November 2017 - NewsHausa NewsHausa: November 2017

Pages

LATEST POSTS

Thursday, 30 November 2017

'Dalilin Da Ya Sa Ake Kira Na Shu'uma —Jaruma Fati Abubakar

Matashiyar nan ta fina-finan Kannywood, Fati Abubakar ta ce ana kiranta da suna Shu'uma ce saboda rashin jin da ta nuna a fim din Shu'uma.

Fim din na Shu'uma na koya darasi ne kan mummunar makomar miyagun mutane.
A hirarta da Nasidi Adamu Yahaya , Fati ta ce tana matukar son taka rawa a matsayin "muguwa" a fina-finai.
"Na fi so na fito a matsayin muguwa saboda na fadakar da mutane irin illar mugunta da son rai.

"Ka san yawancin jarumai sun fi son fitowa a matsayin masu kirki, amma ina ganin hakan ba ya aikewa da sako kai tsaye kamar jarumi mugu, wanda ake nuna karshensa bai yi kyau ba", in ji jarumar.
Fati, wacce ta soma fitowa a fina-finan Kannywood a shekarar 2010, ta kara da cewa "Na fito a fina-finan mugunta irinsu Shu'uma da Sai Na Auri Zango da Baya Da Kura da Basma da sauransu".

A cewarta, fim din Basma ne ya fi ba ta wahala "saboda yarinyar da aka hada ni fim da ita, wacce ba ta wuce shekara bakwai ba, shi ne fim dinta na farko, don haka idan na kai mata mangari ko naushi takan ji kamar da gaske ne sai ta tsorata.

"Don haka sai da aka rika sake daukar fim din sau da dama kafin a gama shi".
Jarumar, haifafiyar jihar Bauchi, ta bukaci masu kira a gare ta ta yi aure da su yi mata addu'a, tana mai cewa "idan Allah ya nufa sai ka ga an yi, don haka lokaci muke jira. Amma ina da wanda zan aura".

Fati Abubakar ta ce tana so a hada ta fim da ubangidanta Adam A. Zango da kuma Jamila Umar (Nagudu) saboda suna burge ta "kuma hankalina a kwance yake idan ina tare da su".

INNALILLAHI WAINNA ILAIHIRRAJI'UN Wani Ya Daddatsa Dalibai Da Adda A Jihar Borno kalli hotuna



Daga Adamu Lawan Mohammed (Bature)

Yanzu wani wanda ba a san ko wanene ba ya shigo cikin makarantar firamari ta Jafi dake karamar hukumar Kwaya Kusar dake jihar Borno da adda, inda ya kashe Yara biyu har lahira da raunata wata daliba da kuma sare hannun wata Malama.

Yanzu haka an garzaya da su asibitin Medical Center dake jihar Gombe.

Saidai matasan gari  sun yi nasarar cafke wanda ya yi laifin inda suka far masa da duka.
Da kyar  jami'an 'yan sanda suka karbe shi a hannun matasan suka tafi da shi ofishinshisu domin yi masa bincike.


Buhari Zai Sake Tsallakawa Kasar Jodan Wajen Taron Yaki Da Ta'addanci



A ranakun 2-3 ga watan Disamba ne, ake sa ran Shugaba Muhammad Buhari zai sake tsallakawa kasar Jordan don halartar taro kan ci gaban da aka samu kan yaki da ayyukan ta'addanci a duniya.

Sarkin Jordan, Mai Martaba Abdullahi II ne zai karbi bakuncin shugabannin yankin Afirka ta Yamma da kuma wakilan kasashen duniya 48 inda ake sa ran Buhari zai bayan awa mahalarta taron matakan da yake dauka wajen murkushe mayakan Boko Haram.

An Kaddamar Da Sabuwar Manhajar Karatu A Yanar Gizo


A jiya ne aka kaddamar da sabuwar hanyar karatu a yanar gizo mafi sauki; wato www.mylearningacadem­y.com . Wannnan manhaja dai kokari ne da wani dan Arewa na farko ya yi, wanda ba a taba samun irinsa ba a Arewacin Najeriya.

Bikin kaddamarwar ya wakana ne a hotel din Transcorp da ke Abuja, kuma taron ya sami halarta masana da jami'an tsaro da 'yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati da wakilai daga kungiyoyi irin su UNESCO da masu ruwa da tsaki a kan sha'anin ilimi.

Babban mataimakiyar Sakataren majalisar dinkin Duniya, Hajiya Amina Muhammad ta albarci taro da kuma kira ga al'umma da su yi amfani da wannan manhajar don kara ilimi.

Wannan kalubale ne ga hukumomi da ma'aikatu da kungiyoyi masu zaman kansu da su sani cewa Arewa fa akwai masu hazaka da basira.
www.mylearningacademy.com
mylearningacademy.com



HUKUNCIN SANYA TUFAFIN ARNA A GARURUWANSU:-Daga Dr. Aliyu Muh'd Sani

Lallai abu ne sananne saba wa Kafirai da Mushrikai a abubuwa na rayuwa da suka kebanta da su yana daga cikin Manufofin Shari'ar Muslunci. Shi ya sa aka samu Hadisai masu yawa sun zo suna umurtanmu da saba wa Yahudu da Nasara a siffofinsu na zahiri, na Tufafi da Al'adu da sauran lamura na rayuwa, kuma suka hana mu kamanceceniya da su da kokkoyonsu.

Amma sai dai saba musun yana kasancewa ne a lokacin karfi da izzan Musulmai. Amma duk inda Musulmai suke da rauni to saba musun ba Wajibi ko Mustahabbi ba ne, matukar zai haifar da cutarwa.

Don haka duk lokacin da Musulmai suka kasance a garuruwan Kafirai da kasashensu to babu bukatar su saba musu, don tsoron cutarwa. Kai, kamantuwa da kafiran a siffofinsu na zahiri, kamar Tufafi da Aski da wasu abubuwan na zahiri zai iya zama Wajibi ko Mustahabbi gwargwadon Maslaha ta Shari'a, kamar zuwa Kasar Kafiran don Da'awa da kira zuwa ga Allah.

Shaikhul Islami ya ce: 
لو أن المسلم بدار حرب، أو دار كفر غير حرب؛ لم يكن مأمورا بالمخالفة لهم في الهدي الظاهر، لما عليه في ذلك من الضرر بل قد يستحب للرجل، أو يجب عليه، أن يشاركهم أحيانا في هديهم الظاهر، إذا كان في ذلك مصلحة دينية: من دعوتهم إلى الدين، والاطلاع على باطن أمرهم لإخبار المسلمين بذلك، أو دفع ضررهم عن المسلمين، ونحو ذلك من المقاصد الصالحة.
اقتضاء الصراط المستقيم لمخالفة أصحاب الجحيم (1/ 471)

"Da ace Musulmi yana kasar abokan yaki, ko kasar kafirci ba abokan yaki ba, to ba a umurce shi da saba wa Kafiran a siffofi na zahiri ba, saboda abin da ke cikin haka na samun cutarwa. Kai, zai iya zama Mustahabbi ko Wajibi a kan mutum wani lokacin ya yi tarayya da kafiran a siffofinsu na zahiri (kamar Tufafi, tara gashi ko aski), idan akwai Maslaha ta Addini a cikin hakan, na kiransu zuwa ga Addini, ko leken asirinsu da kawo labari ga Musulmai, ko kawar da wani cutarwa daga Musulmai da makamancin haka na kyawawan Manufofi".

Saboda haka, matukar akwai Maslaha ta Addini to dacewa da kafirai a Tufafinsu a cikin garuruwansu Wajibi ne ko Mustahabbi. In kuma babu Maslahar Addini hakan halal ne. Musamman saboda yadda a yau ake zargin Musulmai Ahlus Sunna da Ta'addanci. Don haka Wajibi ga wanda ya je Turai don yin Da'awa ya sanya Tufafinsu.

Da wannan nake jan hankalin 'Yan uwa Ahlus Sunna, bai kamata muna kutsawa cikin abubuwan da za su kara Ta'assubanci da rabuwar kai a tsakaninmu ba. Sa'annan kuma yana da kyau mu nisanci dukkan abin da zai zubar da Haiba da Kwarjinin Jagororin Da'awar Sunna. Saboda yana daga cikin manyan sabuba na lalacewar al'umma in ta wayi gari ba ta wasu jagorori a lamuransu da take ganin kimarsu da kwarjininsu, a mayar da kowa bai wuce a ci mutuncinsa da hakki ko ba hakki ba. Sai kuma in wata matsala ta kunno kai mu fara lalubensu wajen warware matsalar.

In muka daraja jagororinmu  Da'awa da dukkan Shugabanninmu sai mu samu hadin kai da cigaban rayuwa.

Sababbin Hotunan Hafsat Idris Barauniya tare da Yan uwata yar Fim

Sababbin hotunan jaruma Hafsat idris baruniya da tayi a bukin Happy Birthday na halima atete a instagram dinta ga hotunan kamar haka


Guguwar siyasa :- PDP na zawarcin Kwankwaso ya bar APC zata bashi takara 2019



PDP na zawarcin Kwankwaso ya bar APC zata bashi takara 2019
Majiyoyi masu tushe sun ruwaito cewa jigogin jam’iyyar PDP na cigaba da matsawa tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso lamba kan ya bi sahun Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar APC.

Bayanai sun nuna cewa hakan ne ma tasa a kwanakin baya Kwankwaso ya gana da Shugaban PDP na kasa, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi da Abdul Ningi a Kaduna a inda suka tattauna batun makomar siyasarsa.

Kawo yanzu dai bayanai sun nuna cewa jigogin jam’iyyar PDP sun fi raja’a a kan tsayar da Kwankwaso a matsayin dan takarar Shugabancin kasa na jam’iyyar ganin yadda ya karbu a kowane sashin kasarnan fiye da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Suna kuma ganin shine koda jam’iyyar APC ta tsaida Buhari a 2019 Kwankwaso ne kadai dan takarar da zai iya ja da Buharin a 2019 musamman idan akayi la’akari da zaben fidda Gwamni na jam’iyyar APC a 2015 inda mista Kwankwso ya zo na biyu a zaben.

Cikin wadanda suke muradin ganin Kwankwaso ya koma PDP sun hada da shugaban amintattu na jam’iyyar ta kasa, Sanata Walid Jibrin, da tsohon Kakakin jam’iyyar ta kasa Barrister Abdullahi Jalo, da shugaban magoya bayan Kwankwaso, Alhaji Sharu Garba Gwammaja,

Mista Jalo yace yayi fatan Ganin tsohon Gwamnan Kanon ya sauya sheka zuwa PDP tun da wuri domin a tsara abubuwa tun da wuri. A yayinda magoya bayan tsohon Gwamnan ke ganin gwara ma Kwamkwason ya koma PDP domin APC ba zata bashi damar kaiwa ga cimma manufofinsa ba.

Wednesday, 29 November 2017

[VIDEO FILM] download 'Kalan Dangi 3& 4'Latest Hausa Film 2017|Ali nuhu | Aminu Momo| Sadiq Sani Sadiq | Hafsat Barauniya and Others

Saukar da sabon shirin masana'antar kannywood wato "Kalan Dangi" wannan shiri ne da anka shiri wanda yake dauke da tsarin soyayya da kuma barkwanci a cikinsa.

Wanda ya tara yan karya a cikinsa ba mazan ba, ba matan ba kowa karya tayi masa yawa.

Jarumai da sunka haskakawa a wannan film sune kamar haka:-

Ali Nuhu

Sadiq Sani Sadiq

Aminu Shareef momo

Nafisa Abdullahi

Hafsat idris barauniya

Fati washa

Jamila nagudu

Maryam booth

Aisha Tsamiya

Da dai sauransu

Domin download kallo wannan shiri sau ku latsa wannan link na kasa.


Kalan Dangi 3 &4

Download Video Now

[VIDEO FILM] Download 'Kalan Dangi 1 & 2' Latest Hausa Film 2017|| Ali Nuhu |Aminu Momo | Sadiq Sani Sadiq | Hafsat Barauniya and others

Saukar da sabon shirin masana'antar kannywood wato "Kalan Dangi" wannan shiri ne da anka shiri wanda yake dauke da tsarin soyayya da kuma barkwanci a cikinsa.

Wanda ya tara yan karya a cikinsa ba mazan ba, ba matan ba kowa karya tayi masa yawa.

Jarumai da sunka haskakawa a wannan film sune kamar haka:-

Ali Nuhu

Sadiq Sani Sadiq

Aminu Shareef momo

Nafisa Abdullahi

Hafsat idris barauniya

Fati washa

Jamila nagudu

Maryam booth

Aisha Tsamiya

Da dai sauransu

Domin download kallo wannan shiri sau ku latsa wannan link na kasa.

Kalan Dangi 1 & 2

Download Video Now

Sakon murya na wata mutuniyar Taraba na kara sarkakiya kan batun kisan Bilyaminu


- Matar da ke magana a muryar tace ita a jihar Taraba take

- An dai kashe bilyaminu ne a gidansa dda ke Maitama, sai dai matarsa ta musanta kisansa, inda aka ce tsautsayi ne

- Matar ta ce tana da hujjar cewa Marigayin yana soyayyar batsa da surukar tasa ne, abin da wai ya haukata matar tasa ta dauki mummunan mataki



Sakon murya da ke yawo a Whatsapp ta wayoyin salula, a arewa, na wata mata, ya sake birkita lamari kan batun kisan da aka yi wa Bilyaminu da makami a makon jiya.

A muryar, wata mata ta kare wadda ake zargi, da cewa ai dole ta dauki irin matakin da ta dauka, saboda wai ai sakon text din waya da ta kama a wayar mijn nata, na hirar batsar soyayya ne tsakanin mahaifiyarta da mijinta, wato wai kwartanci suke.


Babu dai wata hujja da matar ta bayar, duk da tayi ikirarin tana da hujjar hakan, inda tayi Allah-Wadai da Allah-Tsine ga wai matan aure masu neman maza a waje.

Ta yi musu kudin goro gaba daya, inda cikin ashariya ta kira mata da karuwai, ta kuma rantse ko ita ce mutum ya neme ta ya zo ya nemi 'yarta to zata hallaka shi murus har lahira.



Ya zuwa yanzu dai, babu wanda ya musanta ko ya gasgata wannan babban zargi daga bakin wannan mata da ba'a fadi sunan ta ba. Duk da cewa uwa da 'ya suna gaban kuliya kan zargin laifukan su daban daban.


Alamu dai na nuna cewa wannan batu baya kusa da mutuwa nan kusa, kuma al'ummar arewa sun kasa kunne sai sunji kwakwap, kamar yadda suke mayatar kallon wasannin Hausa.

SHIGAR DA SU SHEIK BALA LAU SUKE YI A KASASHEN TURAWA SHINE DAIDAI A MAHANGAR ADDIN GA HUJJOJI KAMAE HAKA


Wani bangare na mutane suna suka da aibanta Shugaban Izalar Najeriya da Sakaren sa akan irin tufafin da suke sanyawa a kasashen turawa, imma zargi da sukan nasu ya kasance da kyakkyawan manufa suke yi ko kuma da munmunan manufa, to koma dai yayane ga bayani takaitacce.

Idan mutum ya tafi wani gari ko wata kasa to abinda ake bukata daga gare shi shine ya sanya irin tufafin mutanen garin, bai dace ya saba mu su ba, kai saba musu ma makruhine.
Yazo cikin Mausu'atul Fiqhiyyah a 6/154 cewa:-
لبس الألبسة التي تخالف عادات الناس مكروه لما فيه من شهرة، أي ما يشتهر به عند الناس ويشار إليه بالأصابع، لئلا يكون ذلك سببا إلى حملهم على غيبته، فيشاركهم فى إثم الغيبة.
Sanya suturar da ta sabawa al'adar mutane makruhi ne sbd abinda yake cikin sa na shahara, abin nufi abinda yake yin shahara da shi a wurin mutane har ana yin ishara da yatsu zuwa gare shi, sbd kada hakan ya zama sababi da zai sanya su yin gibar sa, sai shima yayi musharaka da su cikin zunubin giba.

Sheik Uthaymeen a Liqa'ul Babul Maftuh 24/148 (Allah ya jikansa) yace:-
والسنة في كل إنسان أن يلبس ما يلبسه الناس، ما لم يكن محرما بذاته، وإنما قلنا هذا، لأنه لو لبس خلاف ما يعتاده الناس لكان ذلك شهرة.
لقاء الباب المفتوح 24/148.
Abinda yake Sunnah game da kowane mutum shine ya sanya suturar da mutane suke sakawa, matukar bai zama haramun a zatin sa ba, mun fadi hakane sbd da ace zai sanya tufafin da yake sabanin abinda mutane suka rike shi a matsayin al'adar (su wurin sanya tufafi) to da hakan ya zama shuhura.

Ga abinda babban Malamin hadisi kuma Malami a Masallacin Manzon Allah Sheik Al'abbad yace:-
 وإنما الذى لا ينبغي هو أن يكون في بلد ويأتى بلباس غريب.
شرح سنن أبي داود 29/73
Abinda bai dace ba shine mutum yazo da tufafin da yake baqo ne (a wurin mutane tufafin da ba su san da shi ba a wurin su).

Don haka masu sukan su Sheik Bala Lau akan suturar da suke sanyawa a kasashen turawa suna sukan su ne kawai a bisa jahiltan addini da kuma jahiltan rayuwa.

Sbd haka masu sukan su sune jahilai, amma su Sheik Bala Lau sun gina lamarin su ne a bisa shari'ah.

Sanann su masu zagi da suka sun manta yanzu lokacin sanyi ne matuka kuma sanyin da ake yi a wadancan kasashen yafi sanyin da ake yi anan Najeriya, sbd kiyayya sun ma kasa lura da wannan.

Allah ya taimaki shugabanninmu ya kuma dawo da su lafiya.
Ameen.

Fim Sana'a ce mai Rufin Ashiri Inji Balkisu Abdullahi

Shahararriya kuma matashiyar ‘yar wasan Hausan Kannywood, Bilkisu Abdullahi, tana daya daga cikin jarumai mata da tauraruwarsu ke haskawa a wannan lokacin, a cikin kwanakin nan ta yi finafinai da dama wasu sun fito wasu suna kan hanya.

Bilkisu tana daya daga cikin jarumai mata masu kwazo da maida hankali musamman a ta fuskar masana’antar da kuma ayyukanta. Tana da kwarjini idan aka duba ta fuskar al’umma, cikin kankanin lokaci ta samu karbuwa a idon duniya.

Bilkisu ta na iya bakin kokari ta ga ta birge masu kallo. Akasarin masu kallon fim suna son su ganin ta a ciki finafinai. Jarumar ta kware a gurin rawa da iya magana. Masoya na son ganin ta hau kowace rara da darakta ka iya dora ta.

Al’umma suna yabon Bilkisu kwarai da gaske ta wadannan fuskoki uku musamman gani rawar da ta taka a finafinan ta na kwanan nan.

Bilkisu haifaffiyar garin Legas ce, a nan ta girma a can kuma ta yi Makarantar Noziri da Firamare dinta, daga bisani kuma ta dawo Kano da zama, anan ne kuma ta yi karatun Sakandiri a Dinop International School dake Hotoro, bayan ta kammala karatunta, sai ta shiga harkan fim.

Ta bayyana a Abinda ya ja hankali ta ta fara harkan fim a wata hirar da suka yi da wakilinmu ta ce, “fim akwai abubuwa da dama, fim akwai fadakarwa sosai a cikinsa, ni kaina akwai FINAFINAN da na yi na ga abubuwa sosai wanda ni ma na dau darusa a cikinsa”,
Ta kuma bayyana mana cewa ‘Kanina’ na daya daga cikin finafinan da ita kanta ya birge ta, koda aka tambaye ta dalili, sai tace, “Saboda irin yanda labarin fim din yake, ya yi kyau, kuma akwai darussa a ciki wanda al’umma za su karu da su”.

Ta kuma ba ‘yan uwanta maza da mata na masana’antar Kannyood shawarar da su rike sana’ar fim da hannu biyu, inda take cewa, “Fim dai sana’a ce mai kyau daidai gwargwadon da zaka rufa ma kanka asiri, kuma sannan su yi abinda ya kawo su, sannan su bi ta hanyar da suka san ta alhairi ni, kuma za a taimaka masu kuma mai shi yana da hanyar.”
Koda aka tambayeta wani irin kalubalen ta fuskanta a rayuwarta, da fara harkan fim. Ta ce ita bata fuskanci matsaloli ba gaskiya, sadda ta fara harkan fim, saboda da yardar mahaifanta ta shiga industri, kafin Allah ya musu rasuwa, kuma ko yanzu ba ta wani samun tsangwama daga gurin ‘yan uwanta da masoyanta, suna zaman lafiya har gobe.
Ta bayyana a finafinai da daman Gaske wanda ita da kanta ba za ta iya kawo su ba. Cikin kwanakin nan ta yi finafinai da dama, wadanda al’umma ke sha’awar kallonsu, kamar su Kanina.

Kanina fim ne wanda ya samu ingantaccen aiki da kwararrun ma’aikata, da sabbin fuskan jarumai masu tasowa, da kuma wadanda suka dade a masana’antar, wanda ya hada da irin su: fittaccen jarumi kuma sarkin Kannyood Ali Nuhu, yana cikin fim din kuma shi ya bada umarni, Nazir Dan Hajiya kuma ya dau nauyin shirin, Shamsudden da ita Bilkisu suka fito a matsayin jaruman shirin.

Daga cikin fina-finan da ta yi kwanan nan akwai: Burin Duniya, Kama, Wata Mafita, Nawad, Waye Sila, Nafsi Nafsi, Zan Rayu Da Ke, Zubaidah da dai sauransu.
Fim din Ya A So fim ne da ke cike da ilmantarwa gami da fadakarwa, fim me me dauke da labarin soyayya mai shiga jiki kwarai, tare da kara wayar da kan masoya, wanda ya samu aiki kwararrun daraktoci da furodusosi, dauke kuma da manyan jaruman Hausa fim wadanda suke tashe a wannan lokacin.

Juruman da suka bayyana a wannan fim din ya hada da jarumar Bilkisu, inda ta taka rawar gani kwarai a cikin shirin, sai kuma matashin dan wasan Hausa koma mai hazaka Abdul M. Shareef, ya fito a matsayin jarumin shirin, sun bada mamaki kwarai da gaske ganin yadda suka yi abun da ba a zata ba, don kuwa ba industri kadai ba ko ina ana muradin fitowar shirin.
Sanin kowa ne Bilkisu tana juya alkalami a wannan lokacin, inda ta doke sauran matan da yawan finafinai a shekaran nan.
Ta fara aiki ne a karkashen kungiyar Karami Multimedia, wanda kawo yanzu tana tare da su, akalla jarumar ta kwashe shekaru biyar tana aiki a masana’antar, da kuma fara bayyanar ta a fim a matsayin jaruma yau shekara daya kacal, amma abun dubawa anan shi ne ta karbu matuka a idon al’umma kamar wacce ta dade a na dama furar da ita, dik da cewa ta samu wasu manya jarumai zuwanta Kannywood, hakan bai hana ta nuna ta ta bajintar ba.
Jarumar tana da kyakkyawan mu’amala tare da matashin jarumi Abdul M. Shareef, wanda sun yi finafinai da daman gaske tare, haka zalika kuma sun fi shakuwa da jarumar Nafisa Abdullahi a cikin mata.
Ta kuma baiyana cewa London yana daya daga cikin kasar dake birgeta kuma take sha’awar zuwa. A abinci kuwa tana son cin Indomi, koda aka tambaye ta wani kalan mota ya fi birge k, sai ta ce Honda.
An tambaye ta daga karshe me za ta ce ma masoyanta da masu sha’awar kallon fim din Hausa baki daya, sai ta ce “Nagode kwarai da goyan bayan da suke bani ina kuma masu fatan alheri, Nagode”

Kalli Hotunan Manya manya Malamai :-Musulunci Ba Bakauyen Addini Bane ga tambaya Akaramakallah



Dayawa mutane basu fahimci addini ba, ka wai suna yi masa hawan kawara. Inda wani zai ganka a matsayin kai ba cikaken musulmi bane idan ka saka kananan kaya.

Idan aka tambeshi hujja sai yace "ka yan yahudu da nasara ne. Kuma ance kada muyi koyi da su."  Wannan ita ce hujjar sa.

Toh ga tambaya  Akaramakallah.

1. A cikin kabilun da akafi samu  yahudawa da nasara, kamar su turawa da sauransu.
Nasan kasan akwai musulmai a cikin su, mine ne matsayin saka kananan kayan da suke yi ?

2. kai da kake saka kaftani da hula ina kagan su a cikin kur'ani ko hadisi. ?

3. Waya halak ta maka al'adarka ta saka kaftani da hula?

4. Mine ne matsayin Dr. Zakir naik,  Dr bilal Philip, Ahmad Ddad da Nouhman khan. A wurinka?

Addini ba bakauye bane yana tafiya de-de da yadda zamani yake ba tare da an canja shi ba.

Malam ku chila ku sarara Allah ya kara daukaka.




Na Rubuta Fim Din 'Auren Manga ' Fiye da Shekara Biyar Wanda Shine Fim Da Yafi Kowane A Wasan Barkwaci Nishadi



Fitaccen daraktan fina-finan Kannywood Falalu A. Dorayi ya ce ya hada fim din "Auren Manga" ne saboda ya bai wa mutane dariya da sanya nishadi a zukatan masu kallo.

A tattaunawarsa da Nasidi Adamu Yahaya, Baba Falalu, kamar yadda aka fi saninsa a Kannywood, ya ce ya gina maudu'in fim din ne domin ya sha bamban da sauran fina-finan barkwanci.

A cewarsa, "Na rubuta fim din "Auren Manga" ne sama da shekara biyar da suka wuce da zummar marigayi Rabilu Musa Dan Ibro ya zama babban jaruminsa, amma sai Allah ya yi masa rasuwa.

"Don haka ne na yi gyare-gyare a cikinsa kuma ni da kaina na zama babban jarumin cikin fim din".


"Babban abin da yake koyarwa shi ne yadda ake tilasta wa namiji, wato Manga ya fito da matar da zai aura. Ka ga hakan ya bambanta da yadda aka saba."

Falalu A. Dorayi ya ce mai daukar nauyin shirin Yakub Usman, ya kashe sama da naira miliyan biyu wurin hada fim din.
Fim din ya hada manyan jarumai irinsu Adam A Zango da Hadiza Gabon da Sulaiman Yahaya (Bosho) da Baban Chinedu da kuma Falalu Dorayi

Budaddiyar wasika zuwa ga masana'antar kannywood Akan Munafuka Daga Tijjani Asase


Salam zanyi wata budandiyar wasika, ga mutanen masa na antar fim. Agaskiya ina mamaki yarda akekiran mu taro sai kaga kowa yana nokewa wanima sai kajishi yana cewa ai taran na munafukaine kuma da mata sun busa usir nabiki sai kaganmu kowa yaci kwalliya guru yacika da yaran 'yan fim da manyan su ana ta shewa, alhali bashida wata sana'arda tafi wannan kuma so ake akawo gyara da cigaba na masa na antar. 

To kusani idan takamar ka daukaka ina Hauwa Ali dodo. Ahamed S nuhu. ina Dan iburo. ina Amina garba kasumu yaro Tijjani ibirahim duk sun mutu kuma haryan zu ana fim Dan haka kayi kokari ai gyaran dakai kada kamanta yanzuhaka 'yayan mu sune suka fara shigowaciki kai kokari Dan ka ya yi alfahari da kai kada kuma kasa aranka, idan masa'antar ta gyaru kataimakawa kanka,kuma katemaki  Al'umarka, Allah kabamu iko gane gaskiya kuma mubita amin.

Tuesday, 28 November 2017

A Yau Ne Ali Nuhu Ya Baiwa Teema Makamashi Sarautar 'Jakadiyar FKD' Kalli Hotuna

A yau ne ankayi bukin kaddamar da teema makamashi a matsayin jakadiyar kamfanin fkd karkashin babban jarumi kuma daracta na harka shirya fina finan Hausa.
Muna taya ta Allah ya taya riko ga godiya ta kamar haka:-

"ina Al fahari dakai babana Allah yabar kauna Allah yabiyaka Allah yakara daga darajar kamfaninmu FKD Ya AALLAH YA ALLAH 😭😭 Kukan dadi nakegi @realalinuhu @ali_nuhu_fans_club @ali_nuhu_fans_page @kannywoodcelebrities @kannywoodexclusive @malam_dila @hausa_film_stars_pictures"
Daga shafinta na instagram.

Ga hotunan bukin kamar haka



An sauke hotunan Buhari a Kano sakamakon kin zuwansa jihar

An sauke hotunan Buhari a Kano sakamakon kin zuwansa jihar
Rahotanni daga jihar Kano suna bayyana cewa wasu mafusata sun farwa allunan tallan Shugaba Buhari da Gwamnatin Kano ta sassaka a waje da dama a cikin birnin jihar suna cirewa tare da farfasawa a sakamakon kin zuwa da Shugaban kasar yayi a jiya litinin.

Tun farko dai anyi ta yayata cewa shugaban zai kai ziyarar aiki Kano a ranar Litinin 27 ga watan Nuwamba har takai ga aka rika sanarwa a gidajen Radiyo a jihar ta Kano cewar mutane su fito su yi turururwa domin tarbar Shugaban kasar.

Sai dai daga bisani Hausa Times ta ruwaito Mista Buhari ba zai je Kano a watan Nuwamba ba. Hausa Times ta ruwaito wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa na bayyana cewa ‘dama tun farko Buhari bai ce zai ziyarci Kano ba kawai dai wasu makusantan shugaban ne suka kirkiri zancen suka yada’

Hausa Times ta bayar da labarin cewa ‘anyiwa shugaban kasar riga malam masallaci. Domin a ranar Litinin ma shugaban zai fice daga kasar’ kuma hakan akayi.
Hausa Times ta ruwaito dama cen an tsara mista Buhari zai ziyarci wasu jihohi a Arewacin kasar ne ciki har da jihohin Kano da Katsina a farko-farkon watan Disamba ba Nuwamba ba kamar yadda aka yita yadawa.

Sai dai wasu rahotanni da ba’a tantance ba sun nuna har a gidan Gwamnati an sauke hotunan shugaban kasar a wasu wuraren a yayinda mafusata kuma a waje suka rika cirewa tare da balle allunan dake dauke da mista Buharin da aka kakkafa a cikin gari.

Ina da takardan da zan bawa Buhari ya bankado Triliyan Uku -inji Abdulrasheed Maina


Ina da takardan da zan bawa Buhari ya bankado Triliyan Uku -inji Maina
Tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa na sauya fasalin hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, yace yana da takardun shaidu da shugaba Buhari zai gano fiye da Naira Triliyan Uku (3tr) a cikin watanni 9.

Mista Maina wanda yayi wata kebantacciyar hira da gidan Talbijin na Channels yace ya nemi duk hanyar da zai gana da shugaban kasar amma anki bashi dama.
Maina wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa yanzu haka hukumar EFCC na nemansa ruwa a jallo.

A cikin tattaunawar wacce gidan TV ya haska a daren ranar Litinin Hausa Times ta jiyo Maina yana cewa galibin makusantan shugaba Muhammadu Buhari da suke kewaye dashi ko ya aminta dasu ba masu nufin gaskiya bane kuma basa fadi mashi muhimman abubuwa da ya kamata ya sani a kasarnan.

A cewarsa idan har akwai mai ja da maganarsa to a bashi dama ya gana da shugaban kasar, ‘ni kuma nayi alkawarin sai na bashi bayanai da takardun sirri da zai bankado fiye da triliyan Uku

Monday, 27 November 2017

Hotunan Jaruma Maryam Booth A Wajen Hidimar Kasa NYSC A Wannan Shekara

Maryam booth daya daga cikin taurarun masana'antar kannywood tana daya daga cikin masu yiwa kasa hidima wato NYSC a wannan shekara ga hotunan wajen camp Ma'ana wajen basu training kafin a rarabasu wajen inda zasuyi hidima


Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!! Wa'azin Kasa A Kontagora, Niger State Nigeria 2017



Shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau

Shugaban Majalisar Malamai Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

Daraktan agaji Injiniya Mustapha Imam Sitti

A madadin kungiyar Jama’atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunna ta tarayyar Najeriya, suna farin cikin gayyatar 'yan uwa musulmi zuwa wajen wa'azin kasa a garin KONTAGORA, dake jihar NIGER a ranakun asabar da Lahadi 02/03/December/2017. Insha Allah.

Ana san ran halartan:

-Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina
-Sheikh Abbas Muhammad Jega
-Sheikh Habibu Yahaya Kaura
-Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe
-Sheikh Abubakar Giro Argungu
-Sheikh Barista Ibrahim Sabi'u Jibia
-Sheikh Abdulbasir Isah U/Maikawo
-Sheikh Khalid Usman Khalid Jos
-Sheikh Abdullahi Telex Zariya
-Sheikh Abdussalam Abubakar Baban Gwale
-Sheikh Ibrahim Idris Zakariyya Jos
Da
-Alaramma Abubakar Adam Katsina
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Abdulkarim Akwanga
-Alaramma Bashir Gombe
-Alaramma Isma'il Maiduguri
-Alaramma Ilyas Birnin Gwari
-Alaramma Usman birnin kebbi
-Alaramma Ibrahim Yahuza Bauchi

Masu masaukin baki:

Shugaban JIBWIS na jihar Niger, Alhaji Abdullahi mai Rediyo, da

Shugaban Malamai ta jihar Niger Sheikh Aliyu Adarawa Kontagora da

Daraktan agaji ta jihar Niger Malam Abdulbasir Musa

NB/ Ana bukatar kwararrun direbobi su ja ragamar tafiyan, saboda rashin kyawun hanya. Allah ya kiyaye hanya, ya bada ikon zuwa da nasarar abun da akaje yi. Amin.

Sanarwa daga ofishin sakataren kungiyar ta kasa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, ta ofishin JIBWIS Social Media ta kasa.

[VIDEO] kalli Biyon Happy Birthday Na Halima Atete Jarumar Kamar Su:- Ali Nuhu |Adam AZango |Hafsat Barauniya and Others

Wannan shine video bukin zagayowar ranar haihuwar halima atete shekara 29 a duniya.Wannan dai mace ce wanda ta haskaka a shirin fim din hausa a kannywood.


Kalli kyawawan hotunan happybirth na jaruma halima atete

Ga kadan daga cikin jarumai da zaku kalla a cikin wannan bidiyo suna chashewa:-

Ali Nuhu

Adam a zango

Hafsat idris barauniya

Halima atete

Saratu gidado

Da dai sauransu


Download Video Now

[Video Film] Sarauniya Latest Fim Trailer | Staring | Ali Nuhu | Adam A Zango

Saukar da Trailer fim mai suna "SARAUNIYA" fim din Sarauniya fim ne da anka tsara a tsantsar nuna yadda al'adun hausa yake tun a zamanin da.

Fim ne wanda yake bada labarin wata masarauta da tayi fice a kasar hausa.Wanda ya samu jiga jigan manya manya jarumai kamar haka:-

Ali Nuhu

Adam A Zango

Al'amin Buhari

Asabe madaki

Hannan

Tijjani faraga

Tanimu akawu

Bashar nayaya

Hadiza Muhammad

And others.

Director Hassan Giggs



Download Video Now

[Video Film] Gwarzon Shekara Trailer Fim || Staring Ali Nuhu || Ramadan Booth|| Maryam Booth


Saukar da video na Trailer  "Gwarzon Shekara" wanda ya samu shahararun jarumai kamar haka:-

Ali Nuhu

Ramadan Booth

Maryam Booth

Shamsu Dan Iya

And others

Wanda anka shirya karkashin "Ramadan booth movie"

Director by Sanusi oscar 442


Download video Now



Sunday, 26 November 2017

Bamu Ci Kudin Makamai Ba Inji Kungiyar Izala Daga Sheikh Kabiru Hauruna Gombe

Daya daga cikin jagororin Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya musanta zargin da ake wa kungiyar kan karbar "kudin makamai".

Ana zargin gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da raba wa jama'a da kungiyoyi da kuma kamfanoni a kasar makudan kudin da aka ware don sayo wadansu makamai.

Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis tare da rakiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau, wanda shi ne shugaban kungiyar JIBWIS.

"Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar karbar kudin makamai. Wannan abu ne da kungiyar Izala ba ta taba shiga cikin shi ba," in ji Sheikh Kabiru Gombe.
Gwamnatin Najeriya tana ci gaba da tsare tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki ne bisa zargin yana da hannu a badakalar kudin sayo makamai da suka kai dala biliyan biyu.