Sanin kowa ne cewa a wannan makon fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau ta mika roko ga uwar kungiyar masu shirya finafinan Hausa (MOPPAN) domin a yafe mata a d'age takunkumin da aka sa mata. Mujalla Fim bada labarin a ranar. Haka kuma mujallar ta bayyana cewa Ali Nuhu ne ya shige wa jarumar gaba a Kano don ganin an cire mata takunkumin. Ali ya jagoranci jarumar zuwa gidajen rediyo da ke Kano, da Hukumar Tace Finafinai ta jihar, da kuma MOPPAN, inda su ka mika rokon a yafe mata.
Ita dai Rahama Sadau, MOPPAN ce ta dakatar da ita daga fitowa a finanan Hausa saboda wata rawa da ta yi da wani mawaki mai suna ClassiQ a bara, saboda ita da mawakin sun yi rungume-rungume.
Shin me ya sa Ali Nuhu ya yi uwa ya yi makarbiya wajen ganin an yafe wa Rahama an dawo da ita industiri? Mujallar Fim ta tuntubi fitaccen jarumin don sanin dalilin sa na tsaya mata din. Ga yadda hirar mu da shi ta kasance:
FIM: Mun ga cewa kun je wurin shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Malam Isma'il Na'abba (Afakallah), tare da Rahama Sadau. Me ya kai ku?
ALI NUHU: E, to, ba wani abu ba ne illa ya na daya daga cikin shugabannin masana'antar fim. Ni dai abin da na tsara ya na daga cikin wadanda ya kamata a ziyarta, saboda yaro idan ya yi ba daidai ba aka hukunta shi kuma har ya gane illar abin da ya yi ba daidai ba ne, ya nemi tuba ko yafiya, to wajen manya za a je a gaya masu sannan a ga yadda za a yi yafiyar nan an dawo an ci gaba da rayuwa. Wannan shi ne dalili na.
FIM: Ana ta maganar cewa ka dage wajen ganin a sasanta Rahama da shuwagabannin Kannywood, ka na ta yawo tare da ita daga wannan ofis zuwa wancan. Me za ka ce?
ALI NUHU : Rahama dai masana'antar fim din Hausa ta hanya ta ta shigo kuma ta yi laifi. Ni ba zan ce don ta yi laifi kada a hukunta ta ba, dole in goyi bayan a hukunta ta, saboda kowa ya san cewa mu na da doka da tsari. Kuma an hukunta ta kuma abin ya kai kusan shekara guda, tun da kuma ta na cikin wani yanayi wanda za ta iya tuba ina ganin ba komai ba ne don an nemi maslaha. Ta kuma nemi in yi mata jagoranci a matsayi na na uba, shi ya sa na yi.
FIM: Wata majiya ta fada mana cewa akwai wani babban fim ko kuma shiri da ka ke so ka yi da ita a nan Arewa, ganin cewa yanzu ta yi fice a duniyar finafinan Kudu. Kuma dole sai an sasanta tsakanin ta da MOPPAN sannan abin zai yiwu, wai shi ya sa kake ta wannan shige da fice.
ALI NUHU: Wannan ba shi ba ne dalili. Ba ni da wani aiki da zan yi da Rahama Sadau a yanzu. Aikin fim di na da zan yi, 'Abota' ne, 'Abota' kuma babu Rahama a ciki. A yanzu dai babu wani aiki da zan yi da ita.
FIM: Amma an ce ita Rahama ba ta nemi a sasanta ta da MOPPAN ba, kai ne ka ke kokarin sasanta su.
ALI NUHU: Ba haka ba ne. Tun tale-tale Rahama ta na son wannan sasanci. Wato akwai abubuwa da mutane ba su gane ba game da 'yan wasan da su ka yi fice a duniya: yawanci idan irin wannan abin ya faru su kan ja gefe; jan gefen da su ke yi kuma ba don ba su isa tunkara ba ne, amma su na ganin cewa idan ma sun yi magana a lokacin kamar ba za a saurare su ba ne. Kamar kai ne d'an ka ya yi maka laifi, ai ba ya shigowa cikin gida, za ka ga ya tsaya a waje ya na tsoron idan ya shigo baban shi zai dake shi. To, ni haka na dauki rayuwa. Mu na da 'ya'ya, idan har ba za mu samu fahimta ba akwai matsala. Fahimta kuwa shi ne idan yaro ya yi abu, kira shi baban shi zai yi ya masa fada, ya ja masa kunne, ya yi masa hukunci, sai ka ga rayuwa ta zo da sauki. Amma idan ka saki d'an ka, duk fa abin da ya je ya yi asalin sa fa d'an ka ne, ba za a canza masa uba ba. Wannan shi ne abin da na duba, da ta zo ta same ni kuma ta yi magana ni kuma na duba na ga wannan ba wani abu ba ne, da man haka ake so. Allah ma idan ka yi abu ka gane ba daidai ba ne sai ka nemi yafiya Ya yafe maka da kuma zummar cewa ba za ka k'ara ba.
FIM: Wannan ba shi ne karo na farko da Rahama ta fara yin laifuffuka a masana'antar fim ba. Yanzu kuma ka dage wajen ganin cewa an dawo da ita. Yanzu kuma ana ganin ta k'ara gogewa a cikin duniyar finafinai. Ba ka ganin cewa idan aka dawo da ita ta sake yin wani laifin za a zarge ka da cewa da man kai ne mai daure mata gindi ta na abin da ta ga dama?
ALI NUHU : Ni dai a yadda na kalli Rahama a yanzu, ba na jin za ta k'ara aikata laifuffuka kamar wadanda ta aikata a baya. Kullum dan'adam girma ya ke yi ya na k'ara hankali, to ya kamata wani lokacin mu rika yi wa yaran nan uzuri cewa na farko akwai kuruciya, ga daukaka kuma ta zo wa mutum, sai an yi da gaske a ga ya gama ba tare da ya samu matsala ba.
FIM: Kungiyar MOPPAN ce ta kori Rahama Sadau, ba Gwamnan Kano ko kuma Sarkin Kano ba. Me ya kawo Rahama ta roke su, ganin cewa ba su da alhakin korar ta ko kuma dawo da ita? Sannan duka bayanan ta babu inda ta ambaci ta na ba kungiyar hakuri bisa laifin da ta yi.
ALI NUHU: Duk abin da ake maganar idan wani d'an fim din Hausa ko kuma wata 'yar fim din Hausa idan ya yi ba daidai ba, idan ma sun yi laifin ba za ka taba jin korafi daga Sakkwato ko Maiduguri ko Kaduna ko Minna ba. Za ka ga a cikin garin Kano abin ya fi zafi saboda "Kannywood" ake cewa, kuma Kannywood cikin kwaryar Kano abin ya ke. Su waye shuwagabannin Kano din? Su ne Mai Martaba Sarkin Kano da kuma Mai Girma Gwamnan Jihar Kano. Sannan kuma al'ummar Kano al'adar su ce, addinin su ne. Na san ya shafi dukkanin Arewa, amma Kano ita ce cibiya. To, ina ganin idan mutum ya yi ba daidai ba don ya ce al'ummar gari da abokan sana'ar sa da kuma shuwagabanni ba laifi ba ne tunda Kannywood aka ce.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment