Catalonia ya amince da shirin ballewa daga Spain - NewsHausa NewsHausa: Catalonia ya amince da shirin ballewa daga Spain

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 3 October 2017

Catalonia ya amince da shirin ballewa daga Spain

Shugaban yankin Catalonia Carles Puigdemont ya ce, yankin ya amince da shirin ballewa daga kasar Spain bayan kashi 90 cikin 100 na masu kada kuri'a a zaben raba gardama sun goyi bayan matakin ballewar.
Shi dai Carles Puigdemont na bayyana wannan matsayi ne bayan an kwashe jiya ana arangama tsakanin masu goyan bayan shirin zaben raba gardamar da jami’an tsaro.
Jordi Turull mai magana da yawun gwamnati ya ce, mutane sama da miliyan 2 suka kada kuri’a wanda ya kai sama da kashi 42 na masu zabe a yankin.
Akalla mutane 92 suka samu raunuka daga cikin mutane 844 da suka bukaci kulawar likita, yayin da hukumomin yankin suka ce, 'yan sanda 33 suka jikkata.
Tashin hankalin ya dada zafafa tankiyar da ake ciki a kasashen waje da kuma tsakanin gwamnatin Firaminista Mariano Rajoy da na yankin Catalonia.
Rajoy wanda ya bayyana zaben a matsayin haramtacce ya ce, jami’an tsaro sun yi nasarar dakile shi duk da arangamar da aka yi ta samu.
Kungiyoyin kwadago da masu zaman kansu sun kira yajin aikin gama-gari daga gobe Talata saboda abin da suka kira take musu hakkokin su.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment