Daga Ibrahim Baba Suleiman
Ministan Masallatayyan nan guda biyu masu Alfarma na Makkah da Madina, Sheikh Abdurrahman Sudais ya karrama tsohon gwamnan jihar Sokoto Alh. Attahiru Ɗalhatu Bafarawa a birnin Makkah.
Bafarawa ya samu Babbar kyautar ne daga minista Sudais lura da yadda Attahiru Bafarawa ya jajirce a wasu mihimman batutuwa a ƙasar saudiyya.
Bafarawa dai yana da kyakkyawar alaƙa da Sheikh Abdurrahman Sudais da mutunta juna, wanda a baya ma Bafarawa ya taɓa gayyatar Sheikh Sudais zuwa Sokoto domin buɗe wani katafaren masallaci da cibiyar musulunci a lokacin da yake Gwamnan Sokoto.
Haka Zalika sauran manyan Malaman Saudiyya da ɓangaren gwamnati suna girmama Bafarawa a duk lokacin da ya shiga Saudiyƴa, wacce har ta kai matuƙar Bafarawa yana Saudi to yana da wajen da hukumar masallaci ta ware masa a bayan liman domin girmamawa.
Wannan ba karamin alfahari bane ga ƙasar Nijeriya, ace ɗaƴa daga ciin ƴaƴanta ana girmama su a ƙasar Musulunci, kuma jagorar ƙasashen musulmi ta Duniya, wato Saudiyya.
Allah ya ƙarawa Ƙasar Nijeriya albarka, tare da ɗaga darajar ta tare da ƴaƴanta a idon Duniya. Amin.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment