Akan Tambayar Da Sukayi Mashi Na Ya fassara Ayar Al-Qur'ani ba Daidai Ba!!!



A cikin wannan Amsar Dr sani umar r/lemo ya caccaki Yan Akidar Shi'a sosai wanda sunyi tambaya amma bisa jahilci wanda ya nuna biyane kawae suke basu san komai ba.

Wanda yana da kyau ku saurari wannan martani da ya mayar musu da sukace bai fassara ayar Al-Qur'ani dai dai ba.

Latsa wannan link domin downloading

Download Audio here

Ayi saurare lafiya !!!

Wasika Zuwa Ga Matasa - Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Babban malamin addini Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayi wasika zuwa ga matasa na wannan kasar nigeriya da su yi amfani da wannan damar ta samartaka kafin ta gushe musu. 

Shehin mallamin yayi wannan wasika ne ga matasa 'ya'yan talakawa akan yadda suke rayuwa a cikin wannan kasar ga jawabinsa. 

"BAYAN GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI,
INA YI MUKU ADDU'A DA FATAN SHIRIYA
WASU SUNA KIRANKU YAN JAGALIYA, 
WASU SUNA KIRANKU YAN SARA SUKA, 
 WASU SUNA KIRANKU YAN SHARA, 
 WASU SUNA KIRANKU YAN DABA, 
 WASU SUNA KIRAN SU YAN KALARE,
AMMA NI INA KARANKU MATASA MASU DARAJA , DA WASU MARASA KISHI SUKE AMFANI DA KU, DOMIN BIYAN BUKATUN SU NA SIYASA
A LOKACIN DA YAYANSU SUNA MANYAN MAKARANTU, DA MANYAN GIDAJE DA MAKUDAN KUDADE,
KUN TABA GANIN DAN WANI YANA SAI BABANSA
KIN TABA GANIN MATAR WANI DAGA CIKIN SU A WANNAN HALI DA SUKA JEFA KU.?
DON ALLAH KU YI WATSI DA WANNAN RAYUWAR KU KAMA ILMI DA SANAA.
MUYI TIR DA ALLAH WADAI GA MASU BATA MANA RAYUWAR MATASA".

AUDIO :Ko Ina Kano Aka Yi Bad’alar Gidan Gwamnati Sai Dai Mu Yi Allah Ya Isa”!!! Malam Aminu Ibrahim


“Ko ina Kano aka yi bad’alar gidan gwamnati sai dai mu yi Allah ya isa”!!! Malam Aminu Ibrahim 

Malam Daurawa yayi wannan jawabin ne a ranar Juma’a, 16-3-2018 a wajen karatun littafin “Adabul Mufrad” da yake gabatarwa duk sati a majalisin Ansarissunah na Marigayi Sheikh Abubakar Hussein (Albany) da ke Fagge, jihar Kano. Na yi qoqarin tsakuro jawabin da malam yayi akan surutu da kakaci da jama’a suke yi game da shirun da malam yayi akan “rashin kunya da fitsara” da Fatima Abdullahi Ganduje ta yi a wajen bikinta.

Malam yace: “a tafiyar da muka yi a satin nan, na samu saqo sama da 2000. Da hotuna da bidiyo. Aka yi ta yi min waya ana cewa “malam ana ta6argaza a Kano, ana raye-raye da kad’e-kad’e. Bayan na dawo, y’an jarida (da na Fesbuk, da na Whatsapp, da na rediyo, da na talabijin) suka cika a Hizbah suna jirana. Sai wani malami yayi min text, yace idan ka ga text dinnan ka kira ni. Na kira shi. Yace an ce ka tara y’an jarida a Hizbah za ka zuba, to kar [ka sake] ka zuba. Sai ya kashe wayarsa. Sai wani d’an jarida ma ya kirani, yace malam gamu duk an tara mu ana jiran kai so, to don Allah shawarar da zan bayar, kar kayi Magana akan abun. Amma ba dole ka d’au shawarata ba. Duk abinda ka ga dama kayi. Amma don Allah kar ka yi Magana. Na ce ai ni yanzu kun saka ni a tsaka mai wuya. Idan ban yi magana ba ace anyi laifi anyi shiru. Yanzu wanne zan d’auka? In je in yi cashiyata in more? Ko in yi shiru? Wanne ya fi? 

Idan na yi shiru, wad’anda suka saba in an yi abu ina magana, to za su ce to me ya sa malam yayi shiru. Wancan malamin kuma malamina ne, na yi karatu a agurinsa, yana cikin malaman da duk Kano ana girmama su. Shi kuma yace kar nayi magana, yanzu ina zan sa kaina! Don haka sai na zagaye na qi shiga Hizbar. Y’an jarida suka yi ta nema na. Na ce musu ina makaranta. Sai ga su yuuuu. Ni nake gudu suna bina [suna cewa] ‘akaramakallahu an yi ta6argaza, an yi 6arna, an yi shegantaka, an yi  tsalle-tsalle, an yi raye-raye, an kad’a d’uwawu, innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Addini ya mutu a Kano. Mu talakawa da muke sa6o ku daina hana mu. Tunda ba kwa hana manya . . . . . Wani kuma yace akaramakallahu da kana bud’e wuta, yanzu kuma ka daina bud’e wuta. Wani kuma yace abinda ya sa malam ya qi magana, malam yana kare kujerarsa  da muqaminsa ne. Kar yace yar gwamna ta yi tabargaza gwamna ya cire shi. To ni da hizbah wa yake kare wani? Kujerar Hizbah har ta na da wani dad’in da za ka kare ta? To jiya ma sai da aka kaini qara kotu. Qungiyar kiristocin Kano sun dauki lauyoyi sama da goma sha, aka ce wai NA HANA MUTANE SU YI RIDDA A KANO!!!

Ka fito kace an yi ta6argaza a bune mai sauqi. Amma abubuwa dole ana tafiya ana lissafa su. In dai yanzu abinda mutane suke so za ka yi, to wallahi baza kayi komai ba. Duk abinda muke yi, yardarm Allah muke nema. Lokacin yakamata ayi magana za ayi. Lokacin da yakamata ayi shiru za ayi. Mutane so suke mu ringa yin abinda zai burge su, ba wai don Allah ba. Kamata yayi mutum yayi abinda ya dace. Da me zaginka, da mai yabonka, kowa yaje yayi abinda ya ga dama, irin tarbiyyar gidansu kenan. Duk wanda Allah ya bashi qarfin mulki, to ba kowane mai qarfi ba ne a qasa zai iya tunkararsa. Mu Hizbah kwamiti ne qwaya d’aya acikin kwamitocin gwamnati. To ta ya ya za ka kama fad’a da gwamnati? Sai dai ka yi mata nasiha! SAI DAI [MATSALAR] SU YAN SIYASA SUN FI JIN NASIHA A LOKACIN ZABE (shebi you understand?). BA SA JIN ALLAH YA CE ANNABI YA CE. SUN FI JIN TSORON RANAR ZABE. RANAR DA TALAKA ZAI RAMA. Ina cikin gwamnatin, aka zo aka ce za ayi fim village a Kano, gwamnatin na da ra’ayi, na fito nace ban yarda ba! Har daga fadar shugaban qasa sai da aka kira ni. A ka zo aka yi maganar rage shekarun auren y’a mace, duk da na san gwamnatin na da hannu aciki, amma nace ban yarda ba. 

A baya mun yi makamanciyar wannan maganar akan Masallacin Idi! Muka kira taron y’an jaridu. Muka ce mu a matsayinmu na malamai da suke cikin wannan gwamnatin (Zakkah, Hizbah, Shari’a) BA MU YARDA GWAMNATI TA MAIDA MASALLACIN IDI YA KOMA KASUWA BA. Muka rubuta arubuce, duk muka sa hannu, muka kaiwa gwamnati muka ce muna bada shawara kada ta kuskura ta ringa yanka massalaci ana siyarwa. Duk da mun yi abinda kuke so d’in, amma bai yi amfani ba. Kuma kowa yana kallo, ba wanda yace qala. Daga baya ma sai aka zo aka ce an bawa malamai fili d’ai-d’ai [hahhahahah]! Muka je muka kewaye masallacin, y’an jarida suka ringa cewa muna zanga-zanga [kun san an yi haka?]. Mu kace don Allah a qara inganta masallacin, a gyara shi, a sa masa tsaro, a qara fito da darajar Kano, amma [gwamnati] ta yi watsi da mu!

WANNAN BIKIN NA FITSARA, a halin yanzu, a koi’na ana yin shi. Gidajen da ake yi [a Kano] sun fi 100. Mun yi mun yi adaina, da mun bi ta can, sai azo mana da wata doka, ko mutum yayi rijista da da Fed govt. Wani gurin idan ka je ba zai shigu ba. Za ka tarar da sojoji da bindigogi. SU KUMA YAN HIZBAH BA YAN BOKO HARAM BANE! BALLE SU SHIGA GURI SU KWASHI YAN MATA KAMAR YADDA AKA KWASHI MATAN DAPCHI! Wani gurin za su je suga ana badala, amma ga sojoji a bakin gate, sai ince ku taho, ALLAH YA ISA! Yanzu ko ance ana badala a gidan gwamnati, ya d’an Hizbah zai shiga gidan gwamnati ya kamo wani? Gidan gwamnati fa! ‘Dan Hizbah ya je ya ture SOJA, DA DAN SANDA, DA DAN SIKYURITI, YA KAMA YAR GWAMNA, YA KAMA MATAR GWAMNA, YA KAMA MATAR WAYE . . . . . HABA!!! Ko da ina nan aka yi wannan sai dai mu yi Allah ya isa! Abun ya fi qarfinmu. Dokar da ta kafa abun [Hizbah] ba za ta iya ba. 

Akwai gwamnan Sakkwato, ana bikin y’arsa, yan Hizbar Sakkwato suka yi kabbara, suka ce Allahu Akbar, aje a tashi bikin, suka kai farmaki, sai gwamnan yace ya rushe Hizbar. Ba wanda yayi Magana [hahhahhhhah]. Sai ni na tashi na je na same shi, nace your excellency, ka yi haquri ka dawo da Hizbah, yace to malam ga abubuwa [kaza da kaza], nace yi haquri, yanzu ya bani aikin dawo da Hizbah a Sakkwato. Na je na samu gwamnan Katsina, nace don Allah ka kafa Hizbah, za ta yi muku amfani, yace ance in sun kama mutum, sai sun bud’a bakinsa sun shinshina sun ji wai ko ya sha giya. Na ce ba haka bane. Mun kafa makaranta a Kano wacce za ta ringa ba da ilimi. Ba za aringa bin mutum da gudu ba. Ko yanzu in ana biki, in aka kawo min rahoto, cewa nake kar ku je. Idan an fara kar ku je. Idan an gama kar ku je. Ku kawo min sunan mai gidan da adireshinsa. Idan an fara, ka tafi da gudu, akwai mata, akwai masu goyo, akwai yara qanana, da ance ga y’an Hizbah nan, sai a fara guje-guje, sai wani ya karye, wani ya ji ciwo, sai kuma a zo ace y’an Hizbah tsinannu! Subhanakallahumma wa bi hamdik . . . . 

Tsokaci: Wad’annan duk bayanan Malam Aminu Ibrahim Daurawa ne. Babu kalma ta ko d’aya. Kuma malam zai yi magana akan bikin nan. Wannan  kamar wata y’ar shimfida ce. Domin kawai magana ce ta shigo. Domin bi sa al’ada, malam ya fi yin cikakken jawabi wajen amsa tambayoyi. Kuma akwai sauran bayanai masu faida wanda ban kawo su ba. Saboda yanayin lokacina. Ga ma son kashe qishirwarsa akan cikakken bayanin, sai ya nemi karatun da kansa. In sha Allahu zan zo na yi sharhin wasu kalmomi daga kalaman malam.


Dukku Mai son Sauke audio sai ya shiga cikin Wannan link din 

  👇🏽👇🏽👇🏽

Download Audio here

Ayi Sauraro da Karantawa lafiya

Kalli Sababbin New Style Na Hotunan Jaruma Rahama Sadau

Wannan sune sababbin hotunan jaruma rahama sadau da ta fitar a shafinta na instagram wanda ceo hausaloaded blog ya kawo muku domin farin cikinku shine namu, biyan butakar ku shine jin dadin mu.ga hotunan kamar haka