"Ni ce jahila? Na barku da Allah" Hira da Ummah Shehu - NewsHausa NewsHausa: "Ni ce jahila? Na barku da Allah" Hira da Ummah Shehu

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 7 November 2017

"Ni ce jahila? Na barku da Allah" Hira da Ummah Shehu



A kwanakin baya, jaruma Ummah Shehu ta zama wata babban topic da aka ta tattaunawa sakamakon wani faifan video da ya yadu a dukkan kafofi na sadarwa.


A wata tattauna da jarumar, ta bayyana yadda abun ya bata mamaki domin a cewar ta, abun da tayi cikin wasa da raha amma sai gashi mutane masu neman kurakuren wasu sun dauka sun ta yadawa.


Jarumar ta bayyana wannan kokari na su a mamakin abun haushi da takaici, kuma abun ya mata ciwo a mata gorin ilmin addini duk da yaqinin da take da shi na cewa ita gogaggiya ce a wannan fannin, wannan na ma daga cikin dalilan da suka sa ta zabi harkan fim domin bada tata gudunmawa a fadakar da jama'a.


Daga karshe ta bayyana dukkan wata matsala ko tuntube a rayuwa a matsayin kaddama kuma mutum ba zai ci gaba ba ba tare da yana samun irin wadannan jarrabobin ba, kaman yadda bahaushe yake cewa "hassada ga mai rabo taki"




Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment